Editor

9513 Posts
Haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka na haifar da moriya ga ƙasashen nahiyar

Haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka na haifar da moriya ga ƙasashen nahiyar

Daga SAMINU ALHASSAN A tsakiyar makon nan ne kamfanin gine-gine na kasar Sin na CCCC ya kammala ginin hanyar motar kwalta mai tsawon kilomita 56.5, a yankin Oromia na ƙasar Habasha, wanda ya kunshi gina gadoji 4 masu inganci. Sakamakon kammalar wannan muhimmin aiki, yanzu haka al’ummun dake yankin Oromia za su samu zarafin safarar albarkatun gona masu yawa da inganci da suke nomawa, da suka hada da Alkama, da barley, da ’ya’yan itatuwa zuwa kasuwannin birnin Addis Ababa, fadar mulkin ƙasar. Ko shakka babu irin wadannan ayyuka na samar da ababen more rayuwa, waɗanda kamfanonin ƙasar Sin ke yi…
Read More
Bai dace a ce marubuci na da keɓantaccen salo da aka san shi da shi ba – Hadiza Auta

Bai dace a ce marubuci na da keɓantaccen salo da aka san shi da shi ba – Hadiza Auta

"Rubutun barkwanci yana sa nishaɗi a zuciyar mai karatu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A jerin hirarrakin da muke kawo muku da wasu fitattun marubuta da suka yi fice a wasu ɓangarori na rubutun adabi, har kuma aka san su kan wani salo na musamman da ke jan hankalin masu karatu ga rubuce rubucen su, yau shafin Adabi ya zaƙulo muku wata marubuciya ne da masu karatu da abokan rubutun ta suka karyawa kallabi, saboda ƙoƙarin ta wajen nishaɗantar da masu karatu, da salon ta na rubutun barkwanci. Marubuciya Hadiza D. Auta daga Jihar Zamfara ta shahara wajen rubutun labaran ban…
Read More
Samar da ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki ne sirrin nasarar kowacce makaranta – Dakta Sulaiman

Samar da ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki ne sirrin nasarar kowacce makaranta – Dakta Sulaiman

Daga BABANGIDA S.GORA a Kano Kwalejin koyon aikin jinya ta Emirates dake jihar Kano, Kwalejin ce wacce aka kafa kwanan nan don Bunƙasar harkokin ilimi a Arewacin Nijeriya, sannan wannan makaranta ta yi suna a cikin jihar Kano da ma maƙwabtan jihohi. Dakta Shu'aibu Sulaiman shi ne Daraktan makarantar Emirates. A hirar da da wakilin Blueprint Manhaja, Babangida S. Gora, ya feɗe mana biri har wutsiya game da yadda aka samar da ita, da kuma yadda al'amuran suke tafiya a game da ita. Sai a biyo mu don jin cikakken bayani. BLUEPRINT MANHAJA: Ka fara gabatar mana da kanka. DAKTA…
Read More
Shin akwai dalilin zaɓen APC a kakar zaɓen 2023?

Shin akwai dalilin zaɓen APC a kakar zaɓen 2023?

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA A shekara bakwai da watanni na mulkin Najeriya a karkashin tutar jam'iyyar APC: Ba su gyara wutar lantarki ba.Ba su gyara tsaron Rai ba.Ba su gyara tsaron dukiyar jama'a ba.Ba su gyara harkar lafiya da ilimi ba.Ba su gyara musibar rashawa ba.6.Ba su gyara tsadar abinci da kayan noma ba.Ba su gyara hauhawar farashin kayan masarufi ba.Ba su gyara darajar Naira da tashin Dala ba.Ba su gyara hanyoyin sufurin sama da qasa da ruwa ba.Ba su gyara aikin gwamnati ba a kowanne matakiSun yi alƙawurra ba su cika ba. An ba su amana sun ci. A…
Read More
Yankin Arewa: Shin kulɓa ce take ɓarna, ake cewa jaɓa ce?

Yankin Arewa: Shin kulɓa ce take ɓarna, ake cewa jaɓa ce?

Tun bayan ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙasa da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ‘yan Nijeriya ke ta annushuwa da farin cikin Nijeriya ta yi sabon angon da zai ceto ta daga durƙushewa, amma sai a ka ga saɓanin haka. Abinda ya jefa ‘yan ƙasa cikin taraddadi da halin-ni-‘ya-su, ya kuma saka ‘yan ƙasa tagumi da zullumin abinda ka je, ya zo. Da dama wasu suna ganin lokacin da zasu samu sauƙi ya zo, wasu kuma suna shakkar hakan. Domin wasu kan ce, “BA A SAN MA CI TUWO BA, SAI MIYA TA ƘARE”. Shugaba Buhari ya raba muqamai masu yawa…
Read More
Yau ake zaɓen ƙananan hukumomi a Neja

Yau ake zaɓen ƙananan hukumomi a Neja

Daga WAKILINMU Yau Gwamnatin Jihar Neja take gudanar da zaben Kananan Hukumomi a faɗin jihar. Tuni Gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ayyana ranar a matsayin ranar hutu don bai wa jama'a damar fita zuwa wajen zaɓe. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane. Sakataren ya ce yayin zaben, kasuwanni da ma'aikatu za su kasance a rufe, sannan za a hana zirga-zirgar ababen hawa amma ban da masu ayyuka na musamman. A cewar Matane, “Gwamnati na kira ga 'yan jihar da kowa ya fita ya sauke nauyin da…
Read More
Dabara ta rage ga mai shiga rijiya

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya

Daga IBRAHIM YAYA Yanzu haka ana gudanar da taron ƙasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD ko COP27 a taƙaice, a wurin shakatawa na Sham El-Sheikh dake ƙasar Masar, inda shugabannin ƙasashen duniya za su tattauna kan matsalolin dake hana ruwa gudu game da magance matsalar sauyin yanayi dake ci gaba da addabar sassan duniya ta fannoni daban-daban. Galibin shugabannin ƙasashen da suka gabatar da jawabai a taron na wannan karo, sun ƙara yin kira ne ga ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, da su ɗauki matakai na zahiri maimakon maganar fatar baki da suka saba yi…
Read More
An fitar da takardar bayani a wajen babban taron yanar gizo na duniya na shekara ta 2022

An fitar da takardar bayani a wajen babban taron yanar gizo na duniya na shekara ta 2022

Daga CMG HAUSA Da maraicen yau Laraba 9 ga wata ne, a wajen taron ƙolin Wuzhen na babban taron yanar gizo na duniya na shekara ta 2022, cibiyar nazarin kafar yanar gizo ta intanet ta ƙasar Sin, ta fitar da takardar bayani kan rahoto game da ci gaban yanar gizo ta ƙasar Sin na shekara ta 2022, da rahoto game da ci gaban yanar gizo ta duniya na shekara ta 2022. Tun daga shekara ta 2017, an fitar da irin wannan takardar bayani zuwa ga duk faɗin duniya a cikin jerin shekaru shida, matakin da ya kasance wani muhimmin ɓangare…
Read More
Yadda sakacin jami’an asibiti ya yi sanadiyar mutuwar tsohon Kwamishinan Neja

Yadda sakacin jami’an asibiti ya yi sanadiyar mutuwar tsohon Kwamishinan Neja

Mutum ne mai son ya ga na ƙasa ya taso Daga BASHIR ISAH Kanen marigayi Danladi Nadayebo, Usman Ndayebo, ya ce, rasuwar dan uwansa na da nasaba da sakacin ma'aikatan Asibitin Kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna, babban birnin jihar. A ranar Lahadi hatsarin mota ya rutsa da marigayin da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a hanyar Suleja-Minna inda ya Allah Ya yi masa cikawa washegari Litinin da misalin ƙarfe 2 na rana. Da yake bayani game da yadda abin ya faru, Usman ya ce yayan nasa (marigayin) ya isa Asibitin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare…
Read More
An kaiwa tawagar Atiku hari a Borno

An kaiwa tawagar Atiku hari a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau Laraba ne aka kaiwa ayarin motocin Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari a garin Maiduguri na Jihar Borno. A cikin wani faifan bidiyo da aka gani a shafukan sada zumunta, an ga wasu gungun mutane suna ta gudu ta ɓangarori daban-daban yayin da ake ta harbe-harbe. Wakilinmu ya ga yadda aka lalata motoci a cikin ayarin motocin Atiku a dandalin Ramat da ke Maiduguri babban birnin Jihar. Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku, Sanata Dino Malaye, ya ɗora alhakin harin kan jam’iyya mai mulki a Borno.…
Read More