‘Sanadin Kenan’ (5)

Daga FATIMA ƊANBORNO

Ƙananun likitocin suka karɓe ta bayan dube-dube suka tabbatar masa babu abin da za, su iya yi dole sai Dokto Mus’ab ya zo ya taimaka masu. Sun ƙara da cewa akwai marasa lafiya biyu da a ke ta kiransa akan ya zo amma har yanzu bai ɗaga wayar ba, abin da bai tava aikatawa ba.

Sulaiman ya lalubi aljihunsa a lokacin da ya zaro wayarsa ya yi hamdala da bai manceta a gida ba. Ya dubi wacce take yi masa bayanin ya ce “Amma kun tabbatar tana raye ko?”

Ta gyaɗa kai, “Tana da ragowar numfashi. Amma daga yanzu zuwa kowane lokaci ana iya rasata.”

Mus’ab yana kallon kiran ya ƙi ɗauka. A gajarce ya aika masa da saƙo, “Ka yi haƙuri ka zo. Salima ce an kawota asibitinku bata san waye ke kanta ba.”

Bayan kammala karantawa ya ji kansa ya yi masa wani irin sarawa. Da sauri ya miƙe kawai ya yi waje. A falon ya sami Umma tana kwance a dogon kujera barci ya kwasheta. Ya fahimci sarai gadinsa take yi dan haka ya girgiza kai tare da wucewa, baya son ko kaɗan ya tasheta.

“Ina za ka je?” Ya jiyo muryarta tana tambayarsa. Ya tsaya cak! Sai kuma ya waiwayo ya ce, “Umma kiran gaggawa a ka yi min.” Ta ɗan yi shiru sannan ta ce,
“Allah ya tsare ka.”

Ya amsa cike da ƙwarin guiwa ya wuce. A gigice ya tada motar yana jin tamkar ba zai isa asibitin ba. Tunani ne kala-kala a cikin zuciyarsa. Yana tunanin muddin wani abu ya sami Salima sai zaman duniyar ta zamewa Sulaiman masifa.

Yana shigowa cikin harabar asibitin ya ji ana cewa, “Allah ya yi mata rasuwa.”
Tabbas Sulaiman ake sanarwa. Mus’ab ya ware idanu bakinsa yana kyarma ya ce, “What! Ta rasu fa kika ce? Ta rasu?”

Sulaiman ya sunkuyar da kai yana tsiyayar hawaye. Ita kanta Asma’u jikinta ya yi sanyi. Mus’ab ya ƙaraso ya ɗaga shi idanunsa jajir ya ce, “Kukan me za ka yi?

Salima ce fa ta rasu. Kamata ya yi a yanzu ka dariya ka gode Allah da ya ɗauke maka ita daga cikin rayuwarka. Macen da ka mayar da ita tamkar dabba! Ita a ke sanar da kai rasuwarta a yanzu. Sulaiman ka cuci kanka, ka rasa mace ta ƙwarai.

Ka rasa uwa ta gari agun ‘ya’yanka. Ka rasa mace mai haƙuri da juriya. Ka je ka ɗauki gawarta ku bar mini asibitina. Ina so daga yanzu ka shafe tarihin abotarmu. Kada ka kuskura ka sake tuna cewa ka sanni. Ni bana zama da azzalumi. Zuciyata a wanke take, bai kamata in zauna kusa da mai ɗauke da ƙazantacciyar zuciya ba.”

Ya sake shi yana yi masa wani irin kallo. Zuciyarsa tana suya, ya kasa riƙe kansa a lokacin da jiri mai ƙarfi ya so fizgarsa. Da sauri ya dafe bango yana haƙi.

Sulaiman kuwa kuka yake yi riris. Ya sami hukunci daga Mus’ab saura mahaifinsa. Ya tabbata yadda Mus’ab ya roƙi ya shafe komai nasa, haka mahaifinsa zai fatattake shi daga cikin iyalansa.

“Dokto Mus’ab don Allah ka ƙaraso tana motsi.”
Ji ya yi kamar ya tashi daga barci. A gagauce ya wuce ciki suka turo ƙofa. Ya ƙura wa kyakkyawan fuskarta idanu, daga bisani ya fara duba ta cikin gaggawa. Har kusan ƙarfe huɗun asuba yana tsaye akanta. Duk da sakamakon binciken da ya tura bai fito ba, ya fahimci Salima ta haɗu da mummunan ciwon nan da ke addabar mata wanda yake saka su su zama kamar mahaukata wato cutar ‘Damuwa.

Mus’ab ya fito yana sharce gumi. Ya tambayi ina Sulaiman. Ɗaya daga cikin ma’aikatansu ya gaya masa ya tafi mota ya kwanta da matarsa wai barci suke ji. Tirƙashi! A take kamannin Mus’ab suka sauya daga Mus’ab ɗin da ya sani, zuwa wani Mus’ab ɗin da bai taɓa sani ba.
Mu je zuwa.

‘Yar mutan Bornonku ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *