13
Nov
Daga AMINA YUSUF ALI Gamayyar ƙasashen Turai (EU), ta fara zawarcin son ƙara ƙarfafa alaƙar ciniki ta da Nijeriya. Wannan shiri shi ne mafi girman shirin da EU ta fara yi a wajen iyakokinta. Wato shirin nan mai taken 'Mun ga Afirka' ya fara tafiya ba tangarɗa a ƙasashen Nijeriya Kamaru, Kongo, Tanzania da Zimbabwe, kuma ana sa ran zai bi sahun sauran ƙasashen Afirka guda 7 da aka fara gudanar da shi a baya, a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021. Shirin yana harin matasan Nijeriya masu shekaru kamar 18 zuwa 35 waɗanda suke da ido a harkar fasahar zamani.…
