Editor

9513 Posts
Dauda Kahutu Rarara cin mutuncin ya isa haka ko kuwa?

Dauda Kahutu Rarara cin mutuncin ya isa haka ko kuwa?

A wani lokaci ɗan na yi rubutu rangaɗeɗe a kan mawaƙin zamani Dauda Kahutu Rarara ɗan mutanen Katsina bisa ga niyya kyakkyawa. Ban sanshi ba, ban taɓa ganinsa ba, illa kawai ƙauna ta mutum da mutum. Dauda Kahutu Rarara bakatsine ne, kuma wataƙil mazaunin Kano wanda ga almajiranci Allah Ya hore masa hikimar waƙa! Ban san ta yadda wannan fasaha ta samu ba, wanda cikin ƙanƙanin lokaci Dauda Kahutu Rarara wai har kyautar mota yakeyi da miliyoyin Naira! Dauda Kahutu Rarara ance yana kusa-kusa da Villa har ma wai ya kusanci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a kasancewarsa mawaƙin Shugaba Buhari…
Read More
Dakatar da yajin aikin ASUU

Dakatar da yajin aikin ASUU

A kwanakin baya ne Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni 8 tana yi, wanda ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022. ASUU ta bayyana cewa ta janye yajin aikin ne biyo bayan shiga tsakani da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran ’yan Nijeriya masu kishi ƙasa suka yi da kuma umarnin kotun ɗaukaka ƙara na neman mambobinta da su koma bakin aiki. Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da hukuncin da ƙaramar kotun ta bayar tare da umurtar ƙungiyar ASUU da ta bi hukuncin da ƙaramar kotun…
Read More
Aikin gona da kayayyakin tarihi na jawo kankalin Shugaban Ƙasar Sin sosai

Aikin gona da kayayyakin tarihi na jawo kankalin Shugaban Ƙasar Sin sosai

Daga CMG HAUSA A Alhamis ta makon jiya, yayin da aka shiga lokacin girbin tuffa a ƙauyen Nangou na birnin Yan’an dake lardin Shaanxi na Arewa maso yammacin Sin, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yawata a cikin gonar tuffa domin fahimtar yadda aikin girbi na bana ke gudana. Yayin rangadin, Shugaba Xi ya gano yadda fasahar ban ruwa da na tantance ’ya’yan itatuwa a ƙauyen Nangou ke ci gaba da samun tagomashi, inda ya yaba da yadda aka raya sana’ar shuka tuffa, wadda ta kasance a sahun gaba, kuma mai kyakkyawar makoma. Har ila yau, Xi ya jaddada cewa,…
Read More
Wang Yi ya gana da jakadan Amurka da ke Ƙasar Sin

Wang Yi ya gana da jakadan Amurka da ke Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA Ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi ya gana da jakadan ƙasar Amurka da ke ƙasar Sin, Nicholas Burns, a jiya Jumma’a. Wang Yi, ya yi maraba da Nicholas Burns a matsayin sabon jakadan ƙasar Amurka a ƙasar Sin, kana ya bayyana cewa, yanzu an shiga lokaci mai muhimmanci na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Kuma ƙasa da ƙasa suna fatan ganin an raya dangantakar ta su yadda ya kamata. Ya kara da cewa, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Amurka su girmama juna, da yin zama…
Read More
Ƙawancen Sin da Afrika na da muhimmanci ga cimma ajandun nahiyar da na duniya

Ƙawancen Sin da Afrika na da muhimmanci ga cimma ajandun nahiyar da na duniya

Daga CMG HAUSA Masana sun bayyana muhimmiyar dangantakar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afrika, a matsayin mai matuƙar muhimmancin da za ta taimakawa nahiyar aiwatar da ajandunta da ma na duniya, ta hanyar ba matasanta horon fasahohi. Masanan sun bayyana haka ne yayin wani taro mai taken “Makomar haɗin gwiwar Sin da Afrika: taron shugabannin matasa”, wanda ya gudana a ranar Alhamis a Addis Ababa, babban birnin Habasha. Da take jawabi, ministar kula da harkokin mata da walwalar al’ummar ta Habasha, Ergogie Tesfaye, ta ce taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC da aka ƙaddamar a…
Read More
NNPC zai fara gyaran matatar mai ta Kaduna

NNPC zai fara gyaran matatar mai ta Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA Gwamnatin Nijeriya ta amince ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Koriya ta Kudu da zimmar gyara matatar man fetur ta Kaduna da ke Arewacin ƙasar. Shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPC, Mele Kyari, shi ne ya saka hannu a madadin Nijeriya yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar ƙasar ke halarta a Koriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari. Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Tiwita ta ce nan gaba kaɗan za a fara zagayen duba gyaran da za a yi. A ƙarshen shekarar 2021 ne gwamnatin Nijeriya ta ware fiye da Dala biliyan…
Read More
Ba Janar Ishaya ne daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku a Kebbi ba – PDP

Ba Janar Ishaya ne daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku a Kebbi ba – PDP

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kebbi ta musanta naɗa Janar Ishaya Bamaiyi (murabus) a matsayin daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar. Kamar yadda shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Usman Suru ya bayyana wa manema labarai a lokacin da yake zantawa a ranar Larabar da ta gabata a garin Birnin Kebbi, yayin da yake mayar da martani kan wani rahoto da aka samu ta yanar gizo da ya ayyana Janar Ishaya a matsayin daraktan yaƙin neman zaɓen ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa. Ya bayyana cewa an jawo hankalin 'ya'yan…
Read More
Ƙungiyar ‘yan jarida a Yobe ta raba gari da gwamnatin jihar

Ƙungiyar ‘yan jarida a Yobe ta raba gari da gwamnatin jihar

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Ƙungiyar 'yan jarida (Yobe Correspondents' Chapel) a jihar Yobe, ta bayyana ɗaukar matakin raba gari da Gwamnatin Jihar Yobe ta hanyar ƙaurace wa ɗaukar dukkan labaran aikace-aikacen gwamnatin jihar. Ƙungiyar, a sanarwar bayan taron gaggawa wanda ta gudanar a ranar Jumma’a, 28 ga watan Oktoba, 2022 mai ɗauke da sa hannun Shugabanta da Sakatare; Ahmad I. Abba da Micheal Oshomah, sun bayyana ɗaukar matakin sakamakon cin zarafin da jami'an tsaron Gidan Gwamnati ke yi wa mambobinta. Ƙungiyar ta ce ɗaukar matakin ya zo ne sakamakon tursasawa tare da cin zarafin da jami’an tsaron Gidan Gwamnati ke…
Read More
Matatar man Ɗangote za ta fara samar da fetur ga Ƙasar Ghana

Matatar man Ɗangote za ta fara samar da fetur ga Ƙasar Ghana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ghana na jiran tsammanin fara aikin matatar man Dangote da za ta ragewa ƙasar matsalar wahalar makamashi. Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur a Ƙasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid, ne ya bayyana hakan a kwanan nan. A cewarsa, ƙasar Ghana za ta rage shigo da kayayyakin mai daga kasashen Turai da sauran ƙasashen ƙetare. Shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje na samar da nakasu da illa ga fannin makamashi a ƙasar Ghana saboda yadda ake tafiyar da harkokin mai a ƙasar.  Ƙasar Ghana dai ta kasance daga jerin ƙasashen dake shigo da ɗanyen…
Read More
Gwamna Wike ya bada tallafin biliyan N2.1 ga jihohi huɗu yayin da jiharsa ke cikin ƙunci

Gwamna Wike ya bada tallafin biliyan N2.1 ga jihohi huɗu yayin da jiharsa ke cikin ƙunci

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ba da tallafi aƙalla Naira biliyan 2.1 ga jihohi Nijeriya guda 4 a cikin watanni 15 kacal.  Rahotannin sun bayyana cewa, Gwamnan ya raba tallafi ne a tsakanin watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Oktoban 2022. A watan Janairun shekarar 2021 ne dai Wike ya ba da gudunmowar Naira miliyan ga takwaransa na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, don sabunta ginin Babbar kasuwar Sokoto wacce ibtilain gobara ya sabauta.  A cikin watan Mayun dai shekarar dai ta 2021, gwamna Wike ya sake ba da gudunmowar wata Naira miliyan 600 a…
Read More