Cibiyar “Africa CDC” za ta zamo muhimmiyar kyautar Sin ga nahiyar Afirka

Daga CMG HAUSA

Tsohon jakadan ƙasar Habasha a MƊD Teruneh Zenna, ya ce cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Afirka ko “Africa CDC”, wadda ƙasar Sin ke samar da tallafin ginawa, za ta kasance ƙarin kyautar Sin ga nahiyar Afirka.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Mr. Zenna ya ce baya ga samar da kuɗaɗen aikin, ƙasar Sin din ce kuma ke aiwatar da ginin cibiyar, wadda za ta ƙunshi dukkanin kayayyakin aiki da ake buƙata, na inganta bincike da haɓaka harkar kiwon lafiya a Afirka.

Zenna ya ƙara da cewa, ta amfani da helkwatar AU a matsayin cibiyar ba da umarni, AUn za ta taimakawa ƙasashe mambobin ta wajen ƙarfafa ƙwarewarsu a fannin gaggauta ganowa, da shawo kan ɓarkewar cututtuka masu haɗari, kamar cutar Ebola, da COVID-19, da zazzaɓin shawara da dai sauran su.

Tsohon jakadan ya ce ƙari kan haka, cibiyar za ta zamo wani dandali da ƙwararrun masana kiwon lafiya na Sin, za su rika taimakawa takwarorin su na Afirka, da dabarun ƙarfafa sanin makamar aiki a fannin yaki da annoba da ka iya ɓulla a nan gaba.

An fara ginin cibiyar “Africa CDC” ne tun a watan Disambar shekarar 2020 a birnin Addis Ababan ƙasar Habasha.

Ginin cibiyar na da faɗin kusan sakwaya mita 40,000, cikin faɗin filin da ya kai sakwaya mita 90,000.

Ana kuma fatan kammala ta a ƙarshen watan Disamban bana.

Mai Fassarawa: Saminu Alhassan