Editor

9513 Posts
Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani yanayi mai nuna alamun kutingwila ga lashe zaɓen 2023 da zavavven Shugaban Ƙasa mai jiran gado a Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi, wasu ’yan Nijeriya da dama mazauna Birnin Landon, Babban Birnin Ƙasar Ingila, sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar dake birnin Landan ɗin na ƙasar Birtaniya. Wannan ya faru ne jim kaɗan bayan Chatham House ya soki lamarin yadda aka tattara sakamakon zaɓen, wanda ya bai wa Tinubun nasara, inda gidan na dimukraɗiyya ya ce, ba a bi qa’idojin zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman…
Read More
Zannan Kwankwasiyya ya raba tallafin injinan bada wuta ga makarantun islamiyya a Jihar Kano

Zannan Kwankwasiyya ya raba tallafin injinan bada wuta ga makarantun islamiyya a Jihar Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jigo a tafiyar Kwankwasiyya a qaramar hukumar Nasarawa, Alhaji Abubakar Yahuza Gama, Zannan Kwankwasiyya ya tallafa wa wata ɗaliba Fatima Aminu da ta yi nasarar zama ta ɗaya a musabaƙar karatun Ƙur'ani da kayan ɗaki tare da bai wa makarantun Islamiyya 48 injinan bada wutar lantarki don haskaka makarantun, ƙarƙashin ƙungiyar haɗin kan makarantun Islamiyya. A yayin taron da aka gudanar a ɗakin taro na Mento a ranar Alhamis, Zannan na Kwankwasiyya ya kuma bada kyautar firji guda biyar ga ɗaliban makarantun Islamiyya da suka yi nasara a musabaƙa na Sira da sauran fannoni na…
Read More
Yuguda ya bayyana Tinubu a matsayin mai amana

Yuguda ya bayyana Tinubu a matsayin mai amana

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya bayyana dalilansa na goyon bayan shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya danganta da riƙon amanarsa, musamman tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari. "Kamar yadda muka sani, Allah ya yi ikonSa, Tinubu shi ne sanadi da ya sanya masoyinmu Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasar Nijeriya. Inda bai ba shi goyon baya ba, bani tsammani zai kasance shugaba, in bacin wata ƙaddara ta Ubangiji," inji Yuguda. Yuguda, wanda yake yi wa manema labarai jawabi a garin Bauchi, ya kuma bayyana cewar, "Tinubu ya riƙe mu da amana, dalili…
Read More
Ranar Mata: Ƙungiya ta horar da mata 100 girki a Kano

Ranar Mata: Ƙungiya ta horar da mata 100 girki a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar Northern Chef Kamal Foundation ta horar da mata guda 100 dabarub girke-girke daban-daban, saboda ƙaratowar azumi, da ya  gudana a ranar Laraba a Unguwar Hotoro dake Kano, inda taron ya zo daidai da Ranar Mata ta Duniya. Da yake jawabi a wajen, shugaban ƙungiyar kuma wanda ya ƙirƙiri ƙungiyar Chef Kamal Ahmad ya ce ƙungiyar ta shirya taron ne domin horar da mata 100 da kuma murnar zagayowar ranar mata ta duniya. Ya ce babban maƙasudin horarswar shi ne samar da ingantaccen abinci mai gina jiki musamman a wannan wata na azumin Ramadan da…
Read More
Zan bai wa ƙananan hukumomi ’yancin kansu idan na zama Gwamnan Kano, Cewar Gawuna

Zan bai wa ƙananan hukumomi ’yancin kansu idan na zama Gwamnan Kano, Cewar Gawuna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alƙawarin bai wa ƙananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Kano. Gawuna ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wani shiri na gidan talabijin ɗin NTA mai suna “The Balot”. Ya ce: “Ƙananan hukumomi wani ɓangare ne na gwamnati wanda ya fi kusa da jama’a wanda ke taimakawa wajen cigaban al’umma ta kowacce fuska," inji Gawuna. “A matsayina na tsohon shugaban ƙaramar hukumar na san abin da ya shafi…
Read More
Mutane da dama sun rasu a taho-mu-gamar motar bas da ta siminti

Mutane da dama sun rasu a taho-mu-gamar motar bas da ta siminti

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aƙalla mutane 10 ne ake fargabar sun mutu sakamakon wani karo da wata motar bas ta kasuwanci da wata babbar mota maƙare da siminti a hanyar Inugu zuwa Onitsha. Haɗarin ya afku ne da misalin ƙarfe 9 na safe kusa da tashar motar CBN dake Inugu a ranar Alhamis, 9 ga watan Maris, 2023. Rahotanni sun bayyana cewa, motar bas mai ɗauke da mutane 18 mai lamba Enugu XL884 ENU ta shiga cikin wata tirela mai shigowa ɗauke da buhunan siminti. Motocin biyu suna tafiya ne a kan hanya ɗaya sakamakon munanan ramika da…
Read More
Ɗan sane ya sace wayar Kalu yana tsaka da karɓar takardar shaidar cin zaɓe a Abuja

Ɗan sane ya sace wayar Kalu yana tsaka da karɓar takardar shaidar cin zaɓe a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu masu sane da ba a san ko su waye ba sun sace wayar Sanata mai wakiltar mazaɓar Abiya ta Arewa, Orji Uzor Kalu, a lokacin da ya je karɓar takardar shaidar lashe zaɓe a ɗakin taro na International Conference Centre a Abuja. Sanatan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa ta shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Alhamis, 9 ga Maris, 2023. Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa, wayar salular da wani wanda har yanzu ba a tantance ba ya sace na ɗauke da layukansa na MTN da Glo.…
Read More
Ɗan Chana ya fallasa abubuwan ta’ajibi a shari’ar kisan Ummita

Ɗan Chana ya fallasa abubuwan ta’ajibi a shari’ar kisan Ummita

*Ba na roƙon kada a kashe ni, inji shi Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan ƙasar Chana ɗin nan mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47 da ake tuhuma da laifin kashe masoyiyarsa, jiya Alhamis ya sake faɗa wa kotu a Kano cewa bai taɓa niyyar kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya mai suna Ummukulsum Sani 'yar shekara 22, da aka fi sani da Ummita ba. Wanda ake tuhumar, mazaunin Railway Quarters a Kano, ana tuhumar sa da laifin kisan kai. Da lauyan gwamnati, Musa Lawal ke tambayar dalilin sa na zuwa gidan su Ummita ba tare da gayyata ba,…
Read More
HOTUNA: Yadda aka gudanar da jana’izar hamshaƙin ɗan kasuwa, Sani Dahiru Yakasai

HOTUNA: Yadda aka gudanar da jana’izar hamshaƙin ɗan kasuwa, Sani Dahiru Yakasai

A ranar Juma'a aka gudanar da jana'izar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Sani Dahiri Yakasai. An gudanar da sallar jana'izar ce a Fadar Sarkin Kano. Ranar Alhamis Allah Ya yi wa marigayin cikawa a ofishinsa bayan fama da rashin lafiya. Mahalarta jana'izar sun haɗa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Ibrahim Shekarau, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran ɗaruruwan Musulmi.
Read More
Sanatan Kano ta Tsakiya: Kotu ta maye gurbin Shekarau da Rufai Hanga

Sanatan Kano ta Tsakiya: Kotu ta maye gurbin Shekarau da Rufai Hanga

Daga WAKILINMU Kotun Ƙoli ta maye sunan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau da na Rufai Hanga a matsayin zaɓaɓɓen Sanata na Kano ta Tsakiya karƙashin Jam'iyyar NNPP. Da yake yanke hukunci kan ƙarar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ɗaukaka kan hukuncin da Babbar Kotu mai zamanta a Abuja ta yanke da farko, Alƙalin Koton Ƙolin ya tabbatar da Hanga a matsayin ɗan takarar NNPP. Tun farko, Babbar Kotun Tarayya da Kotun Ɗaukaka Ƙara sun tabbatar da Rufai Hanga a matsayin Ɗan Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam'iyyar NNPP biyo bayan janyewa da Ibrahim Shekarau ya yi…
Read More