2023: Zaɓen Nijeriya zai iya shafar Afrika ta Yamma – ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar ECOWAS ta bayyana cewa zaɓen da Nijeriya za ta gudanar cikin 2023 zai iya shafar Afrika ta Yamma.

Tawagar Gani Da Ido ta ECOWAS wadda ta zo Nijeriya domin ganin irin ci gaban da ake samu dangane da shirye-shiryen zaɓen 2023 ce ta bayyana cewa yanayin sakamakon zaɓen zai iya shafar Afrika ta Yamma.

Sun bayyana haka a lokacin da su ka kai wa Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ziyara, ranar Litinin, a Abuja.

Tawagar na ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Hukumar Zaven Ghana, Kwadwo Afadi-Gyan.

Mai magana a madadin tawagar, kuma Daraktan Harkokin Jama’a na ECOWAS, Remi Ajibewa, ya ce ƙungiyar a kullum fatan ta shi ne tabbatar da zaɓe sahihi kuma karɓaɓɓe a ƙasashen Afrika ta Yamma, musamman ma a Nijeriya, wanda za a yi cikin 2023.

Ya ce tilas ECOWAS ta damu sosai domin ta ga an yi zaɓe lami lafiya a Nijeriya, kasancewa Nijeriya ɗin ce jagaba kuma uwa a tsakanin sauran ƙasashen Afrika ta Yamma.

“Mu na sane da muhimmancin da Nijeriya ta ke da shi a Afrika ta Yamma. Saboda idan Nijeriya ta yi atishawa, to gaba ɗayan sauran ƙasashen Afrika ta Yamma za su kamu da mura. Saboda haka ba mu fatan hakan ta faru.

“Saboda haka mun zo ne domin mu saurare ka, kuma mu ga irin shirin da ku ka yi sannan kuma mu ji irin ƙalubalen da ku ke fuskanta, yadda idan mun koma mu kai rahoto.”

Ajibewa ya ce sun zo Nijeriya ne domin ganin irin shirin da aka yi wa zaɓen 2023 tun kafin zaɓen ya zo. Ya ce hakan ya na cikin ƙa’idojin ECOWAS, kasancewar ta mai zuwa ta sa ido a lokacin zaɓe.

Ya ce sharaɗi na 12 da na 13 na 2021 ya nuna ECOWAS na da ikon naxa tawagar zuwa kowace ƙasar Afrika ta Yamma domin ta binciki irin shirin da ta yi wa zaɓen da za ta yi, musamman zaɓen shugaban ƙasa.

“Kuma dalili kenan mu ka zo Nijeriya, kuma a wannan zuwan mun rigaya mun kai siyasa Hukumar ECOWAS mai hedikwatar ta nan Abuja, inda mu ka yi wa Shugaban ECOWAS ɗin ƙarin bayanin abin da ke tafe da mu.

“Kuma mun je Ma’aikatar Harkokin Waje, mun je wurin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, kuma mun gana da wasu ƙungiyoyin jama’a, sannan ga shi mun gangaro nan INEC.

“Dalili kuwa mun tabbatar cewa INEC abokiyar mu ce, mun sha tattauna batutuwa iri ɗaya a tsakanin mu a baya.”

Cikin waɗanda za su gana da su, har da jam’iyyun siyasa, ‘yan jarida, Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa da kuma kotuna.

Farfesa Yakubu ya jinjina masu tare da cewa aikin na su ba sabon abu ba ne. Kuma ya yi masu cikakken bayanin irin shirin da INEC ta yi.