Editor

9513 Posts
Ƙasashen Afirka na ƙara gamsuwa da shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya

Ƙasashen Afirka na ƙara gamsuwa da shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya

Daga SAMINU HASSAN Yayin da wasu sassan na ’yan siyasar ƙasashen yamma ke nuna shakku kan sahihancin niyyar ƙasar Sin, game da cudanyarta da ƙasashen Afirka, har ma wasu ke zargin cewa wai Sin na danawa ƙasashen na Afirka tarkon bashi, a hannu guda, masharhanta da dama na ganin wannan zargi ba shi da tushe ko makama. Ga misali, ƙarƙashin shawarar nan ta ziri ɗaya da hanya daya, ƙasar Sin ta yi haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka da dama, wajen samar da manyan ababen more rayuwa masu matuƙar tasiri ga ci gaban ƙasashen na Afirka. Ga misali, a baya bayan…
Read More
Rundunar sojan ƙasar Sin ta gamsu da sakamakon atisayen soja da ta yi a yankin teku dake gabashin zirin Taiwan

Rundunar sojan ƙasar Sin ta gamsu da sakamakon atisayen soja da ta yi a yankin teku dake gabashin zirin Taiwan

Daga CMG HAUSA Da misalin ƙarfe 1 na yammacin yau ne, rundunar ’yantar da jama’ar ƙasar Sin dake gabashin ƙasar, ta ƙaddamar da harbe-harbe daga nesa yayin atisayen soja kan yankin teku dake gabashin zirin Taiwan. Rahotanni na cewa, rundunar ’yantar da jama’ar ƙasar Sin, ta gudanar da muhimmin atisayen sojan ne daga ƙarfe 12 na ranar yau Alhamis zuwa ƙarfe 12 na ranar 7 ga watan Agusta. Mai Fassarawa: Maryam Yang
Read More
Safarar sassan mutum: Kotu ta ɗage shari’ar Ekweremadu zuwa Oktoba

Safarar sassan mutum: Kotu ta ɗage shari’ar Ekweremadu zuwa Oktoba

Daga BASHIR ISAH Kotun Turai ta ɗage ci gaba da shari'ar tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Ike Ekweremadu, zuwa 31 ga Oktoban 2022. Rahotanni daga kasar sun ce, ɗage shari'ar na nufin za a ci gaba da tsare Ekweremadu din a gidan yari har zuwa ranar da aka tsayar don ci gaba da shari'ar. Sai dai kotun ta bada belin Beatrice. Ana tuhumar Ekweremadu da matarsa Beatrice ne kan safarar sassan mutum.
Read More
NYCN ta yi wa Sanata Adamu mubaya’a

NYCN ta yi wa Sanata Adamu mubaya’a

Daga BASHIR ISAH Majalisar Matasa ta Najeriya (NYCN), ta bayyana mubaya'arta ga Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a matsayin wani mataki na tabbatar da APC ta tafi tare sa matasa a gwagwarmayar da take yi. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban majalisar reshen Jihar Nasarawa, Jaafar Loko, ya fitar ranar Alhamis a Keffi. Loko ya ce tabbatar da ana yi da matasa da inganta rayuwarsu na daga cikin muhimman abubuwan da majalisar ta sa a gaba don bunƙasa fannin dimokuraɗiyyar ƙasar nan. Ya ce, "Bunƙasa matasa a siyasa da samar musu da damammaki masu alfanu…
Read More
Har yau akwai masu kai marubuta wuta a kalamansu – Ruqayya Ibrahim Lawal

Har yau akwai masu kai marubuta wuta a kalamansu – Ruqayya Ibrahim Lawal

"Ban cika damuwa da rashin sharhin masu karatu ta" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuta mutane ne masu ɗimbin baiwa, waɗanda akasarin su za ka tarar baiwarsu ba ta tsaya kan ƙirƙirar labari kaɗai ba, suna da wasu hikimomi da suke cin abinci da su, ko kuma sana'o'in dogaro da kai na yau da kullum. Ruqayya Ibrahim Lawal da aka fi sani da Ummu Inteesar daga Jihar Sakkwato, na daga cikin irin waɗannan marubuta 'yan baiwa da za a iya ce musu ýan komai da ruwanku, don kuwa ba ta tsaya kan harkar rubuce-rubuce kaɗai ba, har ma da wasu sana'o'i…
Read More
2023: Adamu ya ƙalubalanci shugabancin APC na Abia ya daidaita al’amuran jam’iyyar a jihar

2023: Adamu ya ƙalubalanci shugabancin APC na Abia ya daidaita al’amuran jam’iyyar a jihar

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi kira ga shugabancin jam'iyyar a Jihar Abia da haɗa kan 'yan jam'iyyar jihar tare da sulhunta taksanin waɗanda suke ganin an saɓa musu. Adamu ya buƙaci su yi tsayin daka don kai bantensu a zaɓen 2023 maimakon shan kaye kada daga bisani su tattara su koma Abuja. Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Gudanarwa na jam'iyyar inda aka kafa kwamitin sulhunta 'yan jam'iyyar a Abia, Adamu ya ce ba zai lamunci shan kayen jam'iyyar ba. Ya ce, “Ya gana da shugabannin APC na Abia…
Read More
Jam’iyyun siyasa a ƙasashe da dama sun bayyana adawarsu da ziyarar Pelosy a Taiwan

Jam’iyyun siyasa a ƙasashe da dama sun bayyana adawarsu da ziyarar Pelosy a Taiwan

Daga CMG HAUSA Sama da jam’iyyun siyasa 60 a ƙasashe sama da 40, cikinsu har da Masar da Bangladesh da Afrika ta kudu, sun bayyana adawa mai ƙarfi da ziyarar da kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosy ta kai yankin Taiwan. Jam’iyyun sun bayyana adawar ne ta hannu ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, inda suka ce sun yi ammana cewa, wannan yunƙuri, ya yi matuƙar keta ‘yancin kan kasar Sin da mallakar yankunanta, haka kuma barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin zirin Taiwan. Dukkan jam’iyyun sun kuma jaddada nacewa ga manufar Sin daya tak…
Read More
Kamata ya yi ƙasashen dake da tarin makaman nukiliya su fara ragewa bisa adalci inji wani jami’in Ƙasar Sin

Kamata ya yi ƙasashen dake da tarin makaman nukiliya su fara ragewa bisa adalci inji wani jami’in Ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA Jami’in hukumar dake lura da warware makaman nukiliya ta ƙasar Sin Fu Cong, ya ce kamata ya yi ƙasashen dake da tarin makaman nukiliya su wuce gaba, wajen rage makaman yaƙi da suke da su, a fayyace, tare da kaucewa sake ƙara mallakar wasu, kuma su yi hakan bisa tsarin doka. Jami’in ya bayyana hakan ne ga mahalarta taron bita, na sassan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya karo na 10. Yana mai cewa "Yayin da ake kwance ɗamarar makaman nukiliya, kamata ya yi a wanzar da daidaito tsakanin ƙasa da ƙasa, da…
Read More
Na sha tunanin kashe kaina, don baƙin cikin rayuwa – Maryam Isa

Na sha tunanin kashe kaina, don baƙin cikin rayuwa – Maryam Isa

"Iyayena ne babban ƙalubalena a rayuwa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Tarbiyya aba ce mai matuƙar wahalar gaske da ke buƙatar jajircewa, hikima da ƙarfin zuciya. Manazarta na ganin ba kowanne uba ko uwa ne suke iya ɗaukar nauyin iyali ko ba da tarbiyya yadda ya kamata ba, saboda gazawar wasu iyayen wajen laƙantar dabarun tarbiyya da kula da rayuwar yaransu. Wasu iyayen da waɗanda ake bai wa alhakin riqon yara su kansu suna buƙatar kulawa da tarbiyya, bisa lura da yadda suke tafiyar da rayuwarsu ko sauke nauyin da ke kansu. Maryam Isa Ahmad wata matashiya ce da ke zaune…
Read More
Ana zaton wuta a maƙera..

Ana zaton wuta a maƙera..

Daga IBRAHIM YAYA A kwanakin baya ne, aka buɗe taron ƙasa da ƙasa kan cutar ƙanjamau wato AIDS a birnin Montreal na Canada, taron dake zama irinsa mafi girma kan cutar a duniya, baya kasancewarsa wani muhimmin dandali na yayata matakan kariya da magance cutar. Galibi masana kimiyya da masu fafutuka daga sassa daban-daban na duniya, su kan yi amfani da wannan dama, wajen tattauna batutuwan da suka shafi yaƙi da cutar ta ƙanjamau. Sai dai duk da muhimmancin wannan taro, a bana, ɗaruruwan mahalarta daga nahiyar Afrika, ba su samu damar halarta ba kamar yadda aka tsara, saboda wasu…
Read More