Editor

9513 Posts
Darajar masana’antar intanet ta ƙasar Sin zai kai Yuan tiriliyan 4.45 a 2022

Darajar masana’antar intanet ta ƙasar Sin zai kai Yuan tiriliyan 4.45 a 2022

Daga CMG HAUSA Cibiyar nazarin masana’antar intanet ta ƙasar Sin, ta fitar da takardar bayani game da ci gaban tattalin arzikin masana’antar intanet ta ƙasar, inda ta yi hasashen cewa, darajar masana’antar za ta kai yuan triliyan 4.45 a bana, wanda zai kai kaso 3.64 na alƙaluman tattalin arziki na GDP na kasar. A yanzu, masana’antar ta shiga cikin harkokin tattalin arziki da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe kai tsaye, wanda ya shafi rukunoni 45 na tattalin arzikin ƙasar. A shekarar 2021, darajar masana’antar a wannan fanni, ta kai yuan triliyan 2.93, inda aka yi hasashen darajarta a bana za ta…
Read More
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Amurka ta shuka zamba shi za ta girba

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Amurka ta shuka zamba shi za ta girba

Daga CMG HAUSA Rahotanni sun ce, shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce zai matsawa ƙasashen Japan da Holland lamba, don buƙatar su hana fasahohin zamani na ƙera ɓangarorin hada na’urorin laturoni su shiga ƙasar Sin. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin 7 ga wata cewa, abun da Amurka ta yi, ba abu ne da ya kamata wata babbar ƙasa ta yi ba. Kowa ya shuka zamba, shi zai girba, a cewar malam bahaushe. Mai fassara: Murtala Zhang
Read More
Dandalin shawara: mijina ba ya son yin wanka

Dandalin shawara: mijina ba ya son yin wanka

ci gaba daga makon jiya Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Aisha an yini lahiya. Allah Shi taimaka, Ya yi ma ki jagora. To ni ma dai da ‘yar neman shawara na taho kamar yadda aka saba yi. Wallahi miji a gare ni da yake warin jiki, babu ma kamar baki nai. Bai son yin wanka. In ya matso ni kamar in yi amai. Shi ya sa duk da Ina son auratayya wallahi har ban sha’awarta, don da ya matso sai warin ya sa abin ya fita daga raina. Kuma matsalar mijin nau na cikin irin hitinanun mazan nan ne da ba…
Read More
Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai soma aiki kwanan nan -Minista

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai soma aiki kwanan nan -Minista

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Nijeriya ta ba da sanarwar ranar da jirgin ƙasar Abuja zuwa Kaduna zai dawo bayan da ya shafe watanni bakwai ba ya aiki sakamon harin 'yan ta'adda. Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ya ba da sanarwar hakan inda ya ce jirgin zai koma bakin aiki kwanan nan. Ya bayyana hakan ne sa'ilin da yake bayanin ayyukan da ma'aikatarsa ta aiwatar ranar Litinin a Abuja. Ya ce, cikin wannan wata na 11 jirgin zai ci gaba da aiki, tare da cewa an samar da ingantaccen tsaro don kare rayukan fasinjoji. Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Sufurin…
Read More
FIRS ta fara amsar haraji kai-tsaye daga masu manhajojin wasanni na yanar gizo

FIRS ta fara amsar haraji kai-tsaye daga masu manhajojin wasanni na yanar gizo

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tattara haraji ta birnin Tarayyar (FIRS) ta fara cirar haraji daga manhajojin wasannin na yanar gizo ta hanyar zarar harajin a duk yayin da suka yi hada-hadar kuɗi. A wata sanarwar da shugaban zartarwar hukumar, Mista Muhammad Nami ya sanya wa hannu, an bayyana cewa, wannan hukunci na fara zarar harajinta ya samu goyon bayan dukkan mamallakan manhajojin wasannin na yanar gizo. Shi dai wannan tsari na cire harajin nan take wani tsarin cire haraji nan take ne a duk lokacin da manhajojin wasannin suka yi hada-hadar kuɗin ta banki. Sannan kuma a take a…
Read More
Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya, Inji Sarkin Askan Jos

Muna son matasa su karkato da tunaninsu ga sana’o’in gargajiya, Inji Sarkin Askan Jos

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A yayin da sana'o'in gargajiya daban-daban ke samun koma baya, saboda sauye sauyen zamani da rashin samun tallafin hukumomi. An fara ganin farfaɗowar wasu tsofaffin sana'o'in Hausawa na iyaye da kakanni da ke ƙoƙarin jawo hankalin matasa ga raya al'adunsu na gado, don samun abin dogaro. Harkar wanzanci na daga cikin waɗannan sana'o'in da daruruwan matasa ke cin abinci a cikinta, sakamakon sabbin jinin shugabanni da aka samu da ke ƙoƙarin inganta sana'ar da kuma qara kusantar da ƙungiyar raya harkar wanzanci ga gwamnati, don kawo wa sana'ar cigaba. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, ABBA ABUBAKAR…
Read More
Sauya fasalin Naira ba zai magance matsin tattalin arziki a Nijeriya ba -Moghalu

Sauya fasalin Naira ba zai magance matsin tattalin arziki a Nijeriya ba -Moghalu

Daga AMINA YUSUF ALI Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Kingsley Moghalu ya yaba da matakin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin Naira amma sai da ya yi gargaɗin cewa, sauya fasalin kuɗin ba hanya ce da za ta ceto ƙasar daga matsin tattalin arzikin da take ciki ba. A makon da ya gabata ne dai CBN ya ba da sanarwar sauya fasalin takardun Naira 200, 500 da kuma 1000, inda ta bayyana cewa, sabon kuɗin zai fara aiki ne daga tsakiyar watan Disambar shekara ta 2022 da muke ciki. Kodayake, al'amarin ya jawo cece-ku-ce da muhawara mai zafi tsakanin…
Read More
Naira: Daraja za a ƙara ko launi za a sauya?

Naira: Daraja za a ƙara ko launi za a sauya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Babu buƙatar dogon bayani ga wannan batu na shirin sauya samfurin Naira zuwa sabon fasali da zai fara daga tsakiyar watan gobe wato daga 15 ga watan nuwamba 2022. Gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya fito ƙarara ya yi bayani cewa za su sauya fasalin takardar Naira 200, 500 da 1000 zuwa sabon samfuri. Zuwa wannan rubutu ba a fito da fasalin sabon samfurin ba don mutane su gani da hakan zai jagoranci sharhinsu zuwa abun da ya savawa jita-jita ko hasashe. Duk da fitowar ministar kuɗi Zainab Ahmed Shamsuna da ke cewa ba a…
Read More
FAMWAN ta buƙaci ’ya’yanta su yi rijistar zaɓe a a Jigawa

FAMWAN ta buƙaci ’ya’yanta su yi rijistar zaɓe a a Jigawa

Umar AKILU MAJERI a Dutse An buƙaci ’ya’yan Ƙungiyar Musulmi Mata ta FAMWAN a duk inda suke a Jihar Jigawa da su yi ragitar katin zaɓe domin zaɓar shugaba na gari a zaɓen 2023. Shugabar Mata ta Ƙungiyar, Hajiya Maimuna Ahmed Abubakar ce ta yi wannan kiran a wata ganawa da ya yi da wakilinmu na Jigawa a lokacin da ya ke zantawa da ita a Birnin Dutse da ke Jihar Jigawa. Ta kuma buƙaci gwamnati da masu hannu wajen agazawa ƙungiyar a gyara makarantarsu da Islamiyya da suke koyarwa da matan aute da zawarawa da ta samu matsala a…
Read More
Duniya za ta more manyan damammaki uku daga ƙasar Sin mai buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje

Duniya za ta more manyan damammaki uku daga ƙasar Sin mai buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje

Daga CMG HAUSA A daren ranar Jumma’a 4 ga wata ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ta kafar bidiyo, ya halarci bikin ƙaddamar da baje-kolin kayayyakin ƙasa da ƙasa da ake shigowa da su ƙasar Sin ko kuma CIIE karo na biyar wanda ake yi a birnin Shanghai, inda ya yi jawabin dake jaddada cewa, ƙasarsa za ta taimakawa ƙasa da ƙasa, more damammakin ci gaba tare. Xi ya ce, “Ya dace mu kara buɗe kofarmu, don daidaita matsalolin ci gaba, da faɗaɗa haɗin-gwiwa, da ƙara ƙarfin yin ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma samar da ci gaba tare, ta yadda za’a ƙara…
Read More