Naira: Daraja za a ƙara ko launi za a sauya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Babu buƙatar dogon bayani ga wannan batu na shirin sauya samfurin Naira zuwa sabon fasali da zai fara daga tsakiyar watan gobe wato daga 15 ga watan nuwamba 2022. Gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya fito ƙarara ya yi bayani cewa za su sauya fasalin takardar Naira 200, 500 da 1000 zuwa sabon samfuri.

Zuwa wannan rubutu ba a fito da fasalin sabon samfurin ba don mutane su gani da hakan zai jagoranci sharhinsu zuwa abun da ya savawa jita-jita ko hasashe.

Duk da fitowar ministar kuɗi Zainab Ahmed Shamsuna da ke cewa ba a tuntuveta ba kan wannan mataki don haka ba ta goyon baya, bai hana Emefiele tabbatar da cewa aikin gama ya gama ba don ya nuna ya na cikekken goyon shugaba Muhammadu Buhari kuma bankin da alamu ba ya buqatar samun izini daga ma’aikatar kuɗi kan wannan matakin.

Babban bankin ya nuna kimanin kashi 80% na ɗaukacin takardun kuɗin da ke Nijeriya na hannun jama’a ne inda kashi 20% ne kacal ke cikin bankuna.

Hakan in ya zama haƙiƙa ne to ya qara bayyanawa a fili ba lalle kuɗin ma na kasuwanni ba ne a’a jibgin takardun kuɗin ka iya kasancewa a ajiye a wasu rumbuna a gidajen jama’a masu hannu da shuni ko ma’ajiyun ’yan jari hujja.

A kan ba da labarin wasu kuɗin na ramukan ƙarƙashin ƙasa ko cikin wasu gonaki a bayan gari. EFCC ta taɓa gano jerin wasu kuɗi masu yawan gaske na Nijeriya da ketare a wani gida a Kaduna da kuma wani gida a Legas.

Kazalika hukumar ta EFCC ta taba zargin cewa wasu masu riƙe da kuɗin haramun kan sayi gidaje ko filaye don zama kadara a maimakon tura kuɗin bankuna da hakan zai sa hukumomi su san yawan kuɗin da su ke mallaka don ya zama hanyar ƙaucewa bincike.

Ko ma me za a ce ai talakawa ba su da kudi don da zarar sun samu kuɗin za su ruga kasuwa ne su sayi masara ko kayan abinci. Indai kuɗi ba su fi na sayen kwanon masara ba ai ba ma buƙatar kai su banki.

Wani sauyin da a ka samu shi ne a wannan zamani ba lalle sai mutum na mallakar maƙudan kuɗi ne zai iya mallakar asusun ajiya a banki ba. Mallakar asusun ajiya a banki ya ƙara yawa ne don yadda gwamnati da kamfanoni su ka kawo tsarin biyan manya da kananan ma’aikata ta hanyar banki daga tsohon tsarin biyan albashi a tebur ko jido kuɗin a buhu niƙi-niƙi a shigo da su ma’aikata a rabawa kowa adadin haƙƙinsa.

Kazalika babban bankin Nijeriya ya sake vullo da tsarin rage yawo da takardun kuɗi sai ta hanyar katin fidda kuɗi a na’ura wato ATM. Wani dalilin ma shi ne gujewa yadda ’yan fashi da makami kan tare ’yan kasuwa su kwace mu su maƙudan kuɗi don haka said an kasuwa ya dau kuɗin ɓacin rana ya zuba a aljihu yayin da sauran makudan kuɗin ke banki.

Sabon tsarin zamani ma ya nuna mutum ka iya yin odar hajar da ya ke buƙata ta na’ura ya biya ta na’ura a turo ma sa kayansa daga ko ina a faɗin duniyar nan.

Don haka babban bankin Nijeriya CBN zai iya sanin adadin kuɗin da ke yawo a hannun jama’a da waɗanda ke boye a wata mavoyar da ba banki ba.

Don haka ya na da muhimmanci bankin ya riqa samun lokacin bayanai masu ma’ana don fahimtar da jama’a matakan da ya kan ɗauka ba wayar gari lokaci daya ya ce zai aikata kaza ko zaka zuwa lokaci kaza ba.

Abun da ma ya fi damun ’yan Nijeriya shi ne raguwar darajar Nairar ba yawanta a hannun jama’a ba. Za ka ga an tara jibgin Naira ko mutum zai iya cika aljifansa da kuɗi ya shiga kasuwa amma sai ya dawo da ’yan kaya ƙalilan da ba za su biya rinjayen abun da ya je nema ba.

Sauya samfurin kuɗin ba zai kara darajar su ba sai dai ba mamaki ya cimma muradin da ya sa bankin ya dau matakin. Manyan dalilai biyu sun haɗa da dawo da kuɗi banki don bunƙasa tsarin aiki da na’ura da kuma kwaso kuɗi daga dazuka da bankin ya ce su na hannun miyagun iri da kan karɓi kuɗin fansa.

Tuni wannan dalili na biyu na cewa akwai jibgin kuɗin fansa ya samu taɓaɓa daga wajen masu sharhi da dama da ke cewa ta kan yiwu kuɗin na zurarewa wajen Nijeriya ta hanyar sayo makamai ko kuma kuɗin ma na dawowa cikin gari ko bankunan tun da ba abun saya a cikin daji da waɗannan maƙudan kuɗin.

An sake samun zargi daga wasu ’yan siyasa da ke cewa dabaru na hana ’yan adawa samun wadatattun kuɗi a hannunsu a lokacin zave tun da in yanzu sun tanadi takardun kuɗi sun ɓoye a gida don amfani da su a lokacin da kamfen ya ƙara zafi, ba za su iya jidar miliyoyin kuɗi daga banki a lokaci ɗaya ba.

Face bankin ya kore wannan zargi za a cigaba da tattaunawa a kai don a Nijeriya ko kusa ba a tsira daga siyasar amfani da kuɗi ba. An ƙara tabbatar da hakan a zaɓen fidda gwani da ya gabata inda har ma a fagen taron na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a ka ga jami’an EFCC sun bayyana da a ke ganin da zummar cafke masu son sayen wakilai ne don samun ƙuri’a.

An yi zargin a zaɓukan fidda gwani an saye manyan masu faɗa aji na wasu jam’iyyu da hatta Dalar Amurka don samun su kawo wakilan da ke ƙarƙashin su don dangwalawa wani babban ɗan takara mai hannu da shuni baya.

Ko hada-hadar kamfen da ɗaukar shatar jirage don zagaye jihohi 36 da Abuja na buƙatar maƙudan kuɗi da a ke buƙata a lokaci ɗaya ba tare da jinkiri daga bankuna ba. Wani abun ma shi ne don badda sawu wasu da a kan ba wa kasafin kamfen kan karɓi kuɗin a tsabarsu ta hanyar zuba su a manyan jakunkuna da a kan miƙa su hannu da hannu cinikin makaho maimakon tura su ta banki da hakan zai iya sa a samu shaida in buƙatar bincike ta taso.

Ai mun ji labarin yadda a ka riƙa binciken wasu ’yan adawa da karvar wasu kuɗi da wani ko wasu daga ciki su ka ce an kashe su don addu’a.

Har yanzu ba a manta da maqudan kuɗin da a ka ce na makamai ne da wasu ’yan siyasa su ka karɓa daga tsohon mai ba da shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki.

Duk irin wannan yanayi na rubutu kan takarda ko karɓar kuɗi ta hanyar bankuna kan sa wasu buƙatar kuɗin a buhuna. In da ma a ce wasu jam’iyyu ko wasu ’yan ƙalilan ne kan ɓoye kuɗin ba zai zama abun damuwa ba, amma gaskiyar magana za a iya samun wuta a masaƙa maimakon maƙera.

A sanadiyyar matukar tashin farashin Dala, jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC sun kai samame kasuwar canji ta ZONE 4 da ke Abuja. Wannan kasuwa na daga mafi tasiri a tsakanin sauran kasuwannin canjin kuɗi a Nijeriya.

An ga jami’an na EFCC sun girke motocin su biyu a kan magamar hanya inda su ka yi yunƙurin tafiya da wasu masu canjin kuɗin. Wata majiya ta ce aƙalla jami’an sun tafi da wajen mutum 80 inda a halin yanzu a ke yunƙurin karɓo belin su.

An fahimci cewa masu neman canja kuɗin su daga Naira zuwa Dala ne su ka haddasa tashin farashin Dalar don kaucewa zuwa banki da hakan zai sa a gano maƙudan kuɗin da su ka adana. A yanzu haka Dala ɗaya ta haura Naira 800 har ma a na hasashen ta kai Naira 900.

Masu sharhi a kafafen labaru na kira ga babban bankin Nijeriya ya tsawaita lokacin canjin kuɗi don manya da ma ƙananan masu takardun kuɗi su samu damar yin canjin.

Kazalika ga al’ummar karkara da wasun su ma ba su da asusun ajiya na bankuna na buqatar wayewar kai don ɗauko ’yan kuɗaɗen su, su kawo banki don canjawa.

Talakawa da masu hannu da shuni sun tafka asara a lokacin mulkin Buhari na soja da ya kawo canjin kuɗi da zummar dawo da kuɗin da ke hannun ’yan siyasa zuwa bankuna kuma har ya zama lokaci da dogon layi ya sa wasu su ka gaza yin canjin; kazalika wasu kuma sun faɗa hannun ’yan damfara da su ka karbi kuɗinsu da sunan taimakawa don canjin amma su ka wayi gari an cuce su.

Tuni a ka fara samun wasu malaman Islama na zargin akwai wata ɓoyayyar manufa ta cire wasu alamun rubutun ajami a jikin takardun kuɗin kamar yadda a ka yi kan takardar Naira 100.

Kammalawa:

Ya na da kyau gwamnan babban banki ya ƙara fito da haƙiƙanin dalilan yin wannan canjin da kuma ba da tabbacin ba wata asara da wani zai yi a sanadiyyar matakin. Hakanan ya na da kyau Emefiele ya kwaranye raɗe-raɗin cewa matakin ya haɗa da goge haruffan ajami a jikin takardun don kar jita-jita ta yi yawa. In kuma akwai cire ajamin, to bankin ya wayar da kan jama’a cewa hakan ba shi da wata manufa ta nuna wariya ga ma’abota ajamin.