Editor

9513 Posts
Shugaban Ƙasar Nijar ya ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji

Shugaban Ƙasar Nijar ya ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Nijer Mohamed Bazoum da ministocin makamashi, da tsaron ƙasa, da harkokin cikin gida da sauran wasu ministocin ƙasar, sun ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji tare da jakadan Sin dake ƙasar, Jiang Feng. A yayin ziyarar ta safiyar jiya, shugaba Bazoum ya bayyana cewa, ƙasar Nijer ta gamsu da aikin gina madatsar ruwan, yana mai cewa kamfanin Sin mai aikin ginin ya shahara a duniya. A cewarsa, kamfanin na Sin ya tura ƙwararru zuwa wurin don sa kaimi da kyautata tsarin gudanar da aikin. Za a kammala gina madatsar ruwan ne a karshen shekarar…
Read More
Ya kamata Amurka ta soke takunkumi idan tana son taimakawa Afirka

Ya kamata Amurka ta soke takunkumi idan tana son taimakawa Afirka

Daga CMG HAUSA Ranar 25 ga wata, rana ce ta yaƙi da takunkumi, wadda ƙungiyar SADC ta ayyana. Wasu ƙasashen Afirka sun sake yin kira ga Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya da su soke takunkumin da suke ƙaƙaba wa ƙasar Zimbabwe. Amurka ta ɗauki sama da shekaru 20 da sanyawa Zimbabwe takunkumi ya zuwa yanzu. Alkaluman ƙididdiga sun nuna cewa, Zimbabwe ta yi asarar dalar Amurka fiye da biliyan 40 sakamakon takunkumin da aka sanya mata baki ɗaya. Hakika dai yadda Amurka ta ƙaƙaba wa Zimbabwe takunkumi, ta nuna yadda ta daɗe tana tsoma baki cikin harkokin cikin gida…
Read More
Mai da jama’a a gaban komai ita ce ƙa’idar gwamnatin ƙasar Sin

Mai da jama’a a gaban komai ita ce ƙa’idar gwamnatin ƙasar Sin

Daga MINA Abokai, yau na zana wani layin dogo da ake kira “Layin dogo na Qinghai-Tibet” wanda ya hada birnin Xining na lardin Qinghai da birnin Lhasa na yankin Tibet. An shimfida layin ne a tudun dake da matsakaicin tsayi mita 4000 daga leburin teku, hakan ya sa ya zama layin dogo mafi tsayi a duniya. Tudun Qinghai-Tibet na da nisa matuka da teku, saboda matuƙar tsayi, aikin shimfida layin dogo ko hanya a wurin, na fuskantar matuƙar wahala. Ya zuwa shekarar 1949, hanyar mota mai tsawon kimanin mita 1000 ne kawai yankin ke da su, baya ga kuma kwale-kwale…
Read More
CBN zai sauya tsarin wasu takardun kuɗin Nijeriya

CBN zai sauya tsarin wasu takardun kuɗin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, nan ba da daɗewa ba zai sake tsarin wasu takardun kuɗin Nijeriya. Bankin ya ce takardun da sake tsarin zai shafa sun haɗa da N200 da N500 da kuma N1,000. Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai ran Laraba a Abuja. Emefiele ya ce, ya zuwa 15 ga Disamban wannan shekarar za a fara amfani da takardun kuɗin da aka sake wa tsarin. A cewar Emefiele, Gwamnatin Tarayya ce ta buƙaci CBN da ya duba ya sake tsarin takardun kuɗin da lamarin ya shafa.
Read More
Kotu ta umarci Nijeriya ta biya Kanu diyyar miliyan N500

Kotu ta umarci Nijeriya ta biya Kanu diyyar miliyan N500

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Umuahia, babban birnin jihar Abia, ta umarci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ta maida shi Kenya inda ta kamo shi a ranar 19 ga Yunin 2021. Haka nan, kotun ta kuma buƙaci gwamnatin ta biya Kanu kuɗi miliyan N500 a matsayin diyyar kamo shi daga Kenya da ta yi ba bisa ƙa'ida ba. Alƙalin kotun, Mai Shari'a E.N Anyadike, ya jaddada cewa kama Kanu ba bisa ƙa'ida ba da gwamnatin ta yi take haƙƙinsa na 'yanci ɗan Adam ne. Ya ce, gwamnatin ta kasa kare kanta…
Read More
A nisanta yara, almajirai daga hotunan batsa

A nisanta yara, almajirai daga hotunan batsa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na san wannan take na yau zai tayar da hankalin wasun mu da dama, musamman malamai, alarammomi da ɗaliban ilimi, da ma uwa uba iyaye. Ba na zaɓi in yi wannan faɗakarwa kan almajirai ne kaɗai ba, har ma da sauran yaran mu da ke rayuwa a gaban iyayensu. Na san ba ni kaɗai ne wannan al'amari ke damuna ba, lura da yadda ake cigaba da samun taɓarɓarewar tarbiyyar yara ƙanana da ke samun kansu a cikin wata irin gurɓatacciyar rayuwa marar tsafta, saboda rashin kulawar iyaye, sa ido daga manya masu kula da tarbiyya, har…
Read More
Tunasarwa ga ‘yan Arewacin Nijeriya: Takenmu shi ne aiki da Ibada

Tunasarwa ga ‘yan Arewacin Nijeriya: Takenmu shi ne aiki da Ibada

Daga YUSUF MUHAMMAD DOSARA Abinda tambarin Arewa (Arewa logo) yake nufi shi ne; haɗin kai daka ɓangarori mabanbanta. Yankin Arewacin Najeriya yanki ne mai cin gashin kansa a cikin Najeriya, wanda ya sha bamban da yankin kudancin Najeriya. Arewacin Nijeriya na da al’adu masu zaman kansu, sannan suna hulɗa da ƙasashen waje da kuma tsarin tsaro mai kyau. Yankin Arewacin Nijeriya nada kimanin girman da ya kai 660,000 km2 (250,000 sq mi). Tun a shekaraun 1990s yankin Arewacin Nijeriya na da kimanin adadin mutanen da suka kai miliyan tara (9,000,000). Manyan yarurrukan dake cikin Arewacin Najeriya dai sun hada; Fulani,…
Read More
Game da taron jin ta bakin ‘yan takarar Shugabancin Nijeriya guda uku

Game da taron jin ta bakin ‘yan takarar Shugabancin Nijeriya guda uku

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA Ranar Litinin 17 ga watan Oktoba 2022, aka yi zama na biyu a Arewa House da wasu mutum shida daga cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar zaɓe ta 2023. An gayyaci Atiku Abubakar na PDP da Kola Abiola na PRP da Adewale na SDP a ranar Asabar. Dukkansu sun je kuma sun yi bayanin yadda za su tunkari matsalolin Arewa idan Allah ya ba su ragamar ƙasar nan. A ranar an ware wa ɗan takarar shugabancin Nijeriya a jam'iyyar APC wato Alhaji Bola Ahmed Adekunle Tinubu da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP su…
Read More
Maza masu duka da wulaƙanta matansu sam ba su da laifi!

Maza masu duka da wulaƙanta matansu sam ba su da laifi!

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu mai albarka, Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Da farko dai shi duka a zaman aure da maza suke yi wa mata abu ne a al'adance da addinance ma bai kamata ba, kuma abu ne da yake ci wa mata tuwo a ƙwarya. Duk da dai shi duka a gidan aure ba Hausawa suka fi yinsa ba. Wasu ƙabilun na Nijeriya sun fi yinsa. Sai dai shi ma Bahaushe yana nema ya ara ya yafa. Abin tambaya, me yake jawo duka a zaman aure?…
Read More
Sabuwar Ƙasar Sin ta ba ‘yan uwanta na nahiyar Afirka alfahari

Sabuwar Ƙasar Sin ta ba ‘yan uwanta na nahiyar Afirka alfahari

Daga BELLO WANG Wasu shekaru 51 da suka wuce, wato a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, aka zartas da wani ƙuduri a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), inda aka maido da kujerar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin (sabuwar ƙasar Sin) a majalisar. Wani bidiyon da aka ɗauka a lokacin ya nuna yadda wasu jami’an ƙasashen Afirka da suka halarci taron MƊD suka yi matukar murnar ganin yadda sabuwar ƙasar Sin ta samu wannan nasara. Tsohon shugaban ƙasar Sin Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ‘yan uwa na nahiyar Afirka sun ɗauki sabuwar ƙasar Sin, sun kai ta cikin…
Read More