Editor

9513 Posts
Chelsea ta kai zagayen daf da kusa da ƙarshe a gasar Zakarun Turai

Chelsea ta kai zagayen daf da kusa da ƙarshe a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Chelsea ta farfaɗo da fatanta a kakar wasan bana, bayan da ta doke Borussia Dortmud da ci 2 da nema a karawar da suka yi a Stamford Bridge, inda a yanzu ta kai zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a gasar zakarun Turai. Raheem Sterling ne ya fara jefawa Chelsea ƙwallo kafin Kai Havertz ya jefa ta biyo a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Mai horar da ƙungiyar Graham Potter na fuskantar matsin lamba bayan da kwalliya ta gaza biyan kuɗin sabulu, ganin yadda ƙungiyar ta kafa tarihin…
Read More
Gbajabiamila na shirin zama shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a gwamnatin Tinubu

Gbajabiamila na shirin zama shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa a gwamnatin Tinubu

Daga WAKILINMU Alamu sun nuna Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, na shirin zama shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa ga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, a gwamnati mai zuwa. Bayanai sun ce hakan ba ya rasa nasaba da ƙin zuwa karɓar shaidar lashe zaɓe da Gbajabiamila ɗin ya yi inda INEC ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan Majalisar Wakilai da suka kai bantensu a ranar Larabar da ta gabata a Abuja. An sake zaɓar Gbajabiamila don wakilcin yankin Surulere 1 a Jihar Legas, wanda wannan ya zama karo na shida da yake lashe zaɓe a shiyyar.…
Read More
Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Yadda aka tirsasa ni tafka maguɗin zaɓe don APC ta samu nasara – Farfesa Yakasai

Daga WAKILINMU Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana yadda aka tilasta masa tafka maguɗi a sakamakon zaɓe a matsayinsa na Baturen Zaɓe a yankin Tudun Wadah, Kano, yayin zaɓen da ya gudana. Cikin wasiƙar da ya aika wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Ibrahim Yakasai ya aibata sakamakon zaɓen da ya bayyana bayan kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya. A cewarsa, tilasta masa aka yi kan ya tafka maguɗin zaɓe bayan da aka jefa rayuwarsa cikin haɗari a zahiri. Ya ce galibin sakamakon zaɓen da jami’an zaɓe suka bayyana ba na…
Read More
Mulki da sha’aninsa

Mulki da sha’aninsa

Daga MUHAMMAD MAHMUD MUSTAPHA Himma ba ta ga rago! Malam Ali Zarnuji na cewa a Ta'alimi, "ma'abota himma ne kawai ke samun manya-manyan matsayai a duniya da lahira." Babu abinda Allah ba ya bayarwa a dalilin himma in ji ma'abota hikima. Imam al-Gazali a Sirrul Alamina yana cewa: "maɗaukakiyar himma kan sanya mutum ya samu har abinda bai cancanci ya samu ba a zahiri". Almajirai, talakawa, bayi da ‘ya’yansu da yawa sun zama manyan sarakuna da shugabanni saboda maɗaukakiyar himmar da suka samu daga baya. Mahaifin Zulƙarnaini, Sarkin duniya, inji masu tarihi, masaƙi ne. Zulƙarnaini a maraya ya taso. An…
Read More
Sarakunan Machina, Nguru da Bade sun sha alwashin mara wa sojoji baya kan yaƙi da matsalar tsaro

Sarakunan Machina, Nguru da Bade sun sha alwashin mara wa sojoji baya kan yaƙi da matsalar tsaro

Daga BASHIR ISAH Sarkin Machina, Alh Dr. Bashir Albishir Bukar (OON) da na Nguru, Alh Mustapha Ibn Mai Kyari da kuma Sarkin Bade, Alh Mai Abubakar Umar Suleiman, baki ɗayansu a Jihar Yobe, sun sha alwashin mara wa sojoji baya don ci gaba da yaƙi da matsalolin tsaro musmaman a shiyyar Arewa maso Gabas. Sarakunan sun bayyana hakan ne sa'ilin da dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) mai yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabas ta kai musu ziyara a ranar Talata. Rundunar ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso, ta ziyarci sarakunan ne domin ci gaba da neman…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta tsare tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a kurkuku

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta tsare tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a kurkuku

Daga WAKILINMU Kotun Majastare mai zamanta a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ta tsare tsohon Mataimakin Gwamnan Imo, Gerald Irona, a gidan yari. Alƙalin kotun, C.N Ezerioha ne ya ba da umarnin haka yayin zaman kotun a ranar Alhamis. A ranar Laraba ‘yan sanda suka cafke Irona a gidansa da ke Owerri kafin daga bisani aka gurfana da shi a kotu. A cewar ‘yan sanda, an kama shi ne saboda furucin tada fitina da ya yi a Kotun Ƙoli yayin da ake shari’a tsakanin Gwamnan Hope Uzodimma da tsohon Gwamna Emeka Ihedioha.
Read More
Zaɓen 2023: Gwamnati ta tsawaita hutun manyan makarantu

Zaɓen 2023: Gwamnati ta tsawaita hutun manyan makarantu

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta tsawaita hutun da ta ba wa manyan makarantu albarkacin zaɓuɓɓukan 2023. Gwamnati ta tsawai hutun ne sakamakon ɗage zaɓen gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi da Hukumar Zaɓe, INEC, ta yi zuwa ranar 18 ga Maris. Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana tsawaita wa’adin hutun, inda ya ce ya zuwa 20 ga Maris, 2023 makarantun da lamarin ya shafa za su koma bakin aiki. INEC ta ce ta ɗage zaɓen ne domin ba ta damar sake saita na’urorin BVAS da za a yi amfani da su yayin zaɓen na gwamnoni. Da fari INEC…
Read More
TikTok ya gamu da cikas

TikTok ya gamu da cikas

Daga BASHIR ISAH A safiyar ranar Alhamis dandalin TikTok ya gamu da cikas, lamarin da ya jefa dubban masu amfani da manhajarsa a faɗin duniya cikin mawuyacin hali. A cewar shafin intanet na DownDetector mai bibiyar ire-iren waɗannan batutuwa, matsalar ta fara ne da misalin ƙarfe 09:40 agogon GMT daidai da ƙarfe 04:40 agogon ET. Ya zuwa haɗa wannan labari, kimanin mutum 3,000 sun shigar da ƙorafi rashin aikin manhajar TikTok mallakar wani kamfanin Chana mai suna ByteDance. Masu amfani da manhajar a sassan duniya, ciki har da mazauna Birtaniya da London, ne suka yi ƙorafi kan matsalar da aka…
Read More
Ana fargabar mutum da dama sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa da mota a Legas

Ana fargabar mutum da dama sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa da mota a Legas

Dag BASHIR ISAH Ana fargabar mutanen da ba a tantance adadinsu ba sun mutu, sannan da dama sun jikkata sakamakon hatsarin da ya auku tsakanin jirgin ƙasa da wata mota bas (BRT) da safiyar Alhamis a Legas. Wani mai amfani da kafar Tiwita, @Trutfully83, shi ne ya bayyana hakan a shafinsa. Inda ya wallafa cewar "an samu aukuwar hatsari motar BRT mai ɗauke da fasinjoji da kuma jirgin ƙasa a yankin Ikeja a Legas. "Ba a tantance adadin waɗanda suka mutu ba a wannan lokaci, amma waɗanda hatsarin ya rutsa da su ɗin na buƙatar kulawar gaggawa," in ji shi.…
Read More
Tun Ina firamare na fara rubutu – Gimbiya Rahma

Tun Ina firamare na fara rubutu – Gimbiya Rahma

"Marubuta a dinga bincike kafin rubutu" Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Sanannen abu ne, rubutun adabi ya ta shi daga hannun masu buga littafai zuwa yanar gizo, wanda hakan ne ya ba wa matasa damar baje basirarsu ba tare da tunanin fara neman kuɗin buga littafi ba. Ta dalilin hakan ya sa ake samun marubuta da yawa masu rubutu kuma mai ma'ana, hakan ya tabbatar da cewa, matasan marubuta na matuƙar ƙoƙari wurin samar da labarai da za su ƙayatar da masu karatu. Duk da cewa, an yi ammana rubutun intanet ba karɓe wa marubuta kasuwa ya yi ba, samar…
Read More