Editor

9513 Posts
Shirin ƙidaya: NPC ta ƙaddamar da shafin intanet don ɗaukar ma’aikata

Shirin ƙidaya: NPC ta ƙaddamar da shafin intanet don ɗaukar ma’aikata

Daga BASHIR ISAH Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), ta ƙaddamar da shafinta na intanet don ɗaukar ma'aikatan wucin-gadin da za su taya ta aikin shirin ƙidaya mai zuwa. Shugaban hukumar, Honarabul Nasir Isa-Kwarra ne ya jagoranci ƙaddamar da shafin a matsayin wani mataki na shirye-shiryen shirin ƙidaya 'yan ƙasa da hukumar za ta gudanar a Afrilun 2023. Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da shafin ranar Litinin a babban ofishin hukumar da ke Abuja, Isa-Kwarra ya ce ma'aikatan da za a yi amfani da su wajen gudanar da shirin, za a zaɓo su ne daga mazauninsu. Ya ce dabarar…
Read More
Ƙasar Sin za ta ƙara buɗe ƙofarta ga ƙasashen ƙetare

Ƙasar Sin za ta ƙara buɗe ƙofarta ga ƙasashen ƙetare

Daga CMG HAUSA A game da shakkun da ƙasashen ƙetare ke nunawa game da batun buɗe ƙofar ƙasar Sin ga kasashen waje, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Litinin din nan cewa, buɗe ƙofa ita ce babbar manufar ƙasar Sin. Rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, ya bayyana ƙarara game da inganta buɗe ƙofa ga ƙasashen ƙetare, inda ya nuna cewa, ya kamata a inganta matakin haɗin gwiwar cinikayya da zuba jari. Wannan ya ƙara nuna cikakken ƙudirin ƙasar Sin na…
Read More
Sin ta yi nasarar harba samfurin ɗakin gwajin tashar binciken sararin samaniya na Mengtian

Sin ta yi nasarar harba samfurin ɗakin gwajin tashar binciken sararin samaniya na Mengtian

Daga CMG HAUSA Da yammacin yau ne ƙasar Sin ta yi nasarar harba ɗakin gwaje-gwaje na biyu na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya, matakin dake ƙara kusanto ga aikin kammala tashar ya zuwa ƙarshen wannan shekara. Da misalin ƙarfe 3 da mintuna 37 agogon Beijing ne, aka harba samfurin ɗakin gwajin na Mengtian ta hanyar amfani da rokar Long March-5B daga cibiyar harba taurarin ɗan-Adam dake Wenchang na lardin Hainan dake kudancin ƙasar Sin. Mai fassarawa: Ibrahim
Read More
Xi Jinping ya aike da saƙon taya murnar cika shekaru 65 da kafuwar Ƙungiyar Ƙawancen Rasha da Sin

Xi Jinping ya aike da saƙon taya murnar cika shekaru 65 da kafuwar Ƙungiyar Ƙawancen Rasha da Sin

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike da wasiƙar taya murnar cika shekaru 65 da kafuwar ƙungiyar ƙawancen ƙasashen Rasha da Sin. Cikin wasiƙar ta ranar Asabar, shugaba Xi ya ce tun kafuwar ƙungiyar yau shekaru 65 da suka gabata, tana ta ƙara azama wajen kyautata cuɗanya da ɓangaren Sin. Ta kuma bayar da muhimmiyar gudummawa wajen inganta fahimtar juna, da abota, da amincewa juna tsakanin al’ummun ƙasashen biyu, da ma kara faɗaɗa ginshikin tattaunawa tsakanin al’ummunsu. Don haka ya yi fatan ƙungiyar za ta dore da wannan kyakkyawan aiki nata, na haɗa kan al’ummun Sin da…
Read More
Sake fasalin Naira zai sa masu garkuwa fara neman biyan fansa da Dala – Sheikh Gumi

Sake fasalin Naira zai sa masu garkuwa fara neman biyan fansa da Dala – Sheikh Gumi

Daga BASHIR ISAH Fitaccen malamin Islaman nan Ahmad Gumi, ya ce batun sake tsarin Naira zai sa 'yan fashin daji su fara neman a biya kuɗin fansa da Dalar Amurka kafin su sako waɗanda ke hannunsu. Haka nan ya ce, matakin tamkar karya tattalin arzikin ƙasa ne ga 'yan Nijeriya, musamman mazauna karkara. Don haka malamin ya ce ba ya tare da Babban Bankin Nijeriya (CBN) a kan wannan ƙudiri da ya sa gaba. Ya ƙara da cewa, kashi 80 na 'yan Nijeriya, musamman mautanen karkara, sun fi gane ma hada-hada da kuɗi a hannu. Cikin bayanin da ya fitar,…
Read More
Sojoji sun fatattaki mayaƙan ISWAP a Neja

Sojoji sun fatattaki mayaƙan ISWAP a Neja

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga Jihar Neja sun ce, sojoji sun fatattaki wasu 'yan ta'addar da ake zargin mayaƙan ISWAP ne a Jihar bayan yinƙurin da suka yi na neman kuɓutar da 'yan uwansu ya gamu da tasgaro. Bayanai daga jihar sun ce, 'yan ta'addar sun yi ƙoƙarin kutsawa inda ake tsare da wasu jagororinsu a yankin New Bussa don ƙwato su inda suka gamu da ajalinsu. Majiyarmu ta ce, da ma dai sojoji sun tsammaci zuwan 'yan ta'addar, wanda hakan ya sa suka yi musu kwanton-ɓauna. Majiyar ta ƙara da cewa, duk da dai lamarin ya faru ne cikin…
Read More
Yadda za a kawar da tabon fata (2)

Yadda za a kawar da tabon fata (2)

*Me ke kawo tabon fata Daga AISHA ASAS A baya mun fara shimfiɗa ne kan ma’ana ta tabon fata, dalilin samuwar shi da kuma mahaifar shi. Mun yi wannan bayyani ne don tafiya bisa ga fahimta ɗaya, wanda hakan zai sa mu fahimci inda muka dosa a yanzu. A wannan sati kamar yadda muka faɗa a sama, za mu yi bayyani kan ababen da ke zama silar samuwar tabon fuska, ma’ana matsalolin da ke samuwa kafin wannan sinadarin ya yi gudun kawo ceto ga fata wanda ke zama sanadiyyar barin tabo a wurin. Akwai matsalolin fata da dama da ke…
Read More
Dandalin shawara: Game da matsalar warin baki

Dandalin shawara: Game da matsalar warin baki

Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Aisha an yini lahiya. Allah Shi taimaka, Ya yi ma ki jagora. To ni ma dai da ‘yar neman shawara na taho kamar yadda aka saba yi. Wallahi miji a gare ni da yake warin jiki, babu ma kamar baki nai. Bai son yin wanka. In ya matso ni kamar in yi amai. Shi ya sa duk da Ina son auratayya wallahi har ban sha’awarta, don da ya matso sai warin ya sa abin ya fita ga raina. Kuma matsalar mijin nau na cikin irin hitinannun mazan nan ne da ba su amsar laihi idan an…
Read More
Da sanina CBN zai sauya tsarin Naira – Buhari

Da sanina CBN zai sauya tsarin Naira – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce da saninsa Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai canza tsarin wasu takardun Naira. Buhari ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da 'yan jarida Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai suka yi da shi a ranar Lahadi a Abuja. Da yake amsa tambayoyi, Buhari ya ce ya gamsu kuma yana da yaƙinin ƙasa za ta amfana da sauyin tsarin kuɗin da CBN ya ƙudiri aniyar aiwatarwa. Ya ce dalilan da CBN ya gabatar masa dangane da sauyin tsarin kuɗin, sun gamsar da shi cewa, lallai tattalin arzikin ƙasa zai amfana da…
Read More
Yau Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Yau Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Daga BASHIR ISAH Yau Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a Abuja don tattauna batutuwan da suka shafi tsaron ƙasa. Yayin ganawar, Shugaba Buhari zai karɓi bayanai daga jagororin tsaron kana ya yi tsokaci a ɓangarorin da ke buƙatar a bai wa muhimmanci. Tun farko, a wannan Litinin ɗin aka shirya a kan Buhari zai ƙaddamar da cibiyar kimiyya da fasaha ta NASENI amma sai aka ɗage sakamakon taron gaggawar da zai yi da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro. Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun Shugaban…
Read More