Editor

9513 Posts
ASUU na shirin zanga-zanga kan ƙin biyan mambobinta cikakken albashi

ASUU na shirin zanga-zanga kan ƙin biyan mambobinta cikakken albashi

Daga BASHIR ISAH Akwai yiwuwar ɗaliban jami'oin Nijeriya su sake fuskantar rashin malamai a cikin aji sakamakon shirin da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) na hana malamai shiga aji na yi ɗaya a matsayin zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na "babu aiki, babu albashi" a kan malaman. Rahotanni sun ce, ASUU za ta shirya zanga-zangar ne a rassanta da ke jami'o'in gwamnati a faɗin ƙasa. An ce mambobin ASUU za su yi zanga-zangar ne ta hanyar ƙin shiga azuzuwa balle kuma su karantar da ɗalibai. Ɗaya daga cikin shugannin ASUU na ƙasa ne ya…
Read More
Ɗaya daga cikin ɗaliban Yawuri da aka sace ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Ɗaya daga cikin ɗaliban Yawuri da aka sace ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA Ɗaya daga cikin ‘yan matan Kwalejin Tarayya da ke Birnin Yawuri a Jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka sace ta haifi yaro namiji a sansanin da 'yan bindigar ke tsare da su kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito. Ɗalibar mai shekaru 16 wacce har yanzu ba a bayyana sunanta ba, ta kwashe sama da shekara ɗaya a hannun ‘yan bindigan da suka sace su a watan Yunin 2021. Iyayen ‘yan matan dai sun koka kan yadda ‘yan bindigan suka kalmashe kuɗin fansa tare da aurar da ‘ya’yansu bayan garkuwa da suka yi da su. Idan za…
Read More
‘Yan bindiga sun nemi diyyar miliyan N10 a kan gawa

‘Yan bindiga sun nemi diyyar miliyan N10 a kan gawa

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun nemi a biya su Naira miliyan 10 kafin su miƙa gawar Obadiah Ibrahim wanda suka yi garkuwa da shi makonnin baya a Jihar Kaduna. A cewar majiya ta kusa da marigayin, tun farko sai da 'yan fashin dajin suka karɓi Naira miliyan N3 daga wajen 'yan uwa ba tare da sun sake shi ba. Wani ɗan uwan marigayin, Kefas Obadiah, ya ce tun ranar Litinin da ta gabata Allah Ya yi wa ɗan uwan nasa cikawa amma sai a ranar Alhamis aka sanar da su. Ya ce ɓarayin sun ƙi sakar musu gawar ɗan…
Read More
2023: Tinubu ya yarda gwamnatin APC ta gaza, ya roƙi ‘yan Nijeriya su sake ba su wata dama

2023: Tinubu ya yarda gwamnatin APC ta gaza, ya roƙi ‘yan Nijeriya su sake ba su wata dama

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya yarda cewa gwamnatin APC ta gaza, amma ya roƙi 'yan Nijeriya da kada su yi ƙasa a gwiwa dangane da gwamnatin ta APC. Tinubu ya yi wannan roƙo ne yayin da yake jawabi a wajen taron jana'izar mahaifiyar Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, Grace Akeredolu, ranar Lahadi a Majami'ar Cathedral da ke Imola a yankin Owo. Taron wanda ya samu halarcin jiga-jigan 'yan siyasa da manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, gwamnoni da sauransu. A jawabinsa, Tinubu ya gode wa Allah kasancewar…
Read More
2023: BVAS za ta iya hana maguɗi?

2023: BVAS za ta iya hana maguɗi?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Sabuwar na’urar da hukumar zaɓen Nijeriya ta kawo don zaɓen 2023 wacce an fara ma aiki da ita mai taken BVAS, a taƙaice ta zama bun ambatawa a duk lokacin hukumar ta zaɓe ko wani jami’i da sauran masu ruwa da tsaki za su yi magana da ke nuna ɗaukar matakan hana maguɗi. Zave a Nijeriya kan zama wanda ya samu nasara ko da gaskiya ko kuwa a’a ya yi ta murna hakanan wanda bai samu nasara ba ta hanyar gaskiya ko murɗiyar maguɗi ka ga ya na ƙorafi da tafiya kotu. Ba a faye samun…
Read More
Wang Yi ya halarci taron ƙasa da ƙasa kan fasahar tagwaita irin shinkafa da wadatar abinci a duniya

Wang Yi ya halarci taron ƙasa da ƙasa kan fasahar tagwaita irin shinkafa da wadatar abinci a duniya

Daga CMG HAUSA Mamban majalisar gudunarwar ƙasar Sin kuma Ministan harkokin wajen ƙasar Sin, Wang Yi ya halarci taron ƙasa da ƙasa kan fasahar tagwaita irin shinkafa da wadatar abinci a duniya, wanda aka yi jiya a birnin Beijing. A cewar Wang Yi, babban taron wakilan JKS karo na 20 da aka kammala a baya-bayan nan, ya bayyana cewa, ƙasar Sin za ta bayar da sabbin gudunmuwa ga ci gaban bil Adama ta hanyar zamanantar da kanta, inda sabon ci gaban da ƙasar za ta samu, za ta samar da sabbin damarmaki ga duniya. Ya ƙara da cewa, fasahar tagwaita…
Read More
Nazarce-nazarce sun nuna yadda aka samu ƙarin kyautatuwar ra’ayin al’ummun ƙasashe masu tasowa game da Sin

Nazarce-nazarce sun nuna yadda aka samu ƙarin kyautatuwar ra’ayin al’ummun ƙasashe masu tasowa game da Sin

Daga CMG HAUSA Wasu nazarce-nazarce biyu da jami’ar Cambridge ta Birtaniya ta gudanar, sun nuna cewa, jama’ar ƙasashe masu tasowa na ƙara bayyana kyawawan ra’ayoyi game da ƙasar Sin. A ƙarshen watan Oktoba, cibiyar nazarin makomar demokraɗiyya dake jami'ar Cambridge, ta tattara wasu nazarce-nazarce 30 da suka shafi ƙasashe da yankuna 137, wadanda ke da kaso 97 na al’ummar duniya, inda suka gano cewa, a ƙasashe masu tasowa da suka haɗa da na Latin Amurka da Afrika da Asiya, an samu kyautatuwar ra’ayi game da ƙasar Sin cikin shekaru 2 da suka gabata. Inda a tsakanin al’ummar Nijeriya, ƙarin ya…
Read More
Sharhi: Ɗan Adam makomarsu ɗaya ce a gaban ƙalubalen sauyin yanayi

Sharhi: Ɗan Adam makomarsu ɗaya ce a gaban ƙalubalen sauyin yanayi

Daga LUBABATU LEI Daga watan Yunin bana, mamakon ruwan da aka sheka ya haifar da ambaliya a ƙasashen yammacin Afirka da dama. A Nijeriya, bala’in ya shafi jihohi 34 daga cikin gaba dayan 36, wanda ya sababa mutuwar mutane sama da 600, tare da raba wasu miliyan 1.4 da muhallansu da ma lalata gidaje dubu 820 da kuma gonaki da faɗinsu ya kai eka dubu 110. A Nijer, ambaliyar ruwa ta halaka mutane 195, baya ga wasu dubu 320 da ta rutsa da su. A yankin ƙahon Afirka da ke gabashin nahiyar kuma, bala’in fari da ba a taba ganin…
Read More
‘Yan siyasa na shirin ganin bayan shirin sauya fasalin takardun Naira

‘Yan siyasa na shirin ganin bayan shirin sauya fasalin takardun Naira

Daga BASHIR ISAH Wasu 'yan siyasar ƙasar nan da ke da biliyoyin Naira ɓoye a wajen banki sun yi yunƙurin hana ruwan shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na neman sauya wa Naira fasali gudu. Rahotanni sun ce 'yan siyasar sun ƙi kai kuɗaɗen nasu banki ajiya domin yin amfani da su wajen harkokin zaɓen 2023. Jaridar ThisDay ta ranar Lahadi ta rawaito cewa, 'yan siyasar da lamarin ya shafa sun nemi Majalisar Ƙasa ta taka wa shirin sauya wa Nairar fasali burki gudun kada ya shafi maƙudan kuɗin da suka killace a waurare daban-daban sabanin banki don amfanin zaɓen 2023.…
Read More
Ba zan bar Liverpool ba koda an sayar da ƙungiyar, inji Klopp

Ba zan bar Liverpool ba koda an sayar da ƙungiyar, inji Klopp

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin ƙungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya ce, yana nan kan aikin ƙungiyar ko me zai faru ga waɗanda za su mallaketa a gaba. Tawagar Fenway Sports Group (FSG) ta ce, tana neman sabbin masu zuba jari, sai dai wasu rahotanni na cewa suna son sayar da ƙungiyar ne baki ɗaya. Matakin dai ya janyo fargaba da cece-kuce tsakanin magoya bayan Liverpool inda ake tsoron rikici a Anfield, kuma hakan ya janzo tambaya kan makomar kocinta Klopp. A ranar Laraba, Liverpool ta doke Derby County a bugun fenareti a wasan Carabao. Da ya ke bayani karon farko…
Read More