Editor

9513 Posts
Za a ɗaure ɗan wasan Jamus, Jerome Boateng da laifin dukan budurwarsa

Za a ɗaure ɗan wasan Jamus, Jerome Boateng da laifin dukan budurwarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotu a Jamus ta tabbatar da laifin cin zarafi kan fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Jerome Boateng, wanda ake tuhuma da laifin dukan tsohuwar budurwarsa a shekarar 2018. A shekarar da ta gabata ne kotu ta samu Boateng da laifin cin zarafin tsohuwar abokiyar zamansa, mahaifiyar ’ya’yansa tagwaye mata, a lokacin hutun Caribbean shekaru huɗu da suka wuce, makwanni bayan kammala gasar cin kofin duniya a Rasha. Sai dai kotun da ke gundumar Munich ta rage yawan tarar da a baya aka buƙaci Jerome Boateng ya biya daga Yuro miliyan 1.8 zuwa Yuro miliyan 1.2.…
Read More
An samu tashin gobara a wani sashen ginin hukumar NYSC a Abuja

An samu tashin gobara a wani sashen ginin hukumar NYSC a Abuja

Daga BASHIR ISAH Rahotanni sun nuna cewa, gobara ta ci wani sashe na ginin Babban Ofishin Kula da Harkokin 'Yan yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) da ke Abuja. Bayanai sun ce iftila'in ya auku ne da safen ranar Juma'a. Daraktan yada labarai na ma'aikatar, Eddy Megwa ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ƙara da cewa, gobarar ta faru ne a hawa na uku na ginin benen mai hawa shida. Ya ce ba a samu asarar rai ba yayin gobarar, kuma wasu kayan aiki ne gobarar ta shafa.
Read More
Gwamnatin Buhari ta yi buris da batun komawar ASUU sabon yajin aiki

Gwamnatin Buhari ta yi buris da batun komawar ASUU sabon yajin aiki

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Buhari ta ja bakinta ta yi gum, bayan da ƙungiyar Malaman jami'o'i ta ASUU ta sake tsunduma wani sabon yajin aiki. Rahotanni sun bayyana cewa, ASUUn ta shiga wannan sabon yajin aikin ne sakamakon biyan 'ya'yan ƙungiyar rabin albashi a watan Oktoba da Gwamnatin Tarayyar ta yi. Wasu rahotannin sun sake bayyana cewa, gwamnatin ta biya ma'aikatan kuɗin kwanaki 18 kacal ne kawai da suka yi aiki a watan Oktoba. Idan za a iya tunawa, a ranar Juma'a 16 ga watan Oktoban 2022 ne dai ASUU ta janye dogon yajin aikin da ta tafi na…
Read More
Shugaban matan PDP na Zamfara ta koma APC

Shugaban matan PDP na Zamfara ta koma APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Shugabar matan jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara, Hajiya Madina Shehu ta fice daga jam’iyyar ta koma jam’iyya mai mulki a jihar, APC. Ta bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ta yi da Gwamna Matawalle a ranar Alhamis. A cewarta, ta bar jam’iyyar ne saboda rashin shugabanci nagari da rikon amana. "Na yanke shawarar barin jam'iyyata ta PDP tare da shugabannin mata daga dukkan ƙananan hukumomin jihar 14 muka koma jam'iyyar APC mai mulki saboda PDP a Zamfara ba ta da salon shugabanci," inji ta. Gwamna Matawalle a nasa ɓangaren…
Read More
Rarara bai fi ƙarfin hukunci ba – Nabraska

Rarara bai fi ƙarfin hukunci ba – Nabraska

"Rarara da Afakallah ɗan Jumma ne da ɗan Jummai" Daga AISHA ASAS Bada jimawa ba wata 'yar ɓaraka ta shiga tsakanin gwamnan Jihar Kano da kuma shahararren mawaƙin siyasa Dauda Kahuta wanda aka fi sani da Rarara. Ita dai wannan ɓaraka ta soma ne a lokacin da mawaƙin ya canza sheƙa ta ɓangaren siyasar jiha, wato,  ya ƙi yi wa ɗan takarar da gwamna mai ci yanzu ya tsayar a ƙarƙashin Jam'iyyar APC mubaya'a. Wannan al'amari dai ya yi tsamari da ya kai da raɗe-raɗen cewa gwamnan ne ya hana sunan mawaƙin fitowa a jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓe,…
Read More
Pique zai yi ritaya daga buga wasan ƙwallon ƙafa gobe

Pique zai yi ritaya daga buga wasan ƙwallon ƙafa gobe

Daga NASIR S. GWANGWAZO Ɗan wasan baya na Ƙungiyar Barcelona, Gerard Pique, ya bayyana shirinsa na yin ritaya daga wasan ƙwallon ƙafa bakiɗaya a gobe Asabar bayan kammala wasan ƙungiyar tasa da Almeria, wanda zai zamo shine wasansa na ƙarshe a tarihi. Pique, mai shekaru 35, ya bayyana hakan ne a kafafensa na sadarwar zamani cikin wani bidiyo a jiya Alhamis. Ɗan wasan tsakiyar bayan dai sau uku kacal Barcelona ta saka shi a jerin ’yan wasa 11 na farko a kakar wasa ta bana, inda matasan ’yan wasa irinsu Ronald Araujo, Jules Kounde, Andreas Christensen da Eric Garcia suke…
Read More
EFCC ta fara binciken aikin samar da lantarki na Mambilla

EFCC ta fara binciken aikin samar da lantarki na Mambilla

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Dattijai ta bayyana cewa, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) tana gudanar da wani cikakken bincike kan aikin samar da wutar lantarki na Mambila da ya kai Dala biliyan shida. Da ya ke magana a Abuja lokacin da ya bayyana a gaban Sanata Gabriel Suswan, ɗan jam’oiyyar PDP daga Jihar Benuwe a Arewa ta Tsakiya tare da kwamitin Majalisar Dattawa kan kare kasafin kuɗin 2023, Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ce, ma’aikatar ta gana da masu ruwa da tsaki kuma a halin yanzu ana ƙoƙarin warware dukkanin matsalolin. Ya…
Read More
Kotu ta tabbatar da zaɓen Abdulmalik Zubairu na mazaɓar Maru/Bungudu a APC

Kotu ta tabbatar da zaɓen Abdulmalik Zubairu na mazaɓar Maru/Bungudu a APC

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ta tabbatar da zaɓen Abdulmalik Zubairu a matsayin ɗan takarar Jam'iyyar APC a mazaɓar Maru/Bungudu a jihar na zaɓe mai zuwa. Ƙarar, wani da akafi sani da Abdurrahman Tumbido ne ya shigar da ita inda yake ƙalubalantar zaɓen Abdulmalik Zubairu a gaban kotun bisa zargin an tafka maguɗi, inda ya buƙaci kotun da ta soke zaɓen. Da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, Alƙalin Kotun, Mai shari’a Aminu Bappa ya yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta. Mai shari’a Bappa ya ce…
Read More
Zamfara SUBEB ta kashe sama da Naira miliyan 300 a ayyuka 65 a makarantun Ƙaura Namoda

Zamfara SUBEB ta kashe sama da Naira miliyan 300 a ayyuka 65 a makarantun Ƙaura Namoda

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta hannun Hukumar Bayar da Ilimi Matakin Farko ta jihar ta aiwatar da ayyuka sama da sittin da biyar a makarantun firamare daban-daban da ke faɗin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke jihar. Sakataren ilimi na Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda, Hamzat Aliyu ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja a ofishinsa a ci gaba da rangadin tantance fannin ilimin ƙananan hukumomin wanda hukumar ta ZSUBEB ta shirya a ranar Talata. A cewarsa, hukumar bayar da ilimin farko ta jihar ta kashe sama da Naira miliyan 350…
Read More
Kuɗin da aka ware don yaƙi da labaran ƙarya sun yi kaɗan – Lai Mohammed

Kuɗin da aka ware don yaƙi da labaran ƙarya sun yi kaɗan – Lai Mohammed

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labaru da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce kuɗaɗen da ake ware wa ma'aikatarsa sun yi kaɗan wanda kuma ke kawo cikas wajen yaƙi da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a gaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dattawa domin kare kasafin kuɗin ma'aikatarsa a 2023. Ya ce ma'aikatarsa na buƙatar kuɗaɗe da ya kamata domin yaƙi da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci. “Idan akwai ma'aikatar da ya kamata a ware wa kuɗaɗe da yawa, to ita ce ma'aikatar yaɗa labaru,'' inji Lai.…
Read More