Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun Naira ran Laraba

Daga BASHIR ISAH

A wannan Larabar ake sa ran Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali.

Takardun Naira da aka sake wa fasalin sun haɗa da N1,000 da N500 da kuma N200.

Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ranar Talata a wajen taron da bankin ya saba gudanarwa duk wata a Abuja.

Shugaban CBN ya ce ba za a ƙara wa’adin da aka tsayar ba tun farko don mayar da tsofoffin tarkadun Naira da sauyin ya shafa zuwa banki.

A ranar 26 ga Oktoba Emefiele ya ba da sanarwar cewa, ya zuwa ran 15 ga Disamba CBN zai saki sabbin tarkadun Naira na N200, N500, da N1,000, sannan tsaffin za su ci gaba da aiki har zuwa 31 ga Janairun 2023.

Amma kuma sai aka ji shi ranar Talata ya yi mi’ara- koma-baya, inda ya ce CBN ba zai iya jira zuwa 15 ga Disamba don ƙaddamar da sabbin tarkun Naira ɗin ba, yana mai cewa Laraba mai zuwa Shugaba Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun na Naira.