15
Nov
An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, kan zargin daɓa wa surukinsa kwalba a kai. Lauyan mai gabatar da ƙara, Sufeta Evelyn Motim, ta faɗa wa kotun cewa, mai kare kansa ya aikata laifin ne ranar 30 ga watan Oktoba a yankin Abule Ijaye da ke jihar. Ta ce, wanda ake zargin ya daɓa wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai. Ta ce, surukin ya gamu da iftila’in ne bayan da aka gayyato shi don ya zo ya sasanta matsalar aure, daga nan wanda ake zargi ya haɗa…
