Editor

9513 Posts
Tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Super Eagles da Kano Pillars, Bello Musa ya rasu

Tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Super Eagles da Kano Pillars, Bello Musa ya rasu

Daga BASHIR ISAH Rahotanni sun ce Bello Musa Ƙofarmata ya rasu ne ranar Talata a mahaifarsa, Kano yana da shekara 34. Tuni aka yi jana'izar marigayin a Kano daidai da karantarwar Musulunci. Bayanai sun nuna Musa ya soma harkar ƙwallon ƙafa ne a 2007 a kulob ɗin Buffalo da ke Kano, daga bisani ya samu shiga ƙungiyar Kano Pillars. A 2010 ya sauya sheƙa zuwa ƙungiyar Heartland a Owerri sannan ya sake dawowa Kano Pillars a 2012, kana daga bisani ya tafi ƙungiyar Elkanemi Warriors a Maiduguri. Bayan wasu lokuta marigayin ya samu kwantiragi da kulob ɗin IK Start a…
Read More
Cibiyar “Africa CDC” za ta zamo muhimmiyar kyautar Sin ga nahiyar Afirka

Cibiyar “Africa CDC” za ta zamo muhimmiyar kyautar Sin ga nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA Tsohon jakadan ƙasar Habasha a MƊD Teruneh Zenna, ya ce cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko “Africa CDC”, wadda ƙasar Sin ke samar da tallafin ginawa, za ta kasance ƙarin kyautar Sin ga nahiyar Afirka. Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr. Zenna ya ce baya ga samar da kuɗaɗen aikin, ƙasar Sin din ce kuma ke aiwatar da ginin cibiyar, wadda za ta ƙunshi dukkanin kayayyakin aiki da ake buƙata, na inganta bincike da haɓaka harkar kiwon lafiya a Afirka. Zenna ya ƙara da cewa, ta amfani da helkwatar AU…
Read More
Kafin kammala karatunmu gwamnati ta ba mu aiki yana jiran mu – Maimuna Yakubu Muhammed

Kafin kammala karatunmu gwamnati ta ba mu aiki yana jiran mu – Maimuna Yakubu Muhammed

"'Yan mata a guje samari barkatai da miƙa wa waya ragamar rayuwarku" Daga: BABANGIDA S.GORA KANO. Hajiya Maimuna Yakubu Muhammed ita ce mace ta farko da ta far riƙe matakin darakta na tsawon shekaru 15 a Hukumar Kula da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki, wadda aka fi sani da NACA. Baya ga haka, ta samu ƙwarewa da kuma sanin makamar aiki ta sanadiyyar ziyarar kusan ƙasashe 28 da ta yi. Har wa yau, Hajiya Maimuna ta kasance shugabar ƙungiyar SWODEN, wato ƙungiyar nan da ta ke tallafa wa al'umma ta fuskoki da dama. A tattaunawar su da wakilin Manhaja a…
Read More
Matsalar tsaro: Hannu da yawa maganin ƙazamar miya

Matsalar tsaro: Hannu da yawa maganin ƙazamar miya

Ba da jimawa ba ne ofishin jakadancin ƙasar Amurka a Nijeriya ya fitar da wata sanarwa da ke shawartar 'yan ƙasar da ke nan Nijeriya da ma masu niyyar shigowa, su dakata ko kuma su yi hattara, sakamakon wasu rahotannin sirri da aka ce an samu na yiwuwar kai hari wasu muhimman wurare a ƙasar nan, musamman ma dai Babban Birnin Tarayya Abuja. A wasu rahotannin ma an ce ofishin jakadancin ƙasar Birtaniya a Nijeriya shi ma ya sake tabbatar da wannan rahoton. A yayin da hukumomin tsaro a Nijeriya ke ƙoƙarin gudanar da nasu binciken don tabbatar da ingancin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Jamiyyar PDP na Zamfara ya rasu

Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Jamiyyar PDP na Zamfara ya rasu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau, Allah Ya yi Shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Zamfara, Hon. Ahmad Sani Kaura rasuwa. Majiya ta kusa da iyalan marigayin ta tabbatar wa wakilinmu da rasuwar ta wayar tarho. Majiyar ta ce, marigayin ya mutu ne a ɗaya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya a jihar bayan doguwar jinya. Ƙarin bayani na nan tafe…
Read More
Saƙon da muke so mambobinmu na ƙungiyar TIGMEIN su fahimta

Saƙon da muke so mambobinmu na ƙungiyar TIGMEIN su fahimta

Daga MAHADI SHEIKH SUFWAN Babban jagoran ƙungiyar qara samun haɗin kan tijjanawa da tallafawa juna TIGMEIN na ƙasa, Sheikh Tijjani Sheikh Sani Auwal Inyas. Da shugaban kwamitin amitattu na ƙasa Dakta Ibrahim Umar Pandogari, da sauran majalisar shugabanni na ƙasa, Suna miƙa saƙo na musamman ga dukkan shugabannin TIGMEIN na jihohi da ƙananan hukumomi da mazaɓu kamar haka, ganin cewa gwamnatin Nijeriya ta bayar da izini ga jam'iyyun siyasa su fara gudanar da yaƙin neman zaɓe a ƙasa bakiɗaya, wannan kungiya tana umurtar dukkan shugabanni su kula da abubuwa kamar haka: Wayar da kan dukkan tijjanawa wajen kauce wa dukkan…
Read More
Ba Buhari ne kaɗai zai kashe ilmi ba, shi Atiku murus zai masa

Ba Buhari ne kaɗai zai kashe ilmi ba, shi Atiku murus zai masa

Daga IBRAHIM MUSA Ga dai wani sharhi daga likitan siyasa Dakta Ibrahim Musa. Asha karatu lafiya! Yanzu tunda ASUU ta dawo daga yajin aiki, ya kamata ta mayar da hankali wajen tattauna manufofin 'yan takara da yadda hakan zai yi tasiri ga ɗorewa ko rugujewar ƙungiyar. Za mu fara da Alareni Atiku Abubakar wanda ya bayyana manufarsa a kan makomar Jami'o'in gwamnatin tarayya. Shi dai Atiku ya ce zai miƙa ɗawainiya da ikon tafiyar da duk jamioi, kwlejin ilmi da makarantun ilmin fasaha ga gwamnonin kowacce jaha su ci gaba da kula da su. A tsarinsa, zai cire hannun gwamnatin…
Read More
Lokaci ya yi da za mu canza yadda muke tunkarar lamarin ‘yan bindiga

Lokaci ya yi da za mu canza yadda muke tunkarar lamarin ‘yan bindiga

Daga MUS'AB ISA MAFARA (phd) Na ga bidiyon 'yan matan Furfuri da aka sace, an ce sun yi watanni a hannun waɗannan 'yan ta'adda. Abun akwai ƙona rai. Allah Ya ba su mafita Ya sa kaffara. Na san idan mutum bai samu kansa a cikin wani hali ba ba zai taɓa sanin ya lamarinsa zai kasance ba. Amma ni kullum tunanina wai dole ne ka bi ɗan bindiga zuwa daji don kawai yana da bindiga kai ba ka da ita? Ƙarshen ta dai ya kashe ka in ba ka je ba, to ba gara mutuwa da halin da suke sa…
Read More
ATSSSANA ta dakatar da aiki a Filin Jirgin Saman Murtala saboda korar mabobinta daga aiki

ATSSSANA ta dakatar da aiki a Filin Jirgin Saman Murtala saboda korar mabobinta daga aiki

Daga BASHIR ISAH A ranar Talata ma'aikatan Babban Filin Jirgin Saman Murtala Mohammed da ke Legas suka yi zanga-zanga tare da rufe ƙofar shiga filindomin nuna rashin jin daɗinsu dangane da korar wasu jagororinsu da aka yi daga aiki. Wannan al'amari ya jefa matafiya da suka kasance a filin jirgin a wannan lokaci cikin mawuyacin hali kasancewar masu zanga-zangar sun dakatar da komai a filin jirgin. Jiragen da suka kasa samun sararin tashi a wannan lokaci sun haɗa da Ibom Air da Air Peace. Sanarwar da ƙungiyar ma'aikatan (ATSSSAN) ta fitar, ta nuna kora daga aikin ta shafi wasu jagororin…
Read More
Ci gaban ƙasar Sin nasara ce ta duniya ba ƙalubale ba

Ci gaban ƙasar Sin nasara ce ta duniya ba ƙalubale ba

Daga FA'IZA MUSTAPHA Lamuran da suka faru a duniya, sun nuna mana cewa, nasara da ci gaban duniya, sun dogara ne da haɗin gwiwa da taimakekeniya da kuma moriyar juna tsakanin ƙasa da ƙasa. Don haka, ƙyashi ko adawa da ci gaban wata ƙasa, ba zai taba amfanawa duniya ba. Yadda ƙasashen yammacin duniya ke alaƙanta ƙasar Sin da kalmar “barazana” ko “ƙalubale”, abun damuwa ne ga zaman lafiya da ci gaban duniya. Nasarar Sin, nasara ce ga ɗaukacin duniya, bisa la’akari da yadda karuwar tattalin arzikinta ko nasarori ko fasahohi ko ci gabanta ke shafar duniya baki ɗaya. Yayin…
Read More