Editor

9513 Posts
Sama da yara miliyan ɗaya za a yi wa allurar rigakafi a Zamfara

Sama da yara miliyan ɗaya za a yi wa allurar rigakafi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Aqalla ƙananan yara 1,123, 143 miliyan ne ake sa ran za a yi wa allurar rigakafin da za a yi nan gaba a faɗin Jihar Zamfara. Mataimakin gwamnan jihar Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana haka a wani taron kwamitin yaƙi da cuttuttaka da aka gudanar a ofishin sa ranar Talata. Mataimakin gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da harkokin rigakafi a jihar ya ce, aikin rigakafin zai mayar da hankali ne kan cutar Ƙyanda, rigakafin cutar Sanƙarau, ƙarin bitamin A, takardar shaidar haihuwa da aikin rigakafin COVID-19. Ya bayyana cewa za…
Read More
Canja takardun kuɗi: EFCC za ta sa zare da masu ɓoye Naira

Canja takardun kuɗi: EFCC za ta sa zare da masu ɓoye Naira

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati  (EFCC), ta lashi takobin sanya ƙafar wando guda da dukkan masu ɓoye Naira, a yayin da CBN ta samu sahalewar shugaban ƙasa Buhari a kan canza fasalin wasu daga cikin takardun Nairorin Nijeriya.   Idan za a iya tunawa, Babban Banki Nijeriya (CBN) bayan samun sahalewar Buhari ya bayyana cewa, nan da 15 ga watan Disamba za ta fitar Da sabbin takardun Nairori waɗanda aka canza wa fasali. Takardun kuɗin da za a sauya wa fasalin sun haɗa da, takardun Naira 200, Naira 500,…
Read More
Masana sun ɗora laifin ambaliya kan al’umma da kuma watsi da gargaɗin NiMeT

Masana sun ɗora laifin ambaliya kan al’umma da kuma watsi da gargaɗin NiMeT

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ƙwararru masu fafutukar kare muhalli sun ɗora matsalar ambaliya kan halayyar wasu 'yan ƙasa da ke toshe magudanan ruwa da bola, gami da gini a kan hanyoyin ruwa, lamarin da ke haifar da ta’azzara ambaliya a cikin al’umma da garuruwa. Ƙwararru a wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya gudanar a yankin Kudu maso Kudu sun kuma ɗora laifin a kan rashin kula da shawarar gwamnati a kan lamarin. Sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da hasashen ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya, NiMeT, da Hukumar…
Read More
Kotu ta sake ƙwace wasu manyan gidaje na Diezani a Abuja

Kotu ta sake ƙwace wasu manyan gidaje na Diezani a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar da umarnin kammala ƙwace maka-makan gidaje na biliyoyin nairori, waɗanda tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Diezani Allison-Madueke ta mallaka a Abuja. Gidajen waɗanda kotun Babban Mai Shari’a Mobolaji Olajuwon ta ƙwace, sun haɗa da katafaren gida mai Lamba 1854, kan Titin Mohammed Mahashir, da ke Aso Drive. An ƙiyasta gidan zai kai Dala miliyan 2,674,418. Sai kuma gida mai Lamba 6 da ke Aso Drive a Asokoro, wanda tafkeken gidan alfarma ne na gani na faɗa, wanda Hukumar EFCC ta…
Read More
2023: Zaɓen Nijeriya zai iya shafar Afrika ta Yamma – ECOWAS

2023: Zaɓen Nijeriya zai iya shafar Afrika ta Yamma – ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar ECOWAS ta bayyana cewa zaɓen da Nijeriya za ta gudanar cikin 2023 zai iya shafar Afrika ta Yamma. Tawagar Gani Da Ido ta ECOWAS wadda ta zo Nijeriya domin ganin irin ci gaban da ake samu dangane da shirye-shiryen zaɓen 2023 ce ta bayyana cewa yanayin sakamakon zaɓen zai iya shafar Afrika ta Yamma. Sun bayyana haka a lokacin da su ka kai wa Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ziyara, ranar Litinin, a Abuja. Tawagar na ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Hukumar Zaven Ghana, Kwadwo Afadi-Gyan. Mai magana a madadin tawagar, kuma Daraktan Harkokin…
Read More
Manufar Sin ta faɗaɗa buɗe ƙofa ga waje za ta tallafawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

Manufar Sin ta faɗaɗa buɗe ƙofa ga waje za ta tallafawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

Daga SAMINU ALHASSAN Masharhanta da dama sun nazarci muhimman batutuwa da aka tattaunawa, yayin babban taron wakilan JKS na 20 da ya kammala a kwanan nan, tare da yabawa alƙawuran da shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin ya ambata, cikin jawabinsa yayin ganawa da ’yan jaridu, lokacin kammalar taron na bana, musamman ma gabar da ya ambato aniyar ƙasar sa, ta kara fadada buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje, tare da tabbatar da nasarar manufar zurfafa gyare-gyare a dukkanin fannoni, da samar da ci gaba mai nagarta. Har ma ya sha alwashin cewa, Sin za ta samar da ƙarin damammaki ga…
Read More
Shugabar Tanzania za ta zama shugabar Afirka ta farko da za ta ziyarci Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 20

Shugabar Tanzania za ta zama shugabar Afirka ta farko da za ta ziyarci Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 20

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru a yau cewa, shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta zama shugabar ƙasar Afirka ta farko da za ta ziyarci Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 20. Bisa labarin da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta bayar, bisa gayyatar da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yi mata, shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta ziyarci ƙasar Sin daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Nuwanba. Mao Ning ta bayyana cewa, a shekarar 2013, yayin da shugaban ƙasar…
Read More
Xi ya jagoranci shugabannin JKS zuwa tsohuwar hedkwatar jam’iyyar

Xi ya jagoranci shugabannin JKS zuwa tsohuwar hedkwatar jam’iyyar

Daga CMG HAUSA Sakatare janar na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci mambobin zaunannen kwamitin ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar, domin ziyartar Yan’an, wato tsohuwar hedkwatar JKS, wadda ke lardin Shaanxi na Arewa maso Yammacin ƙasar. Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban ƙasar, kuma shugaban rundunar sojinta, ya samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar da suka haɗa da Li Qiang da Zhao Leji da Wang Huning da Cai Qi da Ding Xuexiang da kuma Li Xi. Sun kuma ziyarci wajen da babban taron wakilan JKS karo na 7…
Read More
An rufe kantin Jabi Lake saboda barazanar tsaro

An rufe kantin Jabi Lake saboda barazanar tsaro

Daga BASHIR ISAH Rohotanni daga birnin tarayya Abuja, na nuni da cewa, barazanar tsaro ta sa an rufe katafaren kantin zamanin nan na Jabi Lake. Hukumar gudanarwar kantin ce ta ba da sanarwar rufe shagon a shafinta na Instagram a ranar Alhamis. A cikin sakon da ta wallafa din, hukumar ta ce an ɗauki matakin rufe kantin ne don kare rayukan ma'aikata da na kwastomomi. Ta ce tana ci gaba da tuntuɓa da neman shawarwari daga hukumomin tsaron don samun daidaito kafin daga bisani ta sanar da lokacin da za a sake buɗe kantin. Don haka hukumar ta ce tana…
Read More
Rubutu hanyar zamani ce ta isar da saƙo – Oum Nass

Rubutu hanyar zamani ce ta isar da saƙo – Oum Nass

"Ina sauya salon rubutuna kamar launin hawainiya" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Rubutu wata hanya ce ta isar da saƙo ga al'umma, ta amfani da hikima da azancin magana. Akwai marubuta da Allah ya yi wa baiwar sarrafa harshe da falsafar iya magana, kai ka ce wahayi ake yi musu. Ɗaya daga cikin su ita ce Hajara Ahmad Hussaini Maidoya, wacce aka fi sani da Oum Nass, daga ƙaramar Hukumar Haɗejia a Jihar Jigawa. Har wa yau, tana daga marubutan zube da suke cin kasuwa a harkar rubutun wasan kwaikwayo, wanda kawo yanzu wasu daga cikin rubuce rubucen da ta yi…
Read More