24
Nov
Daga SAMINU HASSAN A wannan lokaci da muke cikin yanayi na dunƙulewar al’ummun duniya wuri guda, hidimomin sadarwa na da matuƙar muhimmanci, kasancewar suna buɗe ƙarin ƙofofin raya tattalin arziki, da kyautata zamantakewar al’ummu daban daban. Kaza lika damar sadarwa tsakanin al’ummun duniya ta riga ta zama ɗaya daga cikin hidimomi masu daraja na more rayuwar bil adama. Hakan ne ma ya sa ƙarƙashin kyawawan manufofin ƙasar Sin, gwamnati ke ƙarfafa gwiwar sassa daban daban, musamman kamfanonin ƙasar da su tallafa, wajen bunƙasa samar da ababen more rayuwa ga al’ummun duniya a duk inda suke. A baya bayan nan, kamfanin…
