22
Nov
Daga BELLO WANG Wasu abubuwa guda 2 da suka faru a kwanan baya sun nuna haɗin gwiwar ƙut da ƙut da ƙasashen Afirka da ƙasar Sin suke yi a fannin kula da harkokin ƙasa da ƙasa. Ɗaya shi ne yadda Afirka da Sin suka haɗa kai wajen tabbatar da an zartas da ƙudurin kafa asusun biyan diya ga ƙasashe masu tasowa, wadanda suka samu hasara sakamakon bala’un da sauyawar yanayin duniya ke haddasawa, a taron ɓangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyawar yanayi ta MƊD na COP27, wanda ya kasance wata babbar nasarar da ƙasashe masu tasowa suka…
