Editor

9513 Posts
Rikiɗewar siyasa zuwa ta addini da ƙabilanci a Kaduna

Rikiɗewar siyasa zuwa ta addini da ƙabilanci a Kaduna

Yayin da jam’iyyu ke shirin tunkarar zaɓen gwamna da na ’yan majalisun dokokin jihohi a Nijeriya, wani batu da ke fitowa fili a fagen siyasar Jihar Kaduna shi ne na siyasar addini da kuma ƙabilanci. A baya dai jihar ta sha fama da rikice-rikice masu nasaba da addini da ƙabilanci, lamarin da masana ke nan suka ce yana matuƙar janyo komawa baya ga tsarin dimokuraɗiyya. Duk da cewa akwai masu neman takarar kujerar gwamna a jihar fiye da 10, takarar tafi zafi ne a tsakanin jam’iyyar APC da kuma PDP. Masana harkokin siyasa a jihar dai sun fara nuna damuwa…
Read More
Masu safarar itatuwa da gawayi sun ce sun dawo da ƙarfinsu bayan gwamnatin Nijeriya ta ɗage musu takunkumi

Masu safarar itatuwa da gawayi sun ce sun dawo da ƙarfinsu bayan gwamnatin Nijeriya ta ɗage musu takunkumi

Daga AMINA YUSUF ALI Bayan gwamnatin tarayya ta ɗage musu takunkumin fita da hajarsu ƙasashen ƙetare, masu safarar gyararrun gungumen itatuwa da gawayi sun yi kira da a zo a sanya musu hannayen jarin Dalar Amurka biliyan 152.94. 'Yan kasuwar sun lashi takobin haɓaka jarin kasuwancinsu har zuwa Dalar Amurka biliyan $152.94 a wannan shekara ta 2023. Bayan gindaya musu sharuɗɗa, gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumi a kan safarar gawayi da guma-guman itace domin ta taimaka wa kasuwancin, musamman ma waɗanda suke gyara shara ta koma dukiya domin havaka hada-hada tsakanin Nijeriya da ƙasashen duniya. Ministan Muhalli na Nijeriya, Mohammed…
Read More
CBN ya kammala shirin canjin kuɗi a yankunan karkara

CBN ya kammala shirin canjin kuɗi a yankunan karkara

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya ce ya kammala shirin canjin tsoffin kuɗi da sabo a yankunan karkara da sauran yankunan da babu bankuna. Muƙaddashin Kakakin CBN, Isa Abdulmumin, ne ya bayyana haka tare da cewa shirin ya cimma manufarsa. A cewarsa, “Shirin ya kammala. Shirin abu ne mai ƙayyadadden lokaci amma ba wanda zai ci gaba da gudana ba." Sai dai Ƙungiyar Masu Hada-hadar Kuɗi ta Waya da Wakilan Bankuna a Nijeriya, ta bayyana shirin a matsayin mara armashi, saboda taƙaita damawa da masu ruwa da tsaki a cikinsa. CBN ya ce an samar da shirin ne…
Read More
Ɓata-gari sun cinna wa ɓangaren ƙabilar Ibo a kasuwar Legas wuta

Ɓata-gari sun cinna wa ɓangaren ƙabilar Ibo a kasuwar Legas wuta

Daga AMINA YUSUF ALI Ana zargin wasu ɓata-gari da cinna wuta wacce har ta yi sanadiyyar tayar da gobara a kasuwar Legas ta sayar da kayayyakin gyaran mota wacce mafi akasarin ahalinta inyamurai ne, wato 'yan ƙabilar Ibo. Wannan kasuwar sayar da kayan gyaran mota tana kan titin Kirikiri, Ajegunle, ƙaramar hukumar Ajeromi ifelodun ta jihar Legas. Al'amarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba, 8 ga Maris, 2023. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hari da aka kai kasuwar sayar da kayan mota wacce akasarinta ƙabilar Ibo ne suke da rinjaye a cikinta an yi shi ne da gayya kuma…
Read More
NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

NNPP ta kori ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar da wasu ƙusoshinta a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jam'iyyar NNPP a Jihar Katsina ta kori wasu jiga-jigan jam'iyyar ciki har da mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar, Muttaqa Rabe Darma da shugaban jam'iyyar, Alhaji Sani Liti da sakatarenta Alhaji Mustapha Bashir da kuma shugaban matasa da shugabannin jam'iyyar na shiyyoyin Katsina, Daura da kuma Funtua. Kakakin jam'iyyar, Alhaji Nasiru Usman Kankia ne ya bayyana wa manema labarai hakan lokacin da yake ƙarin bayani dangane da lamarin a Katsina. A cewar kakakin, an kori mutanen ne bisa aikata laifin yi wa jam'iyya zagon ƙasa. Ya ƙara da cewa shugabannin jam'iyyar sun kira wani taron da…
Read More
Direban motar da jirgin ƙasa ya yi awon gaba da ita a Legas, ya nemi afuwa

Direban motar da jirgin ƙasa ya yi awon gaba da ita a Legas, ya nemi afuwa

Daga BASHIR ISAH Direban bas ɗin da ta yi hatsari da jirgin ƙasa ran Alhamis da ta gabata a Legas, Oluwaseun Osinbajo, ya nemi afuwar waɗanda hatsarin ya rutsa da su a cikin motar. Direban ya yi zargin matsalar da motar ke fama da ita a wannan lokaci ya sa hakan ta faru. Tuni dai aka tura direban, wanda ma'aikaci ne a Ma'aikatar Sufuri ta Jihar Legas, Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar don gudanar da bincike kan aukuwar hatsarin. Motar da lamarin ya shafa ta yi taho-mu-gama da jirgin ƙasan ne ɗauke da ma'aikatan da ke ƙoƙarin zuwa wajen…
Read More
Me ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya?

Me ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ai duk masu sharhi na magana kan abin da ya biyo bayan babban zaɓen Nijeriya na 2023 inda hakan ya kawo lokacin da shugaban da ke kan gado Muhammadu Buhari ke shirin ajiye mulki ranar 29 ga watan mayu don ƙarewar wa’adin mulkin saka gabaɗaya bisa tandain tsarin mulki. Bayan kammala zaɓen da aka haqqaqe ya fi kowanne raba kan ’yan Nijeriya ta fuskar bambancin addini da ƙabilanci har ma da vangaranci, hakan wani darasi da kowane mai hankali ya kamata ya zauna shi kaɗai ya yi nazarin makomar Nijeriya kafin ma a je ga makomar…
Read More
Matsalar mutuwar mata masu juna biyu a Nijeriya

Matsalar mutuwar mata masu juna biyu a Nijeriya

Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa ƙasashe masu tasowa tuwo a ƙwarya. Alal misali, ƙasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa; amma a ƙasashe masu tasowa har wajen mata 100-300 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa. Wani sabon rahoton da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar na cewa a duk minti biyu mace na mutuwa a duniya yayin da take ɗauke da juna biyu ko haihuwa. Hakan na ƙara nuna rashin…
Read More
Akwai alaƙa mai kyau tsakanina da gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashinsu  – Gawuna

Akwai alaƙa mai kyau tsakanina da gwamnonin da na yi aiki ƙarƙashinsu – Gawuna

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewar akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da dukkanin gwamnonin da ya yi aiki ƙarƙashinsu a jihar. Gawuna ya bayyana hakan ne a gidan Talabijin na TVC a cikin shirin “Countdown Nigeria Decides 2023” da aka yi tare da shi. A cewarsa, “Ina da kyakkyawar alaƙa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da sauran tsofaffin gwamnonin da na yi aiki da su a gwamnatocin baya a matsayin shugaban ƙaramar hukuma, kwamishina da kuma a yanzu a matsayina na Mataimakin…
Read More
Hukumar tsaro ta damƙe mutum 4 da jabun sabon kuɗi na N1.9m

Hukumar tsaro ta damƙe mutum 4 da jabun sabon kuɗi na N1.9m

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta kama wasu mutum huɗu da suka ƙware wajen buga jabun kuɗaɗe. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma'a, Kakakin NSCDC, Kwamanda Olusola Odumosu, ya ce an damƙe waɗanda lamarin ya shafa ne a garin Jos, babban birnin Jihar Filato. A cewar Odumosu sun kama tawagar farko da ta ƙunshi mutum huɗu da jabun kuɗi Dala 64,800 fa kuma Naira 475,000. Yayin da suka kama tawaga ta biyu mai ƙunshe da mutum biyar ɗauke da jabun Naira miliyan 1.5. Ya ce duka waɗanda aka kama ɗin 'yan shekara tsakanin 24 zuwa 56.
Read More