11
Mar
Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Zaɓaɓɓen sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne jita-jitar da ke yawo cewar yana mara wa wata jam'iyya baya a zaɓen gwamna da ke tafe. Mataimaki na musamman ga Sanata Sumaila a kan yaɗa labarai, Abbas Adam Abbas, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar a Kano Abbas ya ce, wannan labari ba shi da tushe balle makama. Ya bayyana cewa wasu masu neman tayar da zaune tsaye gami da yarfen siyasa ne ke yaɗa wannan labari na…
