Ministar Jinƙai ta fallasa yadda Ministar Kuɗi ta yi cushen kasafin Naira Biliyan 206

Daga SANI AHMAD GIWA

Majalisar Dattawan Nijeriya za ta gayyaci Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare ta qasar, Zainab Ahmed, don ta je gaban Kwamitin Kula da Ayyuka na Musamman a majalisar ta bayyana musu yadda Ministar Jinƙai da Agaji, Sadiya Umar Farouq, ta yi zargin Ministar Kuɗin da yin cushen Naira biliyan 206 a cikin kasafin 2023 na Ma’aikatar Jinqai ta Tarayya.

Kiranyen ya biyo bayan wani ƙorafi da Minista Sadiya ta yi cewa ma’aikatarta ba ta da masaniyar yadda aka yi cushen zunzurutun kuɗaɗe har Naira biliyan 206 a cikin kasafin na 2023.

Sadiya Farouq, wadda ta bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Kula da Ayyuka na Musamman, don kare kasafin kuɗin 2023, ta yi iƙirarin cewa ma’aikatar ta buƙaci a biya wasu ayyuka na Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa maso Gabas, NEDC, da shirin National Social Safety Net Project a kasafin kuɗin 2022 da ba a fitar da su ba.

A cewarta ta yi mamakin cewa yanzu an ninka kuɗin da 10 a kasafin kuɗin 2023.
Hakan ya biyo bayan tambayar ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin, Sanata Elisha Abbo (APC Adamawa ta Arewa), game da Naira biliyan 206 da ya gabatar na ayyuka a cikin kasafin kuɗin.

A martaninta, ministar ta ce a zahiri ma’aikatar ta yi tanadin ayyukan da ke cikin kasafin kuɗin 2022, amma ba a fitar da kuɗaɗen da za a gudanar da su ba.

”Eh, mun ambato ayyukan da za mu yi da wannan kuɗi a kasafinmu na 2022 domin yin wasu ayyuka a Ma’aikatar Raya Yankin Arewa maso Gabas. To amma ba a saki kuɗin ba, kuma sai ga shi mun gan su yanzu an ninka yawansu sau 10.”

Ta ƙara da cewa ”za mu nemi bayani dalla-dalla daga Ma’aikatar Kuɗi kan yadda aka yi kuɗin ya ninka haka, duk da a baya ma ba a saki kuɗin domin yin ayyukan ba. Saboda haka za mu ji daga gare su sai mu dawo maku da bayani.”

A kan haka kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Sanata Yusuf Yusuf, ya ce zai gayyaci Ministar Kuɗi da Kasafi, Zainab Ahmed domin ta bayar da bayani kan kuɗin Naira biliyan 206 da Sadiya Farouq ta nesanta kanta da su.

Sai dai Sanata Abbo, wanda ya kaɗu da martanin da ministar ta yi, ya koka da cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da karɓar rancen kuɗi da kashe su ta hanyar almubazzaranci ba.