Raya ƙasa bisa yanayin da ƙasar ke ciki

Daga BELLO WANG

Kwanakin baya, na ziyarci wani lambun ‘ya’yan itatuwa dake yankin karkarar birnin Beijing na ƙasar Sin, inda ake yin amfani da na’urorin zamani har nau’ika 28, wajen gudanar da aikin gona.

A baya ana buƙatar ma’aikata masu kula da lambun har 60, amma yanzu mutane 6 ne kacal ake buƙata, inda suke sarrafa injuna masu gudanar da dukkan ayyuka daban daban.

Shin yawan yin amfani da injuna zai sa manoma su rasa guraben aikin yi? A’a, ba haka ba ne. Wani farfesa mai suna He Xiongkui dake samar da fasahohin zamani ga wannan lambun ‘ya’yan itatuwa ya gaya mana cewa, yanzu haka ci gaban biranen ƙasar Sin ya sa matasan kauyukan ƙasar ƙaura zuwa cikin birane, don neman zaman rayuwa mafi inganci, lamarin da ya haddasa ƙarancin ma’aikata a yankunan karkara.

Don daidaita wannan matsala, dole ne a ƙara yin amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da aikin gona.

Wannan dabara ce da ƙasar Sin ta ɗauka, a ƙoƙarin zamanintar da aikin gona, kana ta nuna wata halayyar musamman ta dabarar raya ƙasa ta ƙasar Sin, wato “zabar hanyar da ta dace da yanayin da ƙasar ke ciki”.

Wannan halayya ta sa hanyar da ƙasar Sin ke bi a ƙoƙarin zamanintar da kai ta sha bamban da ta ƙasashen yamma, hakan na nuna cewa Sin ba za ta yi koyi da dabarun wasu ƙasashe na yaƙar sauran kasashe ba, da yin mulkin mallaka, da kwatar dukiyoyin al’ummun duniya.

A maimakon haka, ƙasar Sin na tsayawa kan hanyar raya ƙasa cikin lumana. Idan mun nazarci tarihin Sin, za mu ga cewa, tsakanin shekarar 1840 da ta 1945, bi da bi ne wasu ƙasashen Turai da ma ƙasar Japan, suka kai wutar yaki ƙasar Sin ɗaya bayan ɗaya, lamarin da ya jefa ƙasar Sin cikin yanayi mai matuƙar wuya.

Kana ƙasar ta daɗe ba ta samu farfaɗowa ba, kafin ta zama cikin wani yanayi na zaman lafiya a shekaru gomai da suka wuce.

Kamar yadda Hausawa kan ce “Kowa ya san ciwon kansa, ya san na wani”. Wannan tarihi na fama da hare-haren da wasu ƙasashen waje suka kai mata, ya sa ƙasar Sin zama wata ƙasar dake iyakacin ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Ban da wannan kuma, tunanin “zabar hanyar raya ƙasa mai dacewa da yanayin da ƙasar ke ciki” shi ma ya sa ƙasar Sin saka buri na bai wa dukkan al’ummun ƙasar damar samun wadata.

Dalilin da ya sa haka, shi ne tsarin siyasa na Gurguzu na ƙasar. Wannan tsarin ya sa ana kokarin tabbatar da adalci a zaman al’ummar ƙasar, da magance ƙaruwar gibi tsakanin al’umma.

Haƙiƙa a cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, hukumar ƙasar Sin ta fid da kimanin mutane miliyan 800 daga ƙangin talauci. Wannan jimilla ta shaida ƙoƙarin gwamnatin ƙasar na neman wadatar da dukkan al’ummun ta.

Haka zalika, yadda ake raya ƙasa bisa yanayin da ƙasar ke ciki shi ma ya sa kasancewar al’ummar ƙasar ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin ta zama dole. Idan mun waiwayi baya, za mu ga yadda a cikin shekaru fiye da 100 da suka wuce, jam’iyyar ta yi ƙoƙarin daidaita matsalolin da kasar ke fuskanta, gami da yi wa kanta kwaskwarima, ta yadda sannu a hankali, ƙasar ta raya kanta, daga wata ƙasa mai raunin tattalin arziki, zuwa wata ƙasar da karfin tattalin arzikinta ya zama na biyu a duniya.

Ta hanyar gudanar da mulki cikin nasara, jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin, ta shaida ƙwarewarta a fannin yin gyare-gyare, da tsara shiri na dogon lokaci, tare da samun cikakken goyon baya daga jama’ar ƙasar.

Yadda ƙasar Sin take la’akari da yanayin kanta, ya sa ta zabar dabarar raya ƙasa da ta sha bamban da ta ƙasashen yamma.

Kamar dai yadda Hausawa su kan ce, “Kayan aro ba ya rufe katara”, kana “Ko wace kwarya tana da marufinta”, abun da ya fi muhimmanci, shi ne zabar turba mai dacewa da kai, wadda za ta haifar da haƙiƙanin ci gaban kasa.

Mai fassara: Bello Wang