Editor

9513 Posts
Shugaban Ƙasar Sin ya miƙa saƙon taya murna gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman ƙasar

Shugaban Ƙasar Sin ya miƙa saƙon taya murna gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman ƙasar

Daga CMG Hausa Babban sakataren kwamitin ƙolin JKS kuma shugaban ƙasar Xi Jinping, ya mika sakon taya murna a madadin kwamitin ƙolin JKS, ga daukacin manoman ƙasar, da sauran waɗanda ke gudanar da ayyuka daban-daban masu nasaba da noma da raya karkara, gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman ƙasar Sin karo na 5. Xi, ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da ci gaba wajen farfado da ƙauyuka, da aiwatar da matakan samar da wadata, da jin dadin rayuwa, da kyakkyawan muhalli ga mazauna yankunan karkara. Mai fassara: Saminu Alhassan
Read More
Sin ta samu ci gaba a ginin tashar sadarwa ta 5G

Sin ta samu ci gaba a ginin tashar sadarwa ta 5G

Daga CMG HAUSA Ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta ƙasar Sin, ta ce adadin tashoshin samar da tsarin sadarwa na 5G dake ƙasar Sin na ƙaruwa, yayin da kasar ke ƙoƙarin inganta ginin tsarin sadarwar a shekarun baya bayan nan. Alƙaluma daga ma’aikatar sun nuna cewa, zuwa ƙarshen watan Agusta, ƙasar Sin na da tashoshin 5G sama da miliyan 2.1, wanda ya ɗauki kaso 19.8 na tashoshin samar da 5G din ga na’urorin tafi da gidanka, adadin da ya ƙaru da kaso 5.5 daga ƙarshen shekarar 2021. Haka kuma, cikin watanni 8 na farkon bana, an gina ƙarin…
Read More
‘Sanadin Kenan’ (5)

‘Sanadin Kenan’ (5)

Daga FATIMA ƊANBORNO Ƙananun likitocin suka karɓe ta bayan dube-dube suka tabbatar masa babu abin da za, su iya yi dole sai Dokto Mus'ab ya zo ya taimaka masu. Sun ƙara da cewa akwai marasa lafiya biyu da a ke ta kiransa akan ya zo amma har yanzu bai ɗaga wayar ba, abin da bai tava aikatawa ba. Sulaiman ya lalubi aljihunsa a lokacin da ya zaro wayarsa ya yi hamdala da bai manceta a gida ba. Ya dubi wacce take yi masa bayanin ya ce "Amma kun tabbatar tana raye ko?" Ta gyaɗa kai, "Tana da ragowar numfashi. Amma…
Read More
Yajin aiki: ASUU ta ce za ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu

Yajin aiki: ASUU ta ce za ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu

Biyo bayan umarnin da kotu ta bai wa Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) kan mambobinta su koma bakin aiki ba tare da ɓata lokaci ba, ƙungiyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa kotu ta gaba. A ranar Laraba ce dai Kotun Ma’aikata ta Kasa ta bai wa malaman jami’o’in umarnin komawa bakin aiki har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar. Amma ASUU ta ce ta soma hada kan jiga-jigan lauyoyi karkashin jagoranci babban lauyan nan, Femi Falana don su wakilce ta wajen daukaka karar. Cikin wata sanarwa da ya fitar…
Read More
Ƙungiyar Marubuta ta Arewacin Najeriya ta gudanar da taronta na shekara

Ƙungiyar Marubuta ta Arewacin Najeriya ta gudanar da taronta na shekara

*Gwamnati za ta ci gaba da haɗa hannu da marubuta don ci gaban ilimi, inji gwamnatin Katsina *Ya kamata a duba yiwuwar koyar da wasu darussa cikin yaren Hausa - Farfesa Amale *An karrama Ala da Balaraba Ramat a wurin taron Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙungiyar Marubuta ta Arewacin Najeriya "Northern Nigeria Writer's Summit" ta gudanar da babban taronta na shekara shekara na bana a Katsina. Kamar kowacce shekara mutane masu tarin yawa waɗanda suka haɗa da gwamnan Katsina, Manyan malaman jami'o'i, marubuta littattafan adabin harsuna daban daban a Arewacin ƙasar nan, yan fim da kuma mawaƙa kan halarci…
Read More
Na yi nasarar samar wa mutane aiki albarkacin sana’ata – Munirat Umar

Na yi nasarar samar wa mutane aiki albarkacin sana’ata – Munirat Umar

"Da sana'a za ki iya share hawayen kanki da kanki" Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Munirat Umar da aka fi sani da M-raah's kitchen, yar kasuwa ce da ta shafe shekara 7 tana sana'ar hannu kala daban-dadan, munirat Umar 'yar boko ce da ta karanci Tsumi da Tanadi, wato Accounting. Sai dai bata bari kwalin digirinta ya hanata yin sana'a ba, don dogaro da kai. Jajirtacciyar mace da ta yarda sana'a mafita ce ga matsalolin rayuwa musamman ma ga 'ya'ya mata. A hirarta da wakilin Blueprint Manhaja a Kano Ibrahim Hamisu, ta bayyana masa yadda ta fara sana'a da kuma…
Read More
Kowa ya ci buzu…

Kowa ya ci buzu…

Daga IBRAHIM YAYA A kwanakin baya ne wasu kafofin watsa labaran Amurka suka ruwaito wani rahoton da cibiyar bincike ta Pew ta gudanar dake nuna cewa, kimanin kashi 77 cikin 100 na Amurkawa baƙaƙen fata, sun bayyana cewa, ya kamata zuriyar mutanen da aka bautar a tarihin ƙasar, a biya su diyya. Sai dai kuma, a cewar rahoton yawancin waɗanda aka zanta da su, ba sa tunanin cewa, za a biya baƙaƙen fatan diyyar, ko da yake, ƙungiyoyin ƙabilu da wasu Amurkawa sun dade suna fatan ganin hakan ya tabbata. Sannu-sannu aka ce ba ta hana zuwa, sai dai a…
Read More
Wakilin Sin ya zargi kan yadda Amurka ke tsare mutane ba bisa doka ba

Wakilin Sin ya zargi kan yadda Amurka ke tsare mutane ba bisa doka ba

Daga CMG HAUSA Wakilin ƙasar Sin ya zargi kan yadda ake tsare mutane ba bisa doka ba a Amurka a yayin taron yin musayar ra’ayoyi da kwamitin kare hakkin ɗan Adam na MƊD karo na 51 da hukumar kula da batun tsare mutane ba bisa doka ba suka shirya tare a ranar 19 ga wata. Wakilin Sin ya bayyana cewa, a shekarar 2021, Amurka ta tsare baƙin haure sama da miliyan 1.7, kuma a ciki akwai 80%, ciki har da yara dubu 45 da aka tsare su a gidajen yari masu zaman kansu. Bugu da kari, yanayin irin waɗannan gidajen…
Read More
Sarki Charles (III), Musulunci da Sufanci: Sharhi a kan Bayanan Khalifa Muhammadu Sunusi (II)

Sarki Charles (III), Musulunci da Sufanci: Sharhi a kan Bayanan Khalifa Muhammadu Sunusi (II)

Dafa FATUHU MUSTAFA In mai karatu yana zaton zai ga na yi bayani akan alaƙar gidan sarautar Ingila da Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ne, to sai in ce ya daɓo a ƙasa. Domin ba abinda ya kawo ni ba kenan. Ƙila idan na samu lokaci, nan gaba zan yi wannan bayanin. Amma a yanzu abinda yafi ɗaukar hankali na shi ne, bayanin da Sarkin Kano, Halifa Muhammadu Sunusi ya yi ne a hirar sa da gidan rediyon RFI akan alaƙar diplomasiyya da ke tsakanin sabon Sarkin Ingila wato Sarki Charles III da addinin Islama, musamman alaqarsa da sufaye.…
Read More
An kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi

An kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi

Daga CMG HAUSA Alƙaluman da ma’aikatar aikin gona da raya ƙauyuka ta ƙasar Sin ta fitar sun nuna cewa, zuwa yanzu an kusan kammala kashi 20% na aikin girbin hatsi na lokacin kaka a ƙasar. Yawan gonakin hatsi da aka girbe ya kai fiye da kadada miliyan 15.7, jimillar da ta kai kashi 18.1% na ɗaukacin gonakin hatsi dake ƙasar. An bayyana cewa, yadda ake girbin hatsin cikin sauri, ya ƙaru da kaso 0.9, idan an kwatanta da na bara. A dangane da yadda ake gudanar da aikin girbin hatsi a wurare daban daban na ƙasar kuwa, ya zuwa yanzu…
Read More