17
Nov
Daga CMG HAUSA Yayin da hankulan duniya ke ƙara karkata ga yadda za ta ƙarke a taron COP27, na ɓangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD, masharhanta da dama na ganin taron babbar dama ce ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki, ta su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen lalubo dabarun gaggauwa na shawo kan ƙalubalen sauyin yanayi, ciki kuwa har da dabarun rage raɗaɗin sauyin yanayin, da gano fasahohin jurewa da ɗorewar rayuwa tare da ƙalubalen, da rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa, da ma batun samar da kuɗaɗen gudanar da waɗannan ayyuka. Tuni…
