Editor

9513 Posts
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jinkirta hukunci kan dambarwar Machina da Lawan

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jinkirta hukunci kan dambarwar Machina da Lawan

Daga SANI AHMAD GIWA Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja a ranar Juma'a ta jinkirta yin hukunci kan ƙarar da Jam’iyyar APC ta shigar kan ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa, Bashir Sheriff Machina. APC ta kai ƙarar ne Kotun Ɗaukaka Ƙara inda ta buƙaci kotun ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu wadda Mai Shari'a Fadimatu Aminu ta bayyana Machina a matsayin ɗan takarar Sanata na Jam’iyyar APC a Yobe ta Arewa ranar 28 ga Satumba, 2022. Shar'iar wadda Mai Shari'a a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja, Justice Monica Dongban-Mensen ta jagoranta, ta…
Read More
Atiku Abubakar ya ba da tallafin miliyan N50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Hadejia

Atiku Abubakar ya ba da tallafin miliyan N50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Hadejia

Daga ABUBAKAR M. TAHEER Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar GCON, ya bada tallafin Naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia. Cikin jawabinsa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun zo jajantawa masarautar Hadeja ne ganin irin asarar dukiyoyi da rayuka da aka samu sanadiyar ambaliya. Atiku ya ƙara da cewa, ya bada tallafin Naira miliyan 50 domin a raba wa waɗanda iftila'in ya shafa. Da yake jawabi, Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje CON, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara ta Atiku, kana ya yi kira…
Read More
Gwamnati ta shigar da sabuwar ƙara a kotu kan Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu

Gwamnati ta shigar da sabuwar ƙara a kotu kan Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sake shigar da ƙarar jagoran masu fafutukar ƙasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, kan wasu tuhume-tuhume guda bakwai da ta yi wa gyaran fuska. Rahotanni sun nuna cewa ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CR/383/2015 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na ƙunshe da dukkan tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu a baya wanda kotu ta riga ta wanke shi a kansu. Gwamnati ta sake maka Kanu a kotun ne kimanin wata ɗaya bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke shi daga zarge-zargen da gwamnati ta yi masa a baya.…
Read More
An sa lokacin gudanar da ƙidayar jama’a a Nijeriya

An sa lokacin gudanar da ƙidayar jama’a a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A hirar da Kwamishinan Ƙidayar Jama'a da Gidaje na Tarayya da ke Jihar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye, ya tabbatar da cewa za a gudanar da ƙidayar jama'a a cikin watan Afrilu na shekarar 2023. Injiniya Bala Almu, wanda shi ne Zarman Katsina, ya yaba da yadda hukumar ta samu nasarar shirin na gwajin ƙidayar mutane da gidaje a shiyyar Daura. Zarman na Katsina ya kuma ce za a gudanar da shirin ƙidayar jama'a da gidaje a ko'ina a cikin Nijeriya a watan Afrilu na shekarar 2023. Ya kuma gode wa Shugaban Nijeriya, Muhammadu…
Read More
Yadda rokokin sojojin Nijeriya suka hallaka shugabannin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Chadi

Yadda rokokin sojojin Nijeriya suka hallaka shugabannin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Chadi

Daga AMINA YUSUF ALI a Kano Wasu ƙasurguman shugabannin mayaƙan ISWAP, Malam Ali Kwaya da Malam Bukar Mainoka, sun haɗu da ajalinsu a hannun jami’an sojin Nijeriya a tafkin Chadi, ranar Asabar ɗin da ta gabata. Dubun Kwaya da Mainoka, waɗanda kuma manya ne a majalisar Shura ta ISWAP ta cika ne a lokacin da tawagar sojin sama ta ‘Operation Haɗin Kai’ ta kai musu samame a garin Belowa. Mamatan biyu suna daga cikin ƙalilan ɗin mayaƙan ISWAP/Boko Haram da suka yi saura a ɓoye a yankin Tumbuns, dake tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Abadam. Majiyarmu ta bayyana cewa, Sojojin…
Read More
Kasafin 2023: Naira biliyan 871.3 ba za ta ishi ‘yan sanda ba – Minista

Kasafin 2023: Naira biliyan 871.3 ba za ta ishi ‘yan sanda ba – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Harkokin 'Yan Sanda, Mohammed Dingyadi ya ce Naira biliyan 871.3 da aka ware domin gudanar da ayyukan 'yan sanda a cikin kasafin kuɗin 2023 ba zai isa ba. Dingyaɗi ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata lokacin da ya ke jawabi a taron kare kasafin kuɗin shekarar 2023 wanda kwamitocin majalisar dattawa da na wakilai na majalisar dokokin ƙasar kan harkokin 'yan sanda su ka gudanar. Ministan ya ce kasafin kuɗin da aka ware wa ma’aikatar da hukumominta domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ba zai isa ba. Dingyaɗi ya…
Read More
Abdul Maikwashewa ya zama Shugaban Kwamitin Yaƙin neman zaɓen Tinubu na Kannywood

Abdul Maikwashewa ya zama Shugaban Kwamitin Yaƙin neman zaɓen Tinubu na Kannywood

Daga AISHA ASAS a Abuja Sanannen abu ne cewa, fim da masu yin fim na ɗaya daga cikin waɗanda ke matuƙar tasiri a rayuwar al’umma ta ɓangaren kwaikwayo da kuma samun soyayyar jama’a. Da yawa sukan ɗauki maganar jaruman finafinai fiye da ta shuwagabanni da makalamtansu, wannan ce ta sa suka zama a layin farko a duk lokacin da ake fatan wayar da kan al’umma ko kuma tusa masu ra’ayi ko soyayyar wani abu. Dalilin kenan da ya sa a ɓangaren siyaya suke da muhimmiyar rawa da suke takawa, don haka duk wani ɗan siyasa da ke neman nasara zai nemi…
Read More
2023: Gobe INEC za ta fara bajekolin rajistar zaɓe

2023: Gobe INEC za ta fara bajekolin rajistar zaɓe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce, za a fara bajekolin rajistar masu kaɗa ƙuri’a a gobe Asabar. Festus Okoye, Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a na Hukumar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya a jiya Alhamis. Ya bayyana cewa, a taronta na mako-mako da aka gudanar a ranar Alhamis 10 ga Nuwamba, 2022, hukumar ta tattauna akan nuna gabaɗaya rajistar masu kaɗa ƙuri’a na ƙasa bakiɗaya, don sauraron ƙorafe-ƙorafe…
Read More
Abin da ya sa muka gamsu da manufofin Kwankwaso – Matasan Arewa a Legas

Abin da ya sa muka gamsu da manufofin Kwankwaso – Matasan Arewa a Legas

Daga WAKILINMU Shugaban Gamayyar Matasan Arewa Mazauna Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya bayyana cewa, sun gamsu da manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa yadda suka ƙunshi dabarun magance manyan matsalolin da suka addabi Nijeriya a zamanin nan. A cewar Galadanci, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su zabura su tabbatar da nagarta wajen zaɓen shugabannin da suka cancanta a 2023 domin fita daga halin da suke ciki na rashin tsaro da tsadar rayuwa. Ya ƙara da cewa, “Ƙungiyarmu ta Gamayyar Matasan Arewa a Legas, mun fahimci manufofin ɗan takarar shugaban…
Read More
Xi Jinping zai halarci taron ƙolin G20 da na APEC tare kuma da ziyara a Thailand

Xi Jinping zai halarci taron ƙolin G20 da na APEC tare kuma da ziyara a Thailand

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Madam Hua Chunying, ta sanar a yau Jumma’a cewa, bisa gayyatar da takwaransa na ƙasar Indonesiya Joko Widodo ya yi masa, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping zai isa tsibirin Bali na ƙasar Indonesiya, don halartar taron ƙolin ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G20 karo na 17, wanda zai gudana daga ranar 14 zuwa 17 ga watan da muke ciki. Haka kuma, bisa gayyatar da firaministan ƙasar Thailand Prayuth Chan-ocha ya yi, shugaba Xi zai isa birnin Bangkok na ƙasar, tsakanin ranar 17 zuwa 19 ga wata, don halartar kwarya-ƙwaryar…
Read More