Editor

9513 Posts
Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun N200, N500 da N1000

Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun N200, N500 da N1000

Daga WAKILINMU A ranar Laraba Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1000 bayan sake musu fasali. Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira ɗin ne a wajen taron Majalisar Zartarwa a Abuja. Idan za a iya tunawa, ranar 26 ga Oktoba n 2022, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba da sanarwar shirin Gwamnatin na neman sake fasalin takardun kuɗin da lamarin ya shafa. Tare da cewa, an ɗauki matakin hakan ne domin kula da kuɗaɗen da ke hannun 'yan ƙasa ana hada-hada da su. CBN ya ce tsaffin takardun Naira da…
Read More
Hukuma ta gargaɗi masu fassara fina-finan ƙetare

Hukuma ta gargaɗi masu fassara fina-finan ƙetare

Daga BASHIR ISAH Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa reshen Arewa maso Yamma, ta gargaɗi masu dobin, fassarawa da safarar fina-finan ƙetare ta haramtacciyar hanya da su gaggauta barin wannan harka. Gargaɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Nuwamba da kuma sa hannun Jami'i mai kula da harkokin hukumar a shiyyar Arewa maso Yamma, Umar G. Fage. Hukumar ta ce fassara fina-finan ƙetare zuwa harsunan gida ba bisa ƙa'ida ba laifi ne da ya saɓa wa sassa na 25(1), 33(1), 56 da 5(1) na Kundin Dokokin hukumar na 1993. Wannan hali…
Read More
Girgizar ƙasa ta kashe mutum 268 a Indonesiya

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 268 a Indonesiya

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga ƙasar Indonesia sun ce aƙalla mutum 268 ne suka mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a tsibirin Java da ke ƙasar. Bayanai sun ce iftila'in ya rutsa har da ɗaliban makaranta. Girgizar ƙasar wadda ta auku ranar Litinin da ta gabata, ta kai ƙarfin maki 5.6 ta yi sanadiyyar lalacewar gidaje da daman gaske a yankin. Kazalika, hatsarin ya jikkata mutum 700 tare da lalata ɗimbin dukiya kamar yadda hukumomin ƙasar suka bayyana. Masana sun ce yanayin ƙasar ya sa ake yawan samun aukuwar girgizar ƙasa a Indonesia.
Read More
Ronaldo ya raba gari da Manchester United

Ronaldo ya raba gari da Manchester United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren ɗan wasan gaban Portugal, Christiano Ronaldo ya bayyana cewa, bayan cimma yarjejeniya da ƙungiyar Manchester United, ya raba gari da ita ba tare da ɓata lokaci ba. Ronaldo ya ce, "ina son Manchester United, kuma soyayyar da nake yiwa magoya baya ba za ta sauya ba." Ɗan wasan na Portugal ya ce, barin ƙungiyar ya zo masa a daidai, don haka zai cigaba da mayar da hankali a fagen ƙwallon ƙafa. Sanarwar da Ronaldo ya fitar a shafinsa na Instagram, ya ce, yana yiwa tsohuwar ƙungiyar tasa fatan samun nasarori a nan gaba. Wannan matakin…
Read More
Saudiyya ta ayyana gobe Laraba a matsayin hutun aiki sakamakon doke ƙasar Argentina

Saudiyya ta ayyana gobe Laraba a matsayin hutun aiki sakamakon doke ƙasar Argentina

Daga IBRAHIM HAMISU Sarki ƙasar Saudiyya Salman bin Abdul Aziz, ya ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar wani mataki na murnar samun nasara da tawagar 'yan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar suka samu a kan ƙasar Argentina. An dai tashi wasan ne Saudiyya ta samu nasara a kan Argentina da ci 2-1 a wasan farko da suka buga a filin wasa na Lusail. Ƙasar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanar wa da ta fitar a ranarTalata. Sanarwar ta ce, Sarkin ya bayar da hutun ne domin 'yan ƙasar tun daga ma’aikatan gwamnati da ma’aikatu masu…
Read More
Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun Naira ran Laraba

Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun Naira ran Laraba

Daga BASHIR ISAH A wannan Larabar ake sa ran Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali. Takardun Naira da aka sake wa fasalin sun haɗa da N1,000 da N500 da kuma N200. Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ranar Talata a wajen taron da bankin ya saba gudanarwa duk wata a Abuja. Shugaban CBN ya ce ba za a ƙara wa'adin da aka tsayar ba tun farko don mayar da tsofoffin tarkadun Naira da sauyin ya shafa zuwa banki. A ranar 26 ga Oktoba Emefiele ya ba…
Read More
Ministar Jinƙai ta fallasa yadda Ministar Kuɗi ta yi cushen kasafin Naira Biliyan 206

Ministar Jinƙai ta fallasa yadda Ministar Kuɗi ta yi cushen kasafin Naira Biliyan 206

Daga SANI AHMAD GIWA Majalisar Dattawan Nijeriya za ta gayyaci Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare ta qasar, Zainab Ahmed, don ta je gaban Kwamitin Kula da Ayyuka na Musamman a majalisar ta bayyana musu yadda Ministar Jinƙai da Agaji, Sadiya Umar Farouq, ta yi zargin Ministar Kuɗin da yin cushen Naira biliyan 206 a cikin kasafin 2023 na Ma'aikatar Jinqai ta Tarayya. Kiranyen ya biyo bayan wani ƙorafi da Minista Sadiya ta yi cewa ma'aikatarta ba ta da masaniyar yadda aka yi cushen zunzurutun kuɗaɗe har Naira biliyan 206 a cikin kasafin na 2023. Sadiya Farouq, wadda ta bayyana a…
Read More
Saudiyya ta girgiza Messi na Argentina bayan da ta yi nasara a gasar kofin duniya

Saudiyya ta girgiza Messi na Argentina bayan da ta yi nasara a gasar kofin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙasar Saudiyya ta ba wa ƙasar Argentina makaki bayan da ɗan wasanta Salem Al-Dawsari ya zura ƙwallo a raga yayin da Lionel Messi ya soke bugun daga kai sai mai tsaron gida. Saudiyya ta samar da ɗaya daga cikin mafi girman tarihin gasar kofin duniya yayin da Salem Al-Dawsari ya taka rawar gani a gasar inda ya samu nasarar doke Argentina da ci 2-1 a rukunin C a filin wasa na Lusail Iconic. Lokaci ya tsaya cak yayin da Al-Dawsari ya fitar da ƙwallon daga sama ya juya cikin ’yan wasan baya na Argentina guda biyu…
Read More
Ronaldo ya zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 500 a Instagram

Ronaldo ya zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 500 a Instagram

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaban Portugal, Cristiano Ronaldo ya zama mutum na farko da ya fara samun mabiya miliyan 500 a manhajar Instagram, miliyan 124 fiye da Lionel Messi, wanda ya zo na 2. Shahararren ɗan wasan Manchester United ne mutane suka fi bibiyar a Instagram, kuma ya zama mutum na farko da ya haura mabiya miliyan 500 a shahararren dandalin sada zumuntar. Ronaldo kuma shi ne gaba ɗaya wanda ya fi yawan mabiya a Instagram, da kuma a Facebook. Lionel Messi na biyu yana da mabiya sama da miliyan 376 a Instagram.
Read More
An yi ganawa tsakanin ministocin tsaron ƙasashen Sin da Amurka

An yi ganawa tsakanin ministocin tsaron ƙasashen Sin da Amurka

Daga CMG HAUSA Yau Talata, ministan tsaron ƙasar Sin Wei Fenghe wanda ke halartar taron ministocin tsaron ƙasashen ASEAN karo na 9 da ke gudana a Cambodiya, ya gana tare da takwaransa na ƙasar Amurka Lloyd Austin bisa gayyatar da ya yi masa. Ɓangarorin biyu na ganin cewa, ya kamata sojojin ƙasashen biyu su yi ƙoƙarin tabbatar da matsaya ɗaya da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma. Yayin ganawar tasu, Wei Fenghe ya nanata matsayin Sin kan batun yankin Taiwan. Ya ce, batun yankin Taiwan yana da muhimmanci ga muradun ƙasar Sin, da ma hulɗar ƙasashen biyu. Taiwan wani yanki na…
Read More