Editor

9513 Posts
Kamfanin Sin ya haskaka ƙauyen Lauteye na Jihar Kanon Nijeriya

Kamfanin Sin ya haskaka ƙauyen Lauteye na Jihar Kanon Nijeriya

Daga FA'IZA MUSTAPHA Hasken lantarki, muhimmin ɓangare ne na ababen more rayuwar ɗan Adam, musammam a wannan zamani da muke ciki da komai ke da alaƙa da hasken lantarki. Tsayayyen wutar lantarki ko akasinsa, wani mizani ne na auna ci gaban wuri. Don haka, samun wutar lantarki daga makamashi mai tsafta, wani karin tagomashi ne ga rayuwar bil adama da muhalli. Na yi wannan shimfida ne bisa la’akari da gagarumar gudunmawar da kamfanin PowerChina ya bayar a baya-bayan nan, inda ya gwangwaje ƙauyen Lauteye na yankin ƙaramar hukumar Bunkure ta jihar Kano dake Arewa maso yammacin Nijeriya, da na’urori 500…
Read More
APC ta naɗa Kannywood cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima

APC ta naɗa Kannywood cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima

Daga BASHIR ISAH Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya amince da naɗin masana'antar shirya fina-finai a Arewacin Nijeriya, Kannywood a matsayin mamba a kwamitin PCC. Naɗin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labarai da mu'amala da jama'a ga Gwamnan Lalong, Dr. Makut Simon Macham, kuma mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Nuwamba, 2022. Gwamna Simon Lalong Sanarwar ta ce, naɗin ya biyo bayan tabbacin da ɗan takarar Shugaban Ƙasa a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bai wa masana'antar ta…
Read More
Gwamnatin Kano za ta maka Sahara Reporters a kotu idan ba ta janye rahotonta, ta ba Ganduje haƙuri ba – Kwamishina

Gwamnatin Kano za ta maka Sahara Reporters a kotu idan ba ta janye rahotonta, ta ba Ganduje haƙuri ba – Kwamishina

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin jihar Kano ta nemi jaridar Sahara Reporters (SR) da ta ba ta haƙuri kuma sannan ta janye rahotonta a kan Ganduje. Bayan sakamakon rahoton EFCC ya wanke gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a kan rahoton da jaridar ta wallafa cewar yana daga gwamnonin Nijeriya waɗanda EFCC ta kasafta a jerin waɗanda suke voye Naira a gidajensu. Hakazalika, gwamnatin jihar Kano ta yi zazzafan Allah wadai ga wani rahoto da jaridar yanar gizon mai suna SR, cewar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana cikin jerin gwamnoni guda uku da suke ɓoye Nairori a…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: ‘2023: PDP ba ta da ɗan takara a Zamfara’

Da Ɗumi-ɗumi: ‘2023: PDP ba ta da ɗan takara a Zamfara’

Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau a ranar Talata ta soke ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 da ke tafe a jihar. Kotun ta bayyana cewa, PDP ba ta ɗan takarar gwamnan a jihar ta Zamfara. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Aminu Baffa ya yanke hukuncin ne yayin zaman kotun kan ƙarar a ranar Talata. An shigar da ƙarar a gaban kotu wanda Injiniya Ibrahim Shehu Gusau ya yi yana mai ƙalubalantar Jamiyyar PDP, Adamu Maina Waziri, Kanal Bala Mande, Dauda Lawal Dare da kuma hukumar INEC kan wasu kura-kurai da…
Read More
Sojojin ruwa sun fara aikin hizba a Fatakwal, sun afka wa gidan karuwai, sun tserar da ‘yan mata 50

Sojojin ruwa sun fara aikin hizba a Fatakwal, sun afka wa gidan karuwai, sun tserar da ‘yan mata 50

Daga WAKILINMU Kimanin ’yan mata sama da hamsin ne aka kuɓutar a gidan karuwai tare da kama wasu mutane uku da ake zargin masu safarar mutane don jima'i ne a wani samame da jami'an sojin ruwan Nijeriya suka kai a wasu gidajen karuwai biyu a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Babban Kwamanda Richard Iginla, Jami’in yaɗa labarai na sansanin sojin ruwa na NNS Pathfinder, ya bayyana hakan a ranar Lahadi ga manema labarai yayin da ya ke gabatar da waɗanda ake zargin a Fatakwal. Iginla ya ce, an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar hukumar hana fataucin mutane…
Read More
Zaɓen 2023: Arewa ina aka dosa?

Zaɓen 2023: Arewa ina aka dosa?

Ban san gaibu ba, amma ga dukkan alamu yankin Arewa na da jan-aiki gabanin zaɓe mai zuwa. Tun da farko qungiyoyi na arewa a bisa jagoramcin Sakataren ta Mal Murtala Aliyu. Sun tsara tare da aiwatar da zama da ’yan takara da a ke kallon su ne a sahun gaba domin miƙa ma su muradu da sharuɗɗan yankin Arewa. An aiwatar da wancen zama a Arewa House na Jihar Kaduna. Ana nan sai mu ka ji wani jigo a wasu gamayyar ƙungiyoyin na arewa mai suna Dr Auwal Abdullahi Aliyu ya fito a wata tattaunawa da wakilin BBC Hausa, Abdussalamu…
Read More
Barazanar hari: ‘Yan Birtaniya na iya ziyartar Abuja – Ofishin Jakadanci

Barazanar hari: ‘Yan Birtaniya na iya ziyartar Abuja – Ofishin Jakadanci

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Birtaniya ta ce yanzu 'yan ƙasar za su iya ziyartar babban birnin Nijeriya, Abuja, ba tare da wani tsoro ba. A ranar 23 ga Oktoba ƙasar ta yi gargaɗin 'ya'yanta su ƙaurace wa Abuja saboda barazanar harin ta'addanci. Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja, ya gargaɗi 'yan ƙasar da su yi taka-tsan-tsan da zamansu a birnin na Abuja. Sai dai kuma, cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na intanet a ranar Litinin da ta gabata, ofishin Jakadancin ya ce 'yan ƙasar na iya ziyartar Abuja duk da dai hadarin barazanar bai gushe ba. Amma ya…
Read More
Sojoji sun kashe shugabannin ’yan ISWAP a tafkin Chadi

Sojoji sun kashe shugabannin ’yan ISWAP a tafkin Chadi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya sun samu nasarar halaka wasu manyan shugabannin ƙungiyar ta'addancin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Tafkin Chadi. An kashe su ne a wani samame da jiragen yaƙin sojin Nojeriya suka kai a tafkin Chadi a ranar Asabar. Kwaya da Mainoka, waɗanda kuma su ne jagororin ’yan ƙungiyar ISWAP Shura (Consultation) Council sun baƙonci lahira a lokacin da Rundunar Sojan Sama na 'Operation Hadin Kai' ta gudanar da aikin ceto a Belowa, ɗaya daga cikin ’yan tsirarun da suka rage na ISWAP/Boko Haram a Tumbuns. Yankin tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Abadam. An…
Read More
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin ta maida martani game da sanarwar Ƙungiyar G7 da ta shafi ƙasar

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin ta maida martani game da sanarwar Ƙungiyar G7 da ta shafi ƙasar

Daga CMG HAUSA Kwanan nan ne ministocin harkokin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar G7, suka fitar da wata sanarwar haɗin-gwiwa a birnin Münster na ƙasar Jamus, sanarwar da ta jibanci harkokin cikin gidan ƙasar Sin, ciki har da batutuwan da suka shafi Taiwan, da Hong Kong, da Xinjiang da kuma Tibet. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin 7 ga wata cewa, sanarwar ta yi biris da babban matsayin ƙasar Sin, gami da hakikanin abubuwan dake faruwa, inda ta yi katsalandan cikin harkokin gidan ƙasar, da shafawa kasar bakin fenti, al’amarin da…
Read More