Editor

9513 Posts
Shugabannin Sin da Madagascar sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar dake tsakanin ƙasashen su

Shugabannin Sin da Madagascar sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar dake tsakanin ƙasashen su

Daga CMG HAUSA A yau Lahadi ne shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Madagascar Andry Rajoelina, suka taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen su. Cikin sakon sa, shugaba Xi ya ce tun kafuwar wannan dangantaka shekaru 50 da suka gabata, alaƙar sassan biyu ta ci gaba da kyautatuwa bisa daidaito, duk da sauye sauyen da ake samu a harkokin ƙasa da ƙasa. Ya ce yana dora muhimmancin gaske ga alaƙar dake tsakanin ta da Madagascar, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Rajoelina, wajen amfani da wannan biki, a…
Read More
Dabarun ƙasar Sin na kiyaye yankuna masu dausayi ga zuriyoyi da ke tafe

Dabarun ƙasar Sin na kiyaye yankuna masu dausayi ga zuriyoyi da ke tafe

Daga CMG HAUSA A jiya Asabar ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bikin buɗe taron wakilan ɓangarorin da suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Ramsar, kan yankuna masu dausayi ko COP14 a takaice, wanda aka yi a birnin Wuhan, inda ya jaddada cewa, ya dace a kara samun fahimta, da fadada haɗin-gwiwa, domin ɗaukar matakan kiyaye yankuna masu dausayi a faɗin duniya baki daya. Shugaba Xi ya bayyana wasu ra’ayoyi uku, dangane da aikin kiyaye yankuna masu dausayi, al’amarin da ya tsara shirye-shirye ga kiyaye yankuna masu dausayi a duk duniya. A wajen…
Read More
Ɗan jarida na neman diyyar miliyan N100  bisa naushin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ya yi masa

Ɗan jarida na neman diyyar miliyan N100  bisa naushin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ya yi masa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A yayin da ake bikin ranar cin zarafin 'yan jarida ta duniya a duk ranar 2 ga Nuwanban kowace shekara, wani ɗan jarida a Kano ya fuskancin cin zarafin a wajen shugaban masu rinjaye na Majalisar Tarayya mai makiltar Tudun Wada da Dogowa Hon. Alasan Ado Doguwa. Lamarin dai ya faru ne bayan Doguwa ya kira taron 'yan jarida a gidansa domin maida martani akan rikicinsu da ɗan takarar Mataimakin Gwamnan Kano Hon. Murtala Sulen Garo.  Ɗan jaridar mai suna Abdullahi Yakubu na Jaridar Leadership ya garzaya kotun Gyaɗi-gyaɗi ƙarƙashin jagorancin Halima Kurawa, inda ya…
Read More
‘Yan Nijeriya ba su da hujjar kukan yunwa, inji Buhari

‘Yan Nijeriya ba su da hujjar kukan yunwa, inji Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce, 'yan Nijeriya ba su da wani dalili na yin kuka akan yunwa a lokacin da ƙasar ke da albarkacin katafarun filayen noma. Buhari ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Tambari Hausa TV, wacce aka yaɗa a daren Laraba. Yayin da ya ke amsa tambaya kan yadda ake fama da yunwa a ƙasar, shugaban ya ce, duk wanda da gaske yunwar ya ke ji, to kuwa zai ɗauki kayan noma ya nufi gona. A cewarsa, rufe iyakokin ƙasa da sauran manufofin…
Read More
Gargaɗin yiwuwar harin ta’addanci daga Amurka da Ingila

Gargaɗin yiwuwar harin ta’addanci daga Amurka da Ingila

A ranar 23 ga Oktoba, 2022, Amurka da Birtaniya suka yi gargaɗi kan yiwuwar a kai harin ta'addanci a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, musamman kan gine-ginen gwamnati, wuraren ibada da makarantu, da dai sauransu. Gwamnatin Birtaniya ɗin ta ƙara da cewa hare-haren na iya zama kan mai-uwa-da-wabi kuma zai iya shafar muradun ƙasashen yamma da ma wuraren da masu yawon buɗe ido ke ziyarta. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke yaƙar masu tayar da ƙayar baya da sunan addini a yankin Arewa maso gabas, amma a watan Yuli ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin wani samame…
Read More
Paul Biya: shugaban ƙasa mafi tsufa zai cika shekaru 40 da hawa mulki

Paul Biya: shugaban ƙasa mafi tsufa zai cika shekaru 40 da hawa mulki

Daga WAKILINMU A ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamb, 2022, Shugaba Biya mai shekaru 89 da haihuwa, kuma mafi tsufa a shuwagabannin duniya zai cika shekaru 40 a matsayin shugaban Ƙasar Kamaru. Kamar yadda Jam’iyyar RDPC ta sanar, zata shirya babban biki don nuna farin cikinta ga wannan rana ta cika shakaru 40 akan shugabancin Ƙasar Kamaru da shugaban jam’iyyar ya yi, wato Paul Biya wanda ya zama uba da ya asassa wannan jam’iyya ta RDPC a shekara ta 1985. A cewar Herve Emmanuel Nkom, ɗaya daga cikin mambobin jam’iyyar, bikin zai kasance na murnar nasarorin da aka samu tsayin…
Read More
ASUU ta kira taron gaggawa kan shiga sabon yajin aiki

ASUU ta kira taron gaggawa kan shiga sabon yajin aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Malaman Jami’'o'i (ASUU) ta kira zaman gaggawa na Majalisar Zartarwarta don yanke shawara kan shiga sabon yajin aiki. ASUU ta kiran zaman gaggawan ne sakamakon rabin albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya malaman jami’a bayan sun janye yajin aiki. Wani mamba a kwamitin zartarwar ASUU ya ce, mambobin ƙungiyar sun fusata da yanke albashin nasu da suke zargin Ministan Ƙwadago, Chris Ngige da yi. Wani jami’in ƙungiyar ya shaida wa manema labarai cewa, majiya mai tushe ce ta sanar da su cewa ministan ne ya ba da umarnin yanke albashin da aka biya…
Read More
Gwamnati ta ƙi biyan kishiyar ASUU duk da ƙin shiga yajin aiki

Gwamnati ta ƙi biyan kishiyar ASUU duk da ƙin shiga yajin aiki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sabuwar ƙungiyar CONUA da aka yi wa rajista domin ta zama kishiyar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta koka kan rashin biyan albashin mambobin ƙungiyar duk da ƙin shiga yajin aikin da ƙungiyar ASUU ta dakatar. Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya a ranar Talata, 4 ga Oktoba, 2022, ta yi rajistar ƙungiyoyin malaman jami'a guda biyu da suka haɗa da; 'Congress of Nigerian Universities Academics' (CONUA) da 'National Association of Medical and Dental Academic' (NAMDA). An yi rajistar ƙungiyoyin biyu kafin ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta shafe watanni takwas tana yi a…
Read More
Buhari da Paul Biya sun ƙaddamar da gadar da ta haɗa tsakanin iyakokin Nijeriya da Kamaru

Buhari da Paul Biya sun ƙaddamar da gadar da ta haɗa tsakanin iyakokin Nijeriya da Kamaru

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar gadar da aka gina a tsakanin iyakokin Nijeriya da ƙasar Kamaru. An gina gadar ne a kan zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 19.3, wato dai-dai da Dalar Amurka miliyan 44. A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne dai Buhari da takwaransa na ƙasar Kamaru, Paul Biya, suka haɗa gwiwa suka ƙaddamar da gadar ta Ekok/Mfum mai tsahon kilomita 1.5 da kuma tashar kasuwanci a bodar dukka a garin Mfun, na Jihar Kuros Ribas. Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Ministan harkokin ƙasashen waje, Zubairu Dada, wanda…
Read More
Xi ya yi jawabi ga taron COP14 kan kiyaye filaye masu dausayi

Xi ya yi jawabi ga taron COP14 kan kiyaye filaye masu dausayi

Daga CMG HAUSA A yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bikin buɗe taron wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniyar Ramsar kan yankuna masu dausayi ko COP14 a taƙaice. Ana gudanar da taron ne daga yau Asabar 5 zuwa 13 ga watan Nuwanba, a birnin Wuhan na lardin Hubei dake yammacin tsakiyar ƙasar Sin, a matsayin wurin dake karɓar baƙuncin taron, da kuma makamancin taron dake gudana a Geneva na kasar Swizerland, dukkansu a zahiri da kuma ta kafar intanet. Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa
Read More