Editor

9513 Posts
Hikayata 2022: Amira Souley ta zama gwarzuwar BBC Hausa ta bana

Hikayata 2022: Amira Souley ta zama gwarzuwar BBC Hausa ta bana

Daga AISHA ASAS Masu iya magana na cewa, rana ba ta ƙarya, kuma duk nisan dare gari zai waye. Kamar yadda aka shelanta ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba, 2022, a matsayin ranar da za a bayyana gwarazan fitacciyar gasar rubutu ta mata zalla da BBC Hausa ke shiryawa a kowacce shekara mai taken Hikayata. Cikin ikon Allah taron ya fara da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar a ɗakin taro na 'Yar Adua Centre da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.  An gabatar da gwarazan gasa da kuma matsayin kowacce daga cikin su, wato daga ta ɗaya har zuwa ta…
Read More
Gwamnatin Bauchi ta ƙarfafa tattalin arzikin jama’ar jihar da kimanin Naira biliyan biyu kyauta

Gwamnatin Bauchi ta ƙarfafa tattalin arzikin jama’ar jihar da kimanin Naira biliyan biyu kyauta

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Alhaji Hamza Koshe Akuyam ya bayyana cewar, shirin ƙarfafa tattalin arzikin jama’a na gwamnatin jiha wato Ƙaura Economic Empowerment Programme (KEEP) ya rarraba kayayyakin sana’o’i da kuɗaɗe kimanin jimlar na biliyan biyu kyauta wa marasa ƙarfi da suka haɗa da ‘ya’yan jam’iyya da ke kan karagar mulki. Da yake yin jawabi a taron kammala rufe bayar da tallafin ƙarfafawan a ƙaramar hukumar Bauchi wacce ta kasance ta ashirin kuma ta ƙarshe a farfajiyar filin wasan ƙwallo na tunawa da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa (ATBS) dake garin Bauchi a kwanakin…
Read More
NDLEA ta rufe asusan bankin wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi cike da biliyoyin Naira

NDLEA ta rufe asusan bankin wani ƙasurgumin mai fataucin miyagun ƙwayoyi cike da biliyoyin Naira

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar Yaƙi da Fatauci, Sha da Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta bayyana ritsa maƙudan kuɗaɗe kimanin Naira biliyan ashirin a cikin asusan banki guda 103 na wani ƙasungumin mai fatauci da miyagun ƙwayoyi da ta cafke a kwanakin baya a birnin Legas. Ana yi wa wanda aka yi wa zargi da aikata laifin, Mallinson Ukatu, laƙabin ɗan kasuwar Legas ma’abucin yakana. Hukumar ta kuma shigar da tuhumce-tuhumce guda 23 akan wanda ake zargi da aikata laifukan, haɗi da kamfanonin sa guda shida masu suna ‘Fruitroprics Industries Limited, Mallinson and Partners Limited, NISPO Porcelain Company Limited, MBL…
Read More
An fara rangadin nuna kashi na uku na fina-finan Ƙasar Sin a Afirka

An fara rangadin nuna kashi na uku na fina-finan Ƙasar Sin a Afirka

Daga CMG HAUSA Tun daga watan Nuwamba ne, kafofin watsa labaran Afirka guda 14 suka fara nuna wasu kayatattun fina-finan ƙasar Sin guda 17 da aka fassara cikin harsunan Turanci da Faransanci da Swahili da Hausa da harshen Larabci. Inda masu kallo daga ƙasashen na Afirka za su kalli fina-finan cikin harsunansu na gida a cikin ƙasashensu. Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin ne wato CMG, ya aika kunsin kyautar waɗannan fina-finai, inda za a watsa su a kafafen watsa labarai 14 na ƙasashen Afirka da suka haɗa da gidan talabijin na ƙasar Uganda da hukumar watsa…
Read More
Haɗin Gwiwar Sin da Afirka na samar da fa’ida a zahiri ga jama’ar Afirka

Haɗin Gwiwar Sin da Afirka na samar da fa’ida a zahiri ga jama’ar Afirka

Daga CMG HAUSA Yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya shirya taron manema labaran da aka saba gudanarwa. Kuma wani dan jarida ya gabatar da tambaya cewa, a kwanakin nan, wani binciken jin ra’ayin jama’a da wata hukumar jin ra’ayin jama’a ta ƙasar Burtaniya da ake kira YouGov ta yi, ya nuna cewa, a shekarun baya, al’ummar Afirka sun kara nuna sha’awarsu ga ƙasar Sin. Adadin ‘yan ƙasashen Najeriya da Kenya da Afirka ta kudu da Masar da aka zanta da su, waɗanda ke ganin ƙasar Sin tana da matuƙar tasiri kan harkoki…
Read More
Xi Jinping ya gana da Shugabar Tanzaniya

Xi Jinping ya gana da Shugabar Tanzaniya

Daga CMG HAUSA Da yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwararsa ta ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, wadda ta zo ƙasar Sin don ziyarar aiki. Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin hulɗar dake tsakanin ƙasashensu wato Sin da Tanzaniya zuwa wani babban ƙawancen haɗin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
Read More
Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Legas zai ingiza bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya

Kammala aikin tashar ruwa mai zurfi ta Legas zai ingiza bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya

Daga SAMINU HASSAN A farkon makon nan ne kamfanin gine-gine na CHEC na ƙasar Sin, ya miƙa wa mahukuntan Najeriya aikin ginin tashar ruwa mai zurfi da ya kammala, a yankin Lekki na jihar Lagos dake kudu maso yammcin ƙasar. Ƙwararru da dama na ganin kammala wannan gagarumin aiki a Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, zai ingiza ci gaban tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya. Nasarar kammalar wannan aiki ɗaya ne daga hanyoyin da Najeriya ke morar haɗin gwiwarta da ƙasar Sin, ƙarƙashin shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”. A matsayinta na mafi girma a Najeriya, kuma daya daga mafiya girma a…
Read More
Marubuci da ɗan jarida tagwayen juna ne – Zaidu Barmo

Marubuci da ɗan jarida tagwayen juna ne – Zaidu Barmo

"Ƙaunar juna da son zumuncin marubuta ya sa nake son su" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan Zaidu Ibrahim Barmo wanda aka fi sani da Mr Zaid ba baƙo ba ne, musamman a tsakanin marubutan adabi, saboda yadda yake da son zumunci da kishin yaɗa harkokin rubuce rubucen Hausa. Matashi ne ɗan ƙwalisa daga Jihar Katsina wanda ya shafe shekaru yana rubuce rubuce a ɓangarorin rayuwa daban daban, kama daga kan zamantakewa zuwa mu'amala ta yau da gobe. Bayan kasancewar sa ɗan kasuwa, Zaidu ɗan jarida ne da ya buɗe shafin Mujallar Zauren Marubuta, inda ake ba da labarin rayuwar marubuta…
Read More
Sin ta sanar da shirin bunƙasa fasahar VR

Sin ta sanar da shirin bunƙasa fasahar VR

Daga CMG HAUSA Ƙasar Sin tana fatan samar da na’urorin da ake kira virtual reality (VR) miliyan 25 nan da shekarar 2026, kamar yadda wani shiri game da bunƙasa fasahar ta VR da aka fitar Talatar nan ya bayyana. Wani shiri na haɗin gwiwa da ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa da wasu sassa huɗu da abin ya shafa suka fitar tare, ya nuna cewa, darajar masanan’antar VR na ƙasar Sin da suka haɗa da manya da ƙananan na’urori da waɗanda ake sarrafawa, za ta zarce Yuan biliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 48.1 nan da shekarar 2026. Mai…
Read More
Kyawun alƙawari cikawa

Kyawun alƙawari cikawa

Daga IBRAHIM YAYA A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma hukumomi da masana a fannin yaƙi da sauyin yanayi na yin gargaɗi game da yadda yunwa da fari da sauran bala’u daga indallahi za su iya addabar sassan duniya. Kuma ana iya ganin haka a wasu sassa na duniya dake fama da matsaloli na ambaliyar ruwa ko mahaukaciyar guguwa dake tafe da ruwan sama da ma fari a wasu sassa na nahiyar Afirka da makamantansu. Masana dai sun sha yin gargaɗi tun ma kafin ɓullar annobar cutar COVID-19 ta zama wani…
Read More