Editor

9513 Posts
An caccaki Ƙatar kan cin zarafin baƙi gabanin gasar Kofin Duniya

An caccaki Ƙatar kan cin zarafin baƙi gabanin gasar Kofin Duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ƙasashe da babbar tawagar ƙwallon ƙafar Australiya sun caccaki jerin cin zarafin bil adama a Ƙatar, gabanin Gasar Kofin duniya da ke tafe a watan Nuwamban wannan shekarar, lamarin da ya sa Australiya kasance tawaga ta farko da ke cikin wannan gasa da ta caccaki ƙasar da ke karɓar baƙuncin gasar. Gasar Kofin Duniya da za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba ta fuskanci cece-kuce tun daga lokacin da aka bai wa Ƙatar damar karɓar baƙuncin shekaru 12 da suka wuce. Hukumar ƙwallon ƙafar Australia ta ce ta san cewa an yi sauye-sauye…
Read More
2023: Za mu haɗa kai da INEC don daƙile sayen ƙuri’u – EFCC

2023: Za mu haɗa kai da INEC don daƙile sayen ƙuri’u – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Nijeriya (EFCC), ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, domin daƙile ta'adar sayen ƙuri’u, musamman a lokacin babban zaɓen 2023. Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Abuja jiya Alhamis, jim kaɗan bayan kare kasafin kuɗin hukumar na 2023 a gaban kwamitin majalisar dattawa kan yaƙi da cin hanci da rashawa. "Za mu ci gaba da yin abin da ya kamata mu yi, muna ƙoƙarin tabbatar…
Read More
Sauya takardun Naira: Zainab ta ce babu ruwanta, ta gargaɗi CBN kan abin da ka iya biyowa baya

Sauya takardun Naira: Zainab ta ce babu ruwanta, ta gargaɗi CBN kan abin da ka iya biyowa baya

Daga BASHIR ISAH Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmad, ta nesanta kanta da matakin da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya shirya ɗauka na sauya tsarin wasu takardun Naira. Haka nan, Ministar ta gargaɗi CBN da ya shirya tunkarar matsalolin da ka iya biyowa baya mudin ya aiwatar da sauya tsarin kuɗin. Zainab ta yi waɗannan kalaman ne a lokacin da take yi wa Kwamitin Majalisar Dattawa kan sha'anin kuɗi jawabi kwanan nan a Abuja. Yayin ganawarsu da Ministar, Sanata Opeyemi Bamidele mai wakiltar Ekiti ta Tsakakiya a Majalisar, ya ce kwanaki biyu kacal da bayyana ƙudirin sauya wasu takardun…
Read More
Xi ya jaddada buƙatar inganta farfaɗo da yankunan karkara

Xi ya jaddada buƙatar inganta farfaɗo da yankunan karkara

Daga CMG Hausa Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping, ya jaddada buƙatar inganta farfaɗo da yankunan karkara ta kowacce fuska, da ƙoƙari tukuru domin cimma zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin ƙolin JKS, kuma shugaban rundunar sojin ƙasar, ya bayyana haka ne yayin da yake rangadi a birnin Yan’an dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin ƙasar Sin da birnin Anyang dake lardin Henan, na tsakiyar ƙasar, daga ranar Laraba zuwa yau Juma’a. Mai fassara: Fa’iza
Read More
Ya kamata ɓangarori daban-daban su yi ƙoƙari tare don kiyaye muhallin duniya

Ya kamata ɓangarori daban-daban su yi ƙoƙari tare don kiyaye muhallin duniya

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kiyaye muhallin duniya, alhakin ne na ƙasa da ƙasa, kuma ana buƙatar su yi ƙoƙari tare, don tinkarar ƙalubalen yanayin duniya baki ɗaya. Ya ce ya kamata ƙasashen da suka ci gaba, su sauke nauyin dake wuyansu na rage fitar da abubuwa masu gurɓata muhalli da cika alƙawarinsu yadda ya kamata, da samar da kuɗi da fasahohi ga kasashe masu tasowa a wannan fanni. Kana ƙasar Sin za ta ci gaba da haɗa gwiwa da ƙasashe…
Read More
Ƙasar Sin kyakkyawa za ta ƙara damar da gudummawarta ga duniya

Ƙasar Sin kyakkyawa za ta ƙara damar da gudummawarta ga duniya

Daga LUBABATU LEI Ƙarancin makamashi matsala ce da galibin ƙasashen Afirka ke fuskanta, a yayin da kuma nahiyar Afirka ta kasance ɗaya daga cikin sassan duniya da suke ƙarancin ƙarfin tinkarar sauyin yanayi, don haka, ya zama dole ƙasashen Afirka su bunkasa makamashi mai tsabta a wani ƙoƙari na tabbatar da dauwamammen ci gabansu. A watan Afrilun bana, rukunin na’urori na farko ya fara samar da wutar lantarki a madatsar ruwa ta Zungeru da ke kogin Kaduna na Jihar Neja ta Ƙasar Nijeriya, tasha ce da kamfanin ƙasar Sin ya gina, wadda ake sa ran za ta iya samar da…
Read More
Harƙallar ɗaukar ma’aikata 774,000: Sanatoci sun buƙaci sunaye da lambobin wayar waɗanda aka ɗauka

Harƙallar ɗaukar ma’aikata 774,000: Sanatoci sun buƙaci sunaye da lambobin wayar waɗanda aka ɗauka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin Tantance Bin Ƙa’idar Aikin Gwamnati na Majalisar Dattawa na neman titsiye Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo dangane da ma’aikatan aikin leburanci 774,000 da aka ce an ɗauka aikin ƙarfi na wucin gadi cikin 2020. A cikin 2020 ne Gwamnatin Shugaba Buhari ta fito da Shirin Musamman na Aikin Leburanci, wanda aka ɗauki matasa 1000 daga kowace ƙaramar hukuma ta ƙasar nan su 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja. An tsara cewa za su yi aikin leburanci ne iri daban-daban, har na tsawon watanni uku, inda za a riƙa biyan su Naira 20,000…
Read More
2023: Idan APC ta yi nasara za a sha wahala da farko, a ƙarshe a ji daɗi – Fani Kayode

2023: Idan APC ta yi nasara za a sha wahala da farko, a ƙarshe a ji daɗi – Fani Kayode

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daraktan Kamfen ɗin Tinubu 2023, Femi Fani-Kayode, ya yi sharhi dangane da abin da ya ke nufi da cewa idan APC ta sake yin nasara a zaɓen 2023, to ‘yan Nijeriya za su ji jiki. Ya bayyana cewa jin jikin na wani lokaci ne, amma ba mai ɗorewa ba ne, daga baya tattalin arzikin ƙasa zai gyaru, ‘yan Nijeriya su samu sauƙin rayuwa. Da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels TV, Fani-Kayode ya ce sai an sha wahala kafin tattalin arzikin ƙasa ya gyaru. Yana magana ne dangane da abubuwan da…
Read More
Nan da mako guda ƙarancin fetur zai wuce, cewar IPMAN da NARTO

Nan da mako guda ƙarancin fetur zai wuce, cewar IPMAN da NARTO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya da suka haɗa da ‘yan kasuwa, direbobin fasinjoji, masu ababen hawa, masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i ke ci gaba da kokawa a game da matsalar ƙarancin mai da dogayen layi da suke fuskanta idan suka je neman mai don su gudanar da al’amurran su na yau da kullum, ƙungiyar mamallakin motocin mai ta NARTO da takwararta ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu wato IPMAN sun tabbatarwa ‘yan ƙasar cewa, nan da mako guda za a kawo ƙarshen wahałar mai da ake gani a manyan biranın Nijeriya. Tuni…
Read More
FA ta ci tarar kocin Liverpool Yuro 30,000

FA ta ci tarar kocin Liverpool Yuro 30,000

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar FA ta ci tarar kocin Liverpool, Jurgen Klopp Yuro 30,00 bayan jan katin a wasan da ƙungiyarsa ta yi nasara a kan Manchester City a ranar 16 ga watan Oktoba. An kori Klopp daga filin wasa bayan rashin ɗa'ar da ya yi wa mataimakin alƙalin wasa, lokacin da aka ƙi bai wa Mohamed Salah damar dukan da aka yi masa. Kocin ya nemi afuwa kan halayyar da ya nuna bayan an tashi daga wasa. "Wani abu ne ya ɗauki hankali ne, ba alfahari na ke ba. Na cancanci jan kati," a cewarsa. An tuhumi Klopp…
Read More