01
Nov
Daga CMG HAUSA Da misalin ƙarfe 3 da minti 37 na yammacin jiya Litinin 31 ga watan Oktoba, ƙasar Sin ta yi nasarar harba ɓangare na uku, na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya. Sa’an nan, bayan kimanin minti 8, ɗakin gwaje-gwaje na Mengtian ya rabu da rokar Long March-5B, ya kuma shiga hanyarsa kamar yadda aka tsara. Lamarin da ya nuna cewa, yawan ɗakunan gwaje-gwaje na tashar binciken sararin samaniya ta ƙasar Sin, sun ƙaru daga guda biyu zuwa guda uku, waɗanda za su kasance tamkar “siffar T”, matakin dake ƙara kusanto ga aikin…
