Rarara bai fi ƙarfin hukunci ba – Nabraska

“Rarara da Afakallah ɗan Jumma ne da ɗan Jummai”

Daga AISHA ASAS

Bada jimawa ba wata ‘yar ɓaraka ta shiga tsakanin gwamnan Jihar Kano da kuma shahararren mawaƙin siyasa Dauda Kahuta wanda aka fi sani da Rarara. Ita dai wannan ɓaraka ta soma ne a lokacin da mawaƙin ya canza sheƙa ta ɓangaren siyasar jiha, wato,  ya ƙi yi wa ɗan takarar da gwamna mai ci yanzu ya tsayar a ƙarƙashin Jam’iyyar APC mubaya’a.

Wannan al’amari dai ya yi tsamari da ya kai da raɗe-raɗen cewa gwamnan ne ya hana sunan mawaƙin fitowa a jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓe, duk da sanin irin gudunmawar da yake bayarwa.

Hakazalika, kafar sada zumunci ta karaɗe da labarin bayar da umurni da gwamnan ya yi na rushe gidan mawaqin, har wasu ke yaɗa cewa, aikin gama tuni ya gama, ma’ana an riga an ruguza gidan. Sai dai a wata tattaunawa da aka yi da mawaƙin ya tabbatar da ba a rushe gidansa ba, kuma ya yi iƙirarin babu wata ɓaraka da ta shiga tsakanin sa da mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Duk da haka ya saki waƙar da za a iya cewa zaurance ce ko in ce mayar da martani ga abin da shi gwamnan ya yi masa na daga cire shi daga lissafin waɗanda ake so su jagoranci yaƙin neman zaɓe.

Ita dai wannan waƙar ta fusata masoyan mai girma gwamna da dama har suka yi yunƙurin mayar da martani, daga cikin su akwai shahararren ɗan wasan barkwancin nan kuma mai bada shawara na musamman ga gwamnan Jihar Kano, wato Mustapha Badamasi, wanda aka fi sani da Naburaska, inda ya fito ya yi kira da babbar murya ga Hukumar Tace Finafinai ta jihar da ta gayyato Rarara ya yi rijista, ta kuma hana shi fitar da wata waƙa har sai ya kawo an tace an kuma ba shi izinin fitar da ita.

Ya kuma qara da cewa, rashin yin hakan zai sa ya ɗauki mataki a matsayin sa na mai ba da shawara na musamman kan farfaganda mai kyau ga gwamnan Jihar Kano, inda ya yi alƙawarin maka shugaban hukumar Isma’ila Na Abba Afakallah da shi kansa Rarara matuƙar aka fitar da wata waƙa makamanciyar wadda aka fitar.

Akan wannan ne shafin Nishaɗi na wannan jarida mai farin jini ya nemi tattaunawa da Naburaska don jin sahihanci da kuma dalilin sa na yanke wannan hukuncin. Idan kun shirya, a sha karatu lafiya:

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kanka.

NABURASKA: Assalamu alaikum wa rahmatulla wa barakatuhu. Sunana Alhaji Mustapha Badamasi Naburaska. Mai bada shawara na musamman ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, Khadimul Islam.

A kwanan nan muka ji ka kana vavatu akan sha’anin da ya shafi waƙa da kuma tace finafinai wanda ya samu tushe daga wata waƙa da aka ce Rarara ya fitar, kuma munga yadda aka yi artabu akan wata waƙa da shi kuma mawaƙi Ado Gwanja ya fitar a can kwanakin baya. Mun ji ka fito da wani ra’ayi da har mutane da dama suka yi mamakin ra’ayin. Kasancewar waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi, za mu so ka bayyana mana wannan ra’ayi naka da kuma alaƙarsa da ofishin da kake riƙo a yanzu?

To, shi wannan ofishi nawa na positive propaganda na Jihar Kano, ofishina na da alaƙa da kowane ofishi matuƙar na Jihar Kano ne. To, duba da irin abababen da suka dinga faruwa a baya, a shekara ta 2005 zuwa 2019, akwai mawaƙan da suka yi waƙoƙi waɗanda ake zargin sun tava muhibbar gwamnatin Jihar Kano, wanda a ƙarƙashin haka, Hukumar Tace Finafinai ta yi duba, ta kuma gayyato su, ta miƙa su a hannun ‘yan sanda, daga nan kuma aka miƙa su kotu, ita kuma kotu ta aika da su gidan yari.

Wasu ma ba a kai su ga ‘yan sanda, kai tsaye daga inda suka samu gayyata ba inda suke zarcewa sai kotu, daga nan kuma sai a wuce wa da su gidan yari, saboda ba su kai waƙoƙin da suka yi an tantance su, an ba su dama idan ba gyara su saki, idan da gyara su je su gyara kafin a ba su damar su saki.

To, abin takaici da mamaki shi ne, sai ga mawaƙi Dauda Abdullahi Adamu Kahutu Rarara, ya yi waƙa ta salo da tava muhibbar gwamnati. To idan har wannan hukuma tana duban Allah a aikin nata, da gaske ta ke, inhar za ta sa akai wasu mawaƙa gidan gyaran hali don ba su kawo an duba ba, to fa babu wani dalilin da zai sa waƙoƙin Rarara ita wannan hukuma ta tace finafinai, ƙarƙashin jagorancin Isma’ila Na Abba Afakallah, ba zata iya gayyato waɗannan waƙoƙin da Rarara ya yi, a duba a gani, kafin a ba shi damar ya saki, ko kuma idan da gyara, je ka gyara wuri kaza da kaza kafin a saki.

Ya saki wannan waqa guda ɗaya, kuma yana sake yunƙurin sakin wata waƙa. Wannan ya ja hankalin al’ummar gari, suke ganin zargin anya shi wannan Afakallah ba shi da alaƙa da wannan waƙoƙi da ake yi. Idan har ba shi da alaƙa da su, to bai kamata ya yi shiru ba. Idan yana da alaƙa da su ne za a ji shiru.

To, ganin an yi shirun ne ya sa na yi yunƙuri kan cewa, idan har Rarara ya sake sakin wata waƙa ta siyasa bai kai Hukumar Tace Finafinai ta tace, an ba shi dama ya saki ba, ni kuma sai na yi ƙarar Hukumar Tace Finafinai, bayan na yi ƙarar ta, sai kuma na yi ƙarar shi wannan shugaba na hukumar wato, Isma’ila Na Abba Afakallah, sai na yi ƙarar sa, kuma na yi shari’a da shi. Saboda bai kare ƙima da muhibba ta gwamnatin Jihar Kano ba.

Shin gwamnatin Kano ba ta da gata ne a yanzu ko bata da ƙima ne, da za a saka ido a ci zarafin ta. A baya ne ta ke da girma idan an tava mutuncinta zai ɗauki mataki, yanzu sai ya kasa ɗaukar mataki.

Duk da cewa mutane na ce cewa, tsakanin Afakallah da shi Rarara ɗan Jumma ne da Ɗan Jummai. Shin so yake ya nuna wa duniya cewa, gaskiya ne ake faɗa?

Idan ko ba haka ba ne, to ya kamata ya miƙe tsaye, ya yi abin da ya dace, don mu nan ‘professional’ ne a aikin da aka ba mu daidai gwargwado, ba kuri ko cika baki muke ba. Mun san yadda za mu kare gwamnati. 

Wasu na ganin wataƙila don a baya ya kare wannan gwamnatin ne, don tana tsaka da ci a lokacin, sai dai a yanzu da ta yi kusa kai ƙarshe ake ganin mai zai sa ya ɓata lokacinsa wurin kare gwamnatin da ke shirin yin odabo. Me za ka ce?

To, wannan magana dai za a iya cewa biri yana kama da mutum, domin yana cin ayaba. Ta wani ɓangaren kuwa, ai ita gwamnati bata ƙarewa. Kuma yanzu koda yaqin neman zaɓe ake ciki, ai in har ka yarda da kanka, kuma ka yarda da Allah, wata gwamnati da zata zo zata iya duba irin ƙoƙarin da ka yi ta yi tafiya da kai, ta sake ɗaukar wannan kujerar da ka riƙe a baya ko ma wadda ta fi ta, ta baka, don ta ga huɓasawar da ka yi.

Idan don gwamnati ta zo ƙarshe ne za ka ce ba za ka yi abin da ya dace ba, to ai baka taimaki gwamnatin da zata shigo ba, don sai ka rufe ƙofa da wani alheri na muhibba da mutuntaka sannan gwamnatin da zata shigo ne a lokacin handin oba za ka ji ance bawan Allah nan ya yi ƙoƙari, saboda haka idan an ba shi kujerarsa ta baya ko wadda ta fi ta ba a yi laifi ba.

Bari in ɗan mayar da kai baya kaɗan. Ka yi zancen Hukumar Tace Finafinai ƙarƙashin jagorancin Afakallah ta kama wasu mawaƙa kan rashin bin dokar da ta tanada. Shin za ka iya sanar da mu wasu daga cikin mawaƙan da aka kama?

Ina da mawaƙa da yawa da na san an kama, an kuma kai su gidan yari, kan wanna dalili. Na farko akwai Sadiq Zazzaɓi, an kama Sadiq ne dalilin ya yi waƙa, bai kai an tace ba, dalilin haka ya samu kansa a gidan yari, an kama Sanusi Oscar 442 da laifin sakin waƙa ba tare da an tantance ta ba, dalilin haka ya tsinci kansa a gidan gyaran hali.

An kama Ƙosan Waƙa da lafin waƙa bai kai Hukumar Tace Finafinai ta tace ba, ya tsinci kansa a gidan gyaran hali. An kama Naziru Sarkin Waƙa da laifin bai kai waƙarsa a duba ba, dalilin haka aka kai shi gidan gyaran hali.

Irin waɗannan kuwa suna da yawa, kaɗan ne daga ciki na ɗauko ma ku, idan kuwa har Rarara zai yi waƙa, ya saki ba tare da bin doka ba, to tabbas shi wannan shugaban na wannan hukuma Afakallah bai yi abin da ya dace ba.

Idan har zai yi abin da ya dace ne, to zai gayyato wannan bawan Allah. Na farko baka kawo an tantance ba, na biyu, ga laifin da muke tuhumar ka da shi. Ka kare kanka tun kan mu kai ga saka hukuma a ciki. Idan ya kasa kare kansa, sai a ɗauki mataki daidai da abin da ya aikata.

Za mu cigaba a mako mai zuwa.