Editor

9513 Posts
Kotu ta amince da buƙatar INEC kan sake saita na’urorin BVAS

Kotu ta amince da buƙatar INEC kan sake saita na’urorin BVAS

Daga BASHIR ISAH Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, damar sake seta na'urorin BVAS da ta yi amfani da su a zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisun tarayya. Yayin zaman kotun a ranar Laraba, ta ce hana INEC sake seta na'urorin zai shafi zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da za a gudanar a gaba. Ta yi watsi da ƙorafin da Jam'iyyar Labour da ɗan takararta Peter Obi suka yi kan yunƙurin da INEC ɗin ta yi na sake seta na'urorin BVAS da aka yi amfani da su. Kotun ta…
Read More
Kotu ta yi watsi da buƙatar INEC ta neman sauya damar bincikar kayan zaɓen da aka ba wa su Atiku

Kotu ta yi watsi da buƙatar INEC ta neman sauya damar bincikar kayan zaɓen da aka ba wa su Atiku

Daga BASHIR ISAH Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi watsi da buƙatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta neman a dakatar da damar da aka bai wa 'yan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi, bincikar kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa. A ranar Juma'ar da ta gabata kotu ta bai wa Atiku da Obi damar bincikar kayan zaɓe bayan da suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da Bola Tinubu na Jam'iyyar APC ya samu ta lashe zaɓen. Atiku da Obi sun nuna rashin…
Read More
INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da mako guda

INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi da mako guda

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kammala shirinta don ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi wanda ta shirya gudanarwa ran 11 ga Maris. Yadda al'amarin yake yanzu, shi ne, INEC ta ɗage zaɓe da mako guda zuwa ranar 18 ga Maris, 2023, kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar News Point Nigeria. Manhaja ta gano ɗage zaɓen na da nasaba da gazawar INEC wajen saita na'urar BVAS ɗin da aka yi amfani da su a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu don sake yin amfani da su wajen gudanar da zaɓen gwamnoni. Majiya…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bai wa Tinubu damar bincikar kayayyakin zaɓe

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bai wa Tinubu damar bincikar kayayyakin zaɓe

Daga BASHIR ISAH Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) mai zamanta a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta bai wa Hukumar Zaɓe (INEC), umarnin ta bai wa zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado Bola Tinubu, damar bincikar muhimman kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanarda zaɓen Shugaban Ƙasa. Tinubu da Jam'iyyar APC sun buƙaci kotu ta ba su damar duba kayayyakin zaɓen ne domin tattara bayanan da za su yi amfani da su wajen kare kansu a kotu daga ƙara da aka shigar a kansu. 'Yan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar…
Read More
Sanatoci sun karɓi shaidar lashe zaɓensu

Sanatoci sun karɓi shaidar lashe zaɓensu

Daga BASHIR ISAH A ranar Talata Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga sanatocin da suka yi nasara a zaɓen da ya gabta. Shugaban INEC na ƙasa, Mahmood Yakubu, shi ne ya jagoranci miƙa shaidar ga sanatocin wanda ya gudana a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja. A jawabin da ya yi ran Asabar da ta gabata, Yakubu ya ce 423 ne suka lashe kujerun majalisun tarayya, yayin da za a sake zaɓe a wasu mazaɓu 46. Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da sanatoci 98 daga cikin 109 da ake da…
Read More
INEC ta miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Wakilai shaidar lashe zaɓe

INEC ta miƙa wa zaɓaɓɓun ‘yan Majalisar Wakilai shaidar lashe zaɓe

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga 'yan Majalisar Wakilai da suka lashe zaɓe a zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu. A ranar Laraba INEC ta miƙa wa 'yan majalisar shaidarsu a Babban Zauren Taro na Ƙasa da Ƙasa da ke Abuja. Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da sanatoci 98 daga cikin 109 da ake da su, sai kuma 'yan Majalisar Wakilai 325 daha cikin 360 da ake da su.
Read More
Ba mu umarci bankuna su bada tsofaffin takardun kuɗi ba – CBN

Ba mu umarci bankuna su bada tsofaffin takardun kuɗi ba – CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Bankin Nijeriya (CBN) a ranar Talata ya ce bai bayar da wani sabon umarni ga bankunan kasuwanci ba kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata na bayar da umarnin a riqa rarraba tsofaffin takardun Naira tare da sabbi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba. Kwamitin alqalai na mutane bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro, ya bayyana a matsayin wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa, akan umarnin da Shugaban Ƙasa ya bada. Muhammadu Buhari ya bai wa Babban Bankin Ƙasar CBN na sake gyarawa…
Read More
Masari ya karɓi jiga-jigan PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC

Masari ya karɓi jiga-jigan PDP da suka sauya sheƙa zuwa APC

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP tare da magoya bayansu 10,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Katsina. Akasarin waɗanda suka kwashe kayansu daga jam'iyyar ta PDP zuwa APC na hannun daman tsohon gwamnan jihar ne, wato Ibrahim Shehu Shema. Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya karɓe su a gidan gwamnatin jihar. Sauya sheƙar na zuwa ne 'yan kwanaki kaɗan kafin gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi a ranar Asabar, 11 ga watan Maris. Daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina Ahmed Musa Ɗangiwa ne ya bayyana wa manema…
Read More
Zaɓen 2023: Ƙalubalen da ke gaban Tinubu

Zaɓen 2023: Ƙalubalen da ke gaban Tinubu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Yanzu dai ta tabbata, Sanata Bola Ahmed Tinubu, na Jam'iyyar APC shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata, da ƙuri'u Miliyan 8 da dubu 794 da 726. Bayan ya samu kashi 25 a cikin ɗari na yawan ƙuri'un da aka kaɗa daga jihohi 30, tare da da samun mafi rinjaye ƙuri'u a jihohi 12 na tarayyar Nijeriya. Shi kuma wanda ya zo na biyu shi ne ɗan takarar shugaban qasa a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa, da ya samu ƙuri'u Miliyan 6…
Read More
DSS ta samar da kafafenta a soshiyal midiya

DSS ta samar da kafafenta a soshiyal midiya

Daga BASHIR ISAH Hukumar tsaro ta DSS, ta ce ta ƙirƙiro da shafukan sohiyal domin bunƙasa hanyoyinta na hulɗa da jama'a da masu ruwa da tsaki. Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukunar, Dr Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja. Ya ce shafukan da suka ƙirƙiro sun haɗa da:Twitter: @OfficialDSSNG Facebook: OfficialDSSNG Instagram: @OfficialDSSNG A cewarsa, shafin Tiwita na PRO na hukumar shi ne: @DrAfunanya_PNA. Ya ce kafin wannan lokaci hukumar ba ta da waɗanan kafafe, kuma tana sa ran soma amfani da su ne daga ranar 6 ga Maris. Jami'in ya ce al'umma su sani cewar,…
Read More