Sauya fasalin Naira ba zai magance matsin tattalin arziki a Nijeriya ba -Moghalu

Daga AMINA YUSUF ALI

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, (CBN), Kingsley Moghalu ya yaba da matakin Gwamnatin Tarayya na sauya fasalin Naira amma sai da ya yi gargaɗin cewa, sauya fasalin kuɗin ba hanya ce da za ta ceto ƙasar daga matsin tattalin arzikin da take ciki ba.

A makon da ya gabata ne dai CBN ya ba da sanarwar sauya fasalin takardun Naira 200, 500 da kuma 1000, inda ta bayyana cewa, sabon kuɗin zai fara aiki ne daga tsakiyar watan Disambar shekara ta 2022 da muke ciki.

Kodayake, al’amarin ya jawo cece-ku-ce da muhawara mai zafi tsakanin ‘yan Nijeriya. CBN ya bayyana dalilinsa na canza kuɗin saboda barazana da dama da Naira take fuskanta.

Kodayake, Moghalu ya ce yana goyon bayan matakin na gwamnati, domin kasancewar kaso 80 na kuɗin ƙasar yana hannun mutane ba a bankuna ba.

A cewar sa, wannan abun tashin hankali ne matuƙa. Sai dai kuma a cewar sa, ba hanyar warware matsalar tattalin arzikin ƙasar ba ne.

Wannan tsari na sauya kuɗin ya nuna cewa, CBN yana da burin tilasta dukkan kuɗaɗen hannun mutane, su koma bankuna. Idan ba haka ba kuwa, nan da watan Janairun shekara mai kamawa za su zama yayi ko shara.