Editor

9513 Posts
Bikin CIIE na haifar da moriya ga duniya

Bikin CIIE na haifar da moriya ga duniya

Daga CMG HAUSA Alƙaluman da aka fitar dangane da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin ƙasar Sin (CIIE) karo na 5 sun nuna cewa, akwai ƙasashe da yankuna, da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kimanin 145 da suka halarci bikin. Kana, wasu kamfanoni fiye da 2800 na ƙasashe da yankuna 127, sun nuna sabbin kayayyaki da fasahohi kusan 438, adadin da ya dara na bikin bara. Ban da wannan kuma, darajar kwantiragin da aka ƙulla wajen bikin, wadanda za a aiwatar da su cikin shekara mai zuwa, ta kai dalar Amurka biliyan 73.52, jimilar da…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 200 a Zamfara

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 200 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau. Sama da ‘yan bindiga 200 ne sojoji suka kashe a dajin Gando da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara. Mazaunin yankin da ya bayyana sunansa Malam Garba Lawali Bukkuyum ya shaida wa Blueprint Manhaja ranar Juma'a a wata hira ta wayar tarho cewa, sojojin sun fara ba-ta-kashi da yanbindigar da suka addabi yankin a ranar Talata da Laraba da Alhamis din da ta gabata. Malam Garba ya bayyana cewa sojojin sun tare ‘yan bindigar ne a lokacin da suka yi awon gaba da daruruwan shanu daga al’ummar Zuggu da ke ƙaramar hukumar Kebbe a…
Read More
Wakilin Sin ya buƙaci a ƙara ƙoƙarin taimakawa ƙasashen Afirka yaƙar ta’addanci

Wakilin Sin ya buƙaci a ƙara ƙoƙarin taimakawa ƙasashen Afirka yaƙar ta’addanci

Daga CMG HAUSA Zaunannen wakilin ƙasar Sin a Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD), Zhang Jun, ya yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa, da su ƙara ba da taimako ga ƙasashen Afirka don ƙara ƙwarewarsu a fannin yaƙar ta’addanci, ta yadda za a kawar da matsalar daga tushe. Jami’in Sin ya furta haka ne a taron manyan jami’an yaki da matsalar ta’addanci a nahiyar Afirka na kwamitin sulhu na MƊD, inda ya shawarci ƙasashe daban daban, da su taimakawa ƙasashen Afirka ƙarfafa ɓangarori masu rauni, da ba da karin tallafi na kuɗaɗe, da kayayyaki, da bayanai da dai sauransu. Jami’in ya…
Read More
Bayan biyan malaman jami’a rabin albashi, ASUU ta ce ba za ta sake tsunduma yajin aiki ba

Bayan biyan malaman jami’a rabin albashi, ASUU ta ce ba za ta sake tsunduma yajin aiki ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami'a ASUU, ta ce ba za ta kuma komawa sabon yajin aiki ba duk da gwamnati ta saɓa alƙawarin da ta ɗauka musu. Gwamnatin Nijeriya ta biya ASUU albashin rabin wata bayan da ta janye yajin aikin watanni takwas da ta shiga a watan Fabrairu. Ƙungiyar ta yi zama, ta kuma yi Allah-wadai da abin da Gwamnatin Nijeriya ta yi mata a makon da ya gabata. Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ASUU ta kammala zamanta na Majalisar Zartaswa, inda ta yanke ba za ta sake shiga wani sabon yajin aiki ba a nan kusa.…
Read More
A zaftare albashin ‘yan majalisa a biya malaman jami’a – Sanata Ndume

A zaftare albashin ‘yan majalisa a biya malaman jami’a – Sanata Ndume

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata Ali Ndume ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta zaftare albashin 'yan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami'o'i da ke yajin aiki kudaɗensu. Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin wani taro. Jaridun Nijeriya sun rawaito sanatan na cewa wannan abu ne da ya shafi ƙasa bakiɗaya, kuma dole a wasu lokutan a ɗauki matakan ceto 'yan ƙasa da ilimi. Kiran da sanatan ya yi na zuwa ne a daida lokacin da malaman jami'i'oi ke ƙorafin cewa rabin albashinsu…
Read More
Kotun Amurka ta ɗaure ɗan damfara Hushpuppi shekaru 11 a kurkuku

Kotun Amurka ta ɗaure ɗan damfara Hushpuppi shekaru 11 a kurkuku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun Amurka da ke gundumar tsakiyar California ta yanke wa riƙaƙƙen ɗan damfara Raymond Olarinwa Abbas hukuncin ɗaurin watanni 135 a gidan kurkuku. Watanni 135 na daidai da shekaru 11, sannan Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, zai biya ramuwar wasu kuɗaɗe har Dala Miliyan 1,732,841 ga wasu mutum da ya damfara. A cikin watan Afrilu 2021 ne ya amsa laifi ɗaya daga cikin laifukan da ake tuhumar sa da su. An kama shi ne a Dubai inda ya ke da zama, a cikin Yuni, 2020, kuma tun lokacin ya ke ɗaure a…
Read More
NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na kimanin Naira miliyan 200 a cikin watanni 10 a Jihar Kuros Ribas

NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na kimanin Naira miliyan 200 a cikin watanni 10 a Jihar Kuros Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar NDLEA reshen Jihar Kuros Ribas ta kama muggan ƙwayoyi da suka kai Naira miliyan 200 daga watan Janairu zuwa Oktoba 2022. Kwamandan hukumar na jihar Kupi Maulse ya sanar da haka ranar Litinin a garin Calabar. Maulse ya ce hukumar ta kama muggan ƙwayoyin da suka haɗa da hodar ibilis gram 77.9, hodar ibilis ta mai nauyin ruwa gram 104.9, methamphetamine gram 23.4, ganyan wiwi kg 162.52 da wasu ƙwayoyin dake saka maye da har kilogiram 216.12 sannan jimlar su duka zai kai Naira miliyan 50. Ya ce hukumar ta kuma ƙona gonakin…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Borno ta tsare wata akuya bisa laifin cinye kifin sayarwa

Rundunar ‘yan sandan Borno ta tsare wata akuya bisa laifin cinye kifin sayarwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamar yadda jami’in rundunar 'yan sandan Jihar Borno Zagazola Makama, ya bayyana cewa wani mutum mai sana’ar sayar da kifi ya kawo ƙarar wata akuya cewa ta cinye masa tarin kifi da ya kasa don sayarwa. A ƙarar da ya shigar ya ce wannan akuya ta fi shekara biyar tana yi masa ta’adi kuma ya sanar wa mai akuyar. Ibrahim wanda akuyar ta yi masa ta’adi ya ce: ”A wannan rana, akuyar ta riƙa lallaɓowa tana fako na, ni ma kuma na ƙi matsawa. Amma kuma sai ta yi kamar ta tafi, ashe ta…
Read More
Haɗin gwiwar Sin da Afrika kan tattalin arzikin zamani ya bai wa Afrika damarmaki masu kyau

Haɗin gwiwar Sin da Afrika kan tattalin arzikin zamani ya bai wa Afrika damarmaki masu kyau

Daga MINA Abokai, yanzu ana gudanar da babban taron yanar gizo na duniya a ƙasar Sin. Bunƙasuwar Sin a wannan fanni ya amfanawa duk fadin duniya. Yau “duniya a zanen MINA” zai yi muku bayani kan ma’anar hadin kan Sin da Afrika a fannin tattalin arzikin yanar gizo. Taron da ake gudanarwa a birnin Yiwu dake lardin Zhejiang ya samu halartar wakilai fiye da 2000 daga ƙasa da ƙasa, kuma babban abin da ake tattaunawa a taron shi ne hadin kai da samun ci gaba tare. Bisa ƙididdigar da hukumar kula da masana’antu da sadarwa ta ƙasar Sin ta bayar,…
Read More
Ƙasar Sin ta tsara matakai 20 na inganta ayyukan kandagarki da shawo kan annobar Covid-19

Ƙasar Sin ta tsara matakai 20 na inganta ayyukan kandagarki da shawo kan annobar Covid-19

Daga CMG HAUSA Zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin (JKS), ya gana a yau Alhamis, inda mambobinsa suka saurari rahoto game da matakan da ake ɗauka domin shawo kan cutar COVID-19, kana sun tattauna tare da tsara matakai 20, na inganta ayyukan kandagarki da shawo kan annobar. Shugaban ƙasar Sin kana babban sakataren kwamitin ƙolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci zaman tare da gabatar da muhimmin jawabi. Taron ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkun tsare-tsaren kwamitin ƙolin JKS, tare da nacewa aƙidar sanya rayuwar al’umma sama da komai, da wanzar da manufar…
Read More