Editor

9513 Posts
Ƙasar Sin ta kasance ta farko wajen yawaitar mutane masu hazaƙa a duniya

Ƙasar Sin ta kasance ta farko wajen yawaitar mutane masu hazaƙa a duniya

Daga CMG HAUSA Yayin da ake gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da aka shigo da su ƙasar Sin na ƙasa da ƙasa karo na 5, cibiyar CCG ta gudanar da “dandalin tattaunawa kan yadda mutane masu hazaƙa suke kai komo da kuma samun ci gaba a duniya”, sannan an fitar da wani rahoto mai alaƙa na shekarar 2022. Rahoton ya nuna cewa, daga cikin manyan ƙasashe 10 dake kan gaba a fannin takarar mutane masu hazaƙa a duniya, ƙasashen Turai da Amurka da na Asiya sun yi kankankan, yayin da cibiyar dake kula da taruwar mutane masu hazaƙa tana…
Read More
Alaƙar mawaƙa, marubuta, da ‘yan fim a siyasa

Alaƙar mawaƙa, marubuta, da ‘yan fim a siyasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani sabon salon yaƙin neman zaɓe da yanzu haka ya ke ɗaukar hankalin 'yan Nijeriya musamman a nan Arewa, shi ne amfani da fuskokin fitattun 'yan wasan kwaikwayo na masana'antar Kannywood a wuraren tarukan siyasa da cikin ƙungiyoyin yaƙin neman zave. Dama dai filin yaqin neman zaɓe ya saba ganin mawaƙa suna baje kolin basirar su, don zuga ɗan takarar da suke so, ko wanda ya biya su, don ƙara kwarjanta shi a wajen jama'a, da kuma samun na ƙashin miya. Sai dai mai yake janye hankalin matasa masu shirya finafinai da marubuta littattafan adabi da…
Read More
Me ya sa zawarci yake zama lasisin fitsara?

Me ya sa zawarci yake zama lasisin fitsara?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A wannan mako zan so na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta. Da farko dai wacece bazawara? Bazawara ita ce wacce ta rabu da mijinta ta hanyar sakin aure ko kuma wanda ya mutu, ko ma wanda ya ɓace. Ƙasar Hausa kamar yadda muke gani a halin yanzu, ta zama tamkar shalkwatar yaye ƙanana da manyan zawarawa har ma da dattijai. Ba sai na kawo dalilan da suke jawo yawaitar mace-macen aure…
Read More
Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (IV)

Tarihin Sarakunan Fulani na Kano (IV)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A makon jiya muka cigaba da kawo wa masu karatu taƙaitaccen tarihin sarakunan Fulani waɗanda suka fara mulkin ƙasar Kano tun daga jihadin Shehu Usman Ɗan Fodiyo kawo yau. To yau za mu cigaba faga inda muka tsaya. Muhammadu Sanusi I (1953 zuwa 1963) Miladiyya: Sarki Muhammadu Sanusi shi ne Sarki na 53 a jerin Sarakunan Kano, sannan Sarki na 11 a jerin Sarakunan Fulani. Sarki Muhammadu Sanusi babban malamin addini ne kuma sufi. Mutum ne marar tsoro, managarci, sannan masanin addini. Da hawansa karagar mulkin Kano ya fara da tsarkake Masarautar Kano daga ƙazantar giya…
Read More
Kamfanonin Ƙasar Sin sun gina layin dogo da ya haura tsawon kilomita 10,000 a sassan nahiyar Afirka

Kamfanonin Ƙasar Sin sun gina layin dogo da ya haura tsawon kilomita 10,000 a sassan nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce ƙarƙashin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, kamfanonin ƙasar Sin sun gina layin dogo da tsayin sa ya zarce kilomita 10,000, da kusan kilomita 100,000 na titunan mota, da kusan gadoji 1000, da kusan tashoshin ruwa 100, da tarin asibitoci da makarantu a sassan nahiyar Afirka. Zhao Lijian ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da sabuwar gadar Wami da aka bude a baya bayan nan a ƙasar…
Read More
Yin amfani da yanar gizo wajen raya duniya

Yin amfani da yanar gizo wajen raya duniya

Daga BELLO WANG Abokaina, ko kun taba zuwa kauyen Tobolo na jihar Ogun? A can za ku iya ganin yadda yanar gizo ta Internet, da sauran fasahohin sadarwa na zamani suke haifar da sauye-sauye ga zaman rayuwar mutane. Ko da yake babu wutar lantarki a ƙauyen Tobolo, amma ya samu turken sadarwar wayar salula na kansa. Mutanen ƙauyen suna kiran wannan turken sadarwa, da wani kamfanin Sin ya kafa shi, da taken “sanda”, saboda ba shi da girma. Amma duk da haka, na’urar na da inganci: Tana aiki ne bisa yin amfani da zafin rana, kana layin da ta samar…
Read More
Kotu ta tisa keyar shugaban EFCC, Bawa zuwa kurkuku saboda rashin ɗa’a

Kotu ta tisa keyar shugaban EFCC, Bawa zuwa kurkuku saboda rashin ɗa’a

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin tisa ƙeyar Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, zuwa kurkuku bisa laifin raina umarnin kotu dangane da gazawar hukumarsa wajen cika umarnin kotu Alkalin kotun, Mai Shari'a Chizoba Oji ne ya yanke hukuncin tura Bawa gidan kaso a ranar Talata. Alƙalin ya ce shugaban EFCC ya ƙi martaba umarnin da kotun ta bai wa hukumarsa ranar 21 ga Nuwamban 2018, inda kotun ta umarci hukumar da ta maida wa wani da ya shigar da kara a kanta…
Read More
Ɗan takarar majalisa a jam’iyyar APC ya mutu a hatsarin mota

Ɗan takarar majalisa a jam’iyyar APC ya mutu a hatsarin mota

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Nsukka/Igbo-Eze ta kudu ta Enugu a jam’iyyar APC, Ejikeme Omeje, ya rasu a wani hatsarin mota. Omeje ya mutu ne a kan titin Eden Ani/Nsukka, kusa da otal ɗin El-Rina, Nsukka ranar Talata. Jaridar Blueprint ta tattaro cewa, yana tuƙi shi kaɗai a kan titin Erina-Edem Ani, kwatsam sai motarsa ta shiga cikin daji inda motar ta yi karo da wata bishiya a kan hanyar. An garzaya da Omeje asibiti inda ya rasu sakamakon munanan raunuka da ya samu a kai.
Read More
Yadda rokokin sojojin Nijeriya suka hallaka shugabannin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Chadi

Yadda rokokin sojojin Nijeriya suka hallaka shugabannin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Chadi

Daga AMINA YUSUF ALI Wasu ƙasurguman shugabannin mayaƙan ISWAP, Mallam Ali Kwaya da Mallam Bukar Mainoka, sun haɗu da ajalinsu a hannun jami'an sojin Nijeriya a tafkin Chadi, ranar Asabar ɗin da ta gabata. Dubun Kwaya da Mainoka, waɗanda kuma manya ne a majalisar Shura ta ISWAP ta cika ne a lokacin da tawagar sojin sama ta 'Operation Hadin Kai' ta kai musu samame a garin Belowa. Mamatan biyu suna daga cikin ƙalilan ɗin mayaƙan ISWAP/Boko Haram da suka yi saura a boye a yankin Tumbuns, dake tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Abadam. Majiyarmu ta bayyana cewa, Sojojin Nijeriya sun…
Read More
Drogba ya musanta karɓar addinin Musulunci

Drogba ya musanta karɓar addinin Musulunci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ivory Coast, Didier Drogba ya musanta labarin da ke cewa ya karɓi addinin Musulunci. Wannan na zuwa ne bayan da wani malami ya wallafa hotonsa tare da tsohon ɗan ƙwallon suna addu’a a shafinsa na Tuwita. Kotu Ta Daure Barawon Awaki A Gidan KasoMalamin ya wallafa hoton, tare da cewa tsohon ɗan ƙwallon ya musulunta. To sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Drogba ya ce ba musulunta ya yi ba, addu’a kawai ya ke yi wa musulman ƙauyensu bayan da ya ziyarci ƙauyen nasu. Ya…
Read More