05
Nov
Daga CMG HAUSA A jiya ne, aka buɗe bikin baje kolin ƙasa da ƙasa na kayayyakin da ake shigo da su ƙasar Sin karo na biyar (CIIE) a birnin Shanghai. A jawabin da ta gabatar ta kafar bidiyo yayin buɗe bikin baje ƙolin, babbar darektar ƙungiyar cinikaya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, ƙasar Sin ta zama ƙasar dake kan gaba a duniya wajen fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen ƙetare, kana kasa ta biyu a fannin shigo da kayayyaki da samar da hidima a duniya. Rawar da ƙasar ɗin take takawa a harkokin cinikayyar ƙasa da ƙasa…
