08
Mar
Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta ce ta kammala shirinta don karrama Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da lambar yabo saboda nasarorin da ya samu a fannin tsaro da dimokuraɗiyya. Wannan na zuwa ne yayin da Buhari yake shirin kammala wa'adin mulkinsa na biyu. Shugaban ECOWAS kuma Shugaban Ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, shi ne ya bayyana haka a wajen taron ƙawancen da suka yi yayin da suka haɗu a wajen Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a Doha, babban birnin Qatar. Shugaba Embalo ya ce Buhari ya taka rawar gani…
