Editor

9513 Posts
CMG ya shirya tarukan yaɗa ruhin taron wakilan JKS karo na 20 a ƙasashen Afirka

CMG ya shirya tarukan yaɗa ruhin taron wakilan JKS karo na 20 a ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA Cibiyar dake tsara shirye-shirye da harsunan ƙasashen Asiya da Afirka ta babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG da karamin ofishin jakadancin ƙasar Sin dake yankin Zanzibar da hukumar watsa labarai na yankin, sun shirya taron yada ruhin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 mai taken “Sabon tafarki da makoma ta bai daya” a yankin Zanzibar na ƙasar Tanzaniya a ranar 26 ga wannan wata, agogon ƙasar. Yaron da ya samu halartar babban ƙaramin jakadan ƙasar Sin dake yankin Zhang Zhisheng, da babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai…
Read More
Ba ni na kashe Ummita ba, inji ɗan Chana a gaban kotu

Ba ni na kashe Ummita ba, inji ɗan Chana a gaban kotu

Daga AMINA YUSUF ALI Mutumin nan ɗan asalin ƙasar Chana mai suna Geng Quangrong ya musanta zargin kashe budurwarsa mai suna Ummita da ake yi masa a gaban Babbar Kotun Kano.  An gurfanar da Geng Quarong a gaban wata kotu wacce take zamanta a kan titin Miller Road dake jihar Kano. Inda Geng wanda aka kama dumu-dumu yana yi wa budurwarsa Ummukulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita, yankan rago ya ƙeƙasa ƙasa ya ƙi amsar laifinsa.  A ranar 27 ga watan Oktoba, 2022 ne yayin zaman kotu ne dai Alƙalin kotun mai suna, Mai Shari'a Sunusi Ado…
Read More
Kyakkyawar zamantakewa kaɗai za ta kawo zaman lafiya

Kyakkyawar zamantakewa kaɗai za ta kawo zaman lafiya

A wannan mako ina son hankalin mu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautatawa juna a mu'amala ta yau da kullum ke iya haifar da fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama'a, musammam mutane masu bambancin ƙabila, addini ko ra'ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya haɗa jama'a, daga ɓangarori daban-daban. Babu shakka zaman lafiya da jama'a, tausayawa, tallafawa, da kauce wa duk wani abu da zai iya kawo saɓani da rashin fahimta a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuqa, babu ma kamar wannan lokaci da jama'a ke cikin ƙunci da…
Read More
Xi Ya jaddada sake farfaɗo sa yankunan karkara yayin da ya ziyarci Shaanxi da Henan

Xi Ya jaddada sake farfaɗo sa yankunan karkara yayin da ya ziyarci Shaanxi da Henan

Daga CMG HAUSA A yayin ziyararsa da farko tun bayan kammala babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin (JKS) na 20, Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping, ya jaddada buƙatar ƙara ƙaimi ga aikin farfaɗo da yankunan ƙasar baki ɗaya, da ƙara azama wajen ganin an cimma burin zamanantar da aikin gona da na yankunan karkara da aka sanya a gaba. Ya bayyana a yayin da ya ziyarci Yan’an dake lardin Shaanxi dake Arewa maso Yammacin ƙasar da birnin Anyang dake yankin tsakiyar ƙasar daga ranar Laraba zuwa Jumma’a cewa, ya zama tilas a ba da muhimmanci wajen raya yankunan…
Read More
Mutane na cigaba da hada-hada a Abuja duk da barazanar kai hari

Mutane na cigaba da hada-hada a Abuja duk da barazanar kai hari

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Duk wanda ya fito a farkon makon nan a cikin babban birnin Nijeriya, Abuja zai ga mutane su na hada-hadarsu tamkar ba wata barazanar yiwuwar kawo hare-haren ’yan ta’adda. Haƙiƙa sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke nuna akwai barazanar kawo harin ta’addanci musamman a Abuja ya zama abun zantawa da yaɗawa a kafafen labaru amma a gefe guda kai tsaye hakan bai sauya yadda talakawa ke shiga kasuwanni ko gidajen da sauran su don harkokin yau da kullum ba. Ai wasu ma dama sun dawo Abuja ne don garuruwansu sun yi zafi a na ta…
Read More
2023: Na yafe wa Osinbajo, inji Tinubu

2023: Na yafe wa Osinbajo, inji Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar kujerar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ba shi da sauran damuwa a ransa game da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, yana mai cewa, ya yafe masa bisa takara da ya yi da shi a lokacin zaven fitar da gwani na jam’iyyar. Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana haka ne ranar Litinin lokacin da yake jawabi ga wata ƙungiyar da ta yi wa Osinbajo hidimar takarar shugaban ƙasa a Kano jawabi. A cigaba da fafatawa a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, an…
Read More
Tsaro: A kiyayi jihohi 10 a Arewa – Ingila

Tsaro: A kiyayi jihohi 10 a Arewa – Ingila

*Jihohi huɗu a Kudu da iyakar Nijar na da hatsarin gaske*Ba haka ba ne, inji Gwamnatin Tarayya*Jami’an Amurka sun kai samame rukunin gidaje a Abuja*An kulle katafaren ginin ‘Jabi Mall’ a Abuja Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daga dukkan alamu husuma da jayayya sun ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ofisoshin jakadancin Amurka da Ingila bisa zargin yiwuwar barazanar tsaro a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, da wasu jihohin ƙasar, inda yayin da ofisoshin jakadancin ke iqirarin tabbatar da barazanar, ita kuwa Gwamnatin Tarayya ƙaryatawa ta ke yi. Alhamis da ta gabata Ofishin Hulɗa da Ƙasashen Waje, Ƙasashe Rainon…
Read More
Tsaro: A kiyayi jihohi 10 a Arewa – Ingila

Tsaro: A kiyayi jihohi 10 a Arewa – Ingila

*Jihohi huɗu a Kudu da iyakar Nijar na da hatsarin gaske*Ba haka ba ne, inji Gwamnatin Tarayya*Jami’an Amurka sun kai samame rukunin gidaje a Abuja*An kulle katafaren ginin ‘Jabi Mall’ a Abuja Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daga dukkan alamu husuma da jayayya sun ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da ofisoshin jakadancin Amurka da Ingila bisa zargin yiwuwar barazanar tsaro a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, da wasu jihohin ƙasar, inda yayin da ofisoshin jakadancin ke iqirarin tabbatar da barazanar, ita kuwa Gwamnatin Tarayya ƙaryatawa ta ke yi. A jiya Alhamis, Ofishin Hulɗa da Ƙasashen Waje, Ƙasashe Rainon Ingila…
Read More
Yadda matatar Fatakwal ta lamushe biliyan N39.4 a shekara ba tare da taɓuka komai ba

Yadda matatar Fatakwal ta lamushe biliyan N39.4 a shekara ba tare da taɓuka komai ba

Daga AMINA YUSUF ALI Duk da rashin tavuka komai a fannin tattalin arzikin ƙasa da matatar man fetur ɗin Nijeriya dake a garin Fatakwal take yi, a cikin watanni 12 kacal ta lamushe kuɗaɗen da yawansu ya kai Naira biliyan 39.4. Wannan matatar dai an ruwaito ta lamushe Naira 39,491,468,000 a cikin shekarar 2021 duk kuwa da ta kwashe shekaru ba tare da tace ko da ɗigon man fetur guda ba. Waɗannan bayanan sun zo ne daga rahotannin bayanan kuɗin na Kamfanin Samar da Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) wanda hukumar PHRC ta gudanar a kan harkar mai na shekarar…
Read More
Jerin kadarorin da gwamnatin Buhari za ta cefanar don yin ciko a kasafin kuɗin baɗi

Jerin kadarorin da gwamnatin Buhari za ta cefanar don yin ciko a kasafin kuɗin baɗi

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ta fidda wani jerin sunayen kadarorin gwamnati guda 25 da za ta sayar don yin cikon giɓin Naira tiriliyan 10.7 a kasafin kuɗin Nijeriya na shekarar 2013. Daga cikin waɗannan kadarorin 25, wasu an sayar da su ne, yayin da wasu kuma aka rarraba hannun jarinsu aka sayar domin dai a samu a yi ciko a wannan kasafin kuɗin da yake neman kasawa. Idan ba a manta ba da ma, Buhari ya tava faɗa cewa, Naira tiriliyan 10.7 ɗin da ta kasa a cikin kasafin kuɗin shekara…
Read More