Kafin kammala karatunmu gwamnati ta ba mu aiki yana jiran mu – Maimuna Yakubu Muhammed

“‘Yan mata a guje samari barkatai da miƙa wa waya ragamar rayuwarku”

Daga: BABANGIDA S.GORA KANO.

Hajiya Maimuna Yakubu Muhammed ita ce mace ta farko da ta far riƙe matakin darakta na tsawon shekaru 15 a Hukumar Kula da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki, wadda aka fi sani da NACA. Baya ga haka, ta samu ƙwarewa da kuma sanin makamar aiki ta sanadiyyar ziyarar kusan ƙasashe 28 da ta yi. Har wa yau, Hajiya Maimuna ta kasance shugabar ƙungiyar SWODEN, wato ƙungiyar nan da ta ke tallafa wa al’umma ta fuskoki da dama. A tattaunawar su da wakilin Manhaja a Kano, Babangida S. Gora, za ku ji tarihi da kuma gwagwarmayar rayuwa da ta yi. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: mu fara da jin tarihin rayuwarki.

HAJIYA MAIMUNA: Na farko ni haifaffiyar Jihar kano ce, kuma na yi makarantar firamare a unguwar Gawuna inda na yi Gawuna Primary School. Bayan na gama makarantar primary, na wuce zuwa makarantar GGSS Dala ta mata da ke ƙaramar Hukumar Dala, a Jihar Kano. Bayan kammala sakandire, na samu damar ci gaba da karatu inda na je Jami’ar Ahmadu Bello da ke zaria, na karanta Sashen Haɗa Magani, wato, Pharmacy, na kuma kammala a 1980.

Bayan na kammala, na dawo na yi shekara ɗaya a asibitin Murtala Muhammad, sai kuma a 1982 na tafi Jihar Neja inda na yi bautar ƙasa ta shekara ɗaya, daga bisani kuma na dawo asibitin Murtala na ci gaba da aiki a matsayin.

Da yake lokacin ba mu da yawa don haka gwamnati ta turani wurare daban-daban, saboda ƙarancin waɗanda suka karanci pharmacy.

Mu taɓo ɓangaren gwagwarmayar da aka yi.

Eh to, daga tarihin rayuwa, kuma bangama aiki ba, Ina nan sai aka zo ana neman waɗanda za su yi aiki a Bankin Arewa a wancan lokacin, sai na je, na yi shekara shida. Bayan nan na dawo a 1995 na ce aikin ya ishe ni, na gaji.

To, Allah cikin ikonSa, Ina zaune Ina aiki da wata ƙungiyar ƙasashen waje, sai aka ce an buɗe NACA, wata Hukumar Kula da Masu Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki. Sai na koma wurin. Na samu shekaru 15 a matsayin darakta kafin na yi ritaya a shekara ta 2015. Na dawo na ci gaba da harkar ƙungiyata ta Swoden, wanda dama Ina taimaka masu. Sai kuma sauran faɗi-tashi na taimakon al’umma da na ke na saka kaina.

Ko Hajiya ta yi yunƙurin yin wani aiki bayan ritaya daga NACA?

A’a, gaskiya a yanzu bana wani aiki da ya wuce wannan aiki na gidauniyata ta Swoden da kuma aikin sa kai. Amma babu wani aiki da ake biyana, sai dai kasancewar ni pharmacist ce, Ina da chemist ɗina, kuma Ina taɓa kasuwanci da zai tallafa mani.

Ya zancen ƙalubalai a wannan tafiya ta ki?

To gaskiya cikin ikon Allah duk da ban tashi da iyayena ba ban fuskanci wani ƙalubalen rayuwa mai yawa ba, saboda kasan rayuwa akwai abubuwa da dama, na taso hannun kawuna, da daɗi, babu daɗi, kasan lokacin da mu muka yi karatu ma gwamnati Jihar kano ta ɗauki nauyin komai namu, hasali ma kafin mu gama karatu an ba mu aiki, kasancewar ba mu da yawa, kuma daga ɓangaren ilimin kimiya da fasaha, don haka irin wannan ƙalubalen na rayuwa ba mu fuskanci wani cikas ba tunda ga shi ɗan abinda za a iya riƙe iyali tun daga yarana har jikoki akwai, gaskiya babu abin magana anan sai godiya ga Allah.

Ko za mu iya jin wasu daga cikin nasarorin da kika samu?

Nasarorin da na samu kasan shi mai aikin lafiya yadda yake da mutane musamman lokacin da na samu kaina a matsayin darakta a wannan hukuma ta NACA, bazan iya ƙayyade ko mutum nawa na taimaka wa ba, kasancewar idan aka wayi gari kana matsayin shugaba a wuri, kuma a matakin ƙasa mai jihohi 36, kaga kenan an samu dama sosai, kuma alhamdu lillah, an yi amfani da damar da aka samu.

Wacce shawara kike da ita ga mata ‘yan’uwanki?

Na farko maganar tsayawa da gaske wajen abinda mutum yake yi musamman ilimi, ni akan kaina da ban tsaya na yi ilimin nan ba, to da ban kawo matakin da na samu kaina ba. Saboda irin lokacin mu ba mu san wata kwalliya ba ko wani abin azo a gani ba, saɓanin zamanin yanzu. Abin da na ke magana kai shi ne, a yanzu mata sun fi yawan dalilai da zai sa su ta shi su nemi na kansu ko don biyan buƙatunsu na yau da kullum.

‘Yan mata masu tasowa ku maida hankali kan karatu, yawan tara samari barkatai da miƙa wa waya ragamar rayuwarku ba na ku ba ne. Ku guje wa ruɗin duniya da zai kai ku ga zubar da ƙimarku ta ‘ya’ya mata.

Kamar ƙasashe nawa kika samu zuwa ta sanadiyyar aiki ko kuma yawon buɗe ido?

To ba za mu sa Ƙasar Saudiyya ba don wannan kusan za mu iya cewa farilla ne ga dukkan Musulmin da ya cike sharuɗɗan da aka buƙata na daga aikin hajji, bayan ƙasa mai tsarki, na je kusan ƙasashe 27-28 sakamakon tafiya-tafiyen da na yi a Hukumar NACA, don ganin yadda wasu ƙasashen ke magance matsalolin cutar ƙanjamau a lokacin da nake matsayin darakta, kamar ƙasar Amurka,Chana, Netherland, England, Indiya, Germany, Turkey, Central Africa, Korea, South Africa, Ghana, Morocco, Mali, Nijar, Chadi, da dai sauran ƙasashen Nahiyar Afirika da Asia, don gaskiya ban iya tuna wasu, kuma duk darajar wannan aikin na NACA.

Menene babban burinki?

(Dariya) Ahhh to ni dai ba ni da babban burin da ya wuce harkar taimakon da na ke yi in ci gaba da yin ta,ba ni da burin in tara wasu kuɗi ko makamancin haka, kawai fatana Allah ya ƙara buɗa mini in taimaki jama’a.

Wane kalar abinci kika fi buƙata?

Gaskiya na fi buƙatar ‘ya’yan itatuwa, haka kuma kasancewar ni baturiya ce, Ina son duk abincin da za a yi mani a ƙawata shi, ya yi kyau, to zai fi burge ni. Sannan Ina son abincin gargajiya ko wane iri. Yana mun daɗi sosai.

A ɓangaren tufafi fa, wane kika fi so?

Duk da dai mu ba a yi mana horon kwalliya ba, amma ni ko wane irin kaya ya burge ni walau mai arha ko tsada zan iya sa kaya na. Amma kalar da na fi so ita ce, ‘brown’, ita ce kalar da ta fi burge ni.

Ko akwai wani abu da ba za ki iya mantawa da shi ba?

Ka san yarinta idan ta haɗu da maraici, ba za a rasa abin tunawa ba. Wasu lokutan idan na tuna abinda ya faru na yarinta sai na ji daban, amma yanzu abubuwan da sukai yawa za ka iya zagi na ma idan mun haɗu, ka wuce, na manta, saboda irin abubuwan rayuwa da suka yi yawa.

To, madalla, mun gode da lokacin da kika ba mu.

Ni ma na gode, Allah Ya ƙara ɗaukaka.