16
Nov
Daga HAMZA DAWAKI (Dawakin hikima) Na lura da rabuwar kawunan mutane zuwa manyan gidaje uku, bayan samun ɓaraka tsakanin shahararren mawakin siyasar nan da ludayinsa yake kan dawo, wato Dauda Adamu Kahutu Rarara da Ubangidansa na siyasa, kuma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Wato yayin da kaso na farko suke ganin shi Rarara shi ne ɗoɗar a kan turba, kuma shi yake da gaskiya a cikin dambarwar, kaso na biyu gani suke yi Gwamta Gandujen ne a kan gaskiya, kuma shi suke mara wa baya a harƙallar. Yayin da kaso na ukun suka kasance 'yan, 'ku casu ba…
