Editor

9513 Posts
Arewacin Nijeriya: Tauyayyun Zakuna (2)

Arewacin Nijeriya: Tauyayyun Zakuna (2)

Daga MUHAMMAD NASEER LERE Kamar yadda na bayyana mana irin halin da muka tsinci kan mu a arewa a kashi na farko, har na kawo yadda masu yi mana aikace-aikace da biya mana buƙatu na yau kullum suka rikiɗa, suka koma masu nema mana mafitar yanayin da ko dabbobi da gonakin Arewa bai ƙyale ba. Sannan na tsakura muku yadda suka yanke cewa za su fito su nuna irin yadda aka siyasantar da harkar tsaro a yankin Arewa. Wataƙila sun zavi wannan matakin ne domin sun san cewa, 'yan Arewa suna da hakkin rayuwa cikin annashuwa da walwala kamar yadda…
Read More
Sasanci tsakanin Hausawa da Fulani zai magance matsalar tsaro a Arewa

Sasanci tsakanin Hausawa da Fulani zai magance matsalar tsaro a Arewa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ashe matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa, na da nasaba da kisan ƙare dangi da Fulani ke yi wa ƙabilar Hausawa? Tun da ake samun ƙalubalen tsaro a jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma, ban taɓa kawo wannan tambayar a raina ba, don ina ganin ba batun kisan ƙare dangi ba ne, tsohuwar rigima ce da aka saba fuskanta tsakanin manoma da makiyaya, ƙalubalen ɗumamar yanayi da ya kai ga cinye burtalolin shanu zuwa filayen gonaki, da kuma uwa uba shigar ɓata gari cikin harkar satar shanu da…
Read More
Haɗin kan Sin da Afrika na amfanawa al’ummar nahiyar Afrika

Haɗin kan Sin da Afrika na amfanawa al’ummar nahiyar Afrika

Daga MINA Abokai, ko kun san tsawon layukan dogo da hanyoyin mota da kamfanonin Sin suka taimaka wajen ginawa a Afrika? Tsawon layukan dogo ya kai kilomita dubu 10, a yayin da na hanyoyin mota ya kai kusan dubu 100. Ban da haka kuma, kamfanonin sun gina gadoji fiye da dubu da tashoshin jiragen ruwa kimanin dari, da kuma dimbin makarantu da asibitoci, kamfanonin sun kammala waɗannan ayyuka kan lokaci tare da tabbatar da ingancinsu. Yau cikin “duniya a zanen MINA”, na zana wani hoto kan yadda wani kamfanin Sin ya gina layin dogon dake tsakanin biranen Abuja da Kaduna…
Read More
Ƙasar Sin ta mayar da martani ga yadda Nancy Pelosi ta je yankin Taiwan na ƙasar

Ƙasar Sin ta mayar da martani ga yadda Nancy Pelosi ta je yankin Taiwan na ƙasar

Daga CMG HAUSA Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, yadda shugabar majalisar wakilan ƙasar Amurka Nancy Pelosi ta rufe kunnenta game da kin amincewar da ɓangaren ƙasar Sin ta nuna. Inda ta tafi ziyara a yankin Taiwan na ƙasar, ya saba wa manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, da bayanan haɗaɗɗun sanarwoyi guda 3 da ƙasashen Sin da Amurka suka gabatar a baya, lamarin da ya girgiza tushen alaƙar Sin da Amurka, da keta ikon ƙasar Sin na mulkin kai da na kare cikakken yankin kasa. Saboda haka ƙasar Sin ta yi Allah…
Read More
Bisa aiki tuƙuru Sin ta samu karɓuwa a ƙasashen Afirka

Bisa aiki tuƙuru Sin ta samu karɓuwa a ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA A baya bayan nan, tawagar masana ta ƙasar Kenya, mai lakabin "Cibiyar raya tattalin arzikin yankin gabashin Afirka", ta fitar da rahoto, na sakamakon wani bincike game da tasirin haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka. Rahoton ya yi nuni da yadda ƙasashen Afirka ke jinjinawa ingancin ababen more rayuwa da Sin ke ginawa a nahiyar, da saurin aiwatar da manufofi, da kammala ayyuka a kan lokaci. Dalilai na zahiri sun tabbatar da cewa, Sin na aiwatar da matakai masu nagarta da inganci, ta kuma samar da moriya mai yawa, da damammaki na ingiza ci gaban Afirka, matakin…
Read More
Kowace ƙwarya tana da abokin burminta

Kowace ƙwarya tana da abokin burminta

Daga BELLO WANG A kwanakin baya, na zanta da wasu masana a yayin wani taro da ya gudana a birnin Beijing, ƙarƙashin laimar dandalin masanan Sin da Afirka, inda kalaman da wani masani dan ƙasar Habasha mai suna Yonas Adaye ya yi, ya burge ni matuƙa. Ya ce, “sakamakon bambancin al’adu da tarihi, ba za samu wani tsarin raya ƙasa da zai biya buƙatun dukkan ƙasashe ba. Wasu ƙasashen yamma na ganin cewa, ‘Ba za a samu nasarar tafiyar da harkokin mulki ba, idan ba a rungumi tsarinmu ba.’ Amma ƙasashen Afirka ba za su ci gaba da amincewa da…
Read More
Shugaban Kenya ya yaba da hanyar mota da kamfanin Sin ya shimfiɗa

Shugaban Kenya ya yaba da hanyar mota da kamfanin Sin ya shimfiɗa

Daga CMG HAUSA Jiya ne, aka fara aiki da tagwayen hanyar mota dake birnin Nairobi hedkwatar ƙasar Kenya a hukumance, wadda kamfanin shimfiɗa gada da hanya na ƙasar Sin wato CRBC ya zuba jari, tare da gina ta. Shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya halarci bikin ƙaddamar da hanyar, inda ya yaba da yadda hanyoyin mota da kamfanonin ƙasar Sin suka shimfida, wajen magance matsalar cunkuson ababan hawa a birnin na Nairobi matuƙa. A cikin jawabin nasa, Kenyatta ya ce, tagwayen hanyoyin na Nairobi da kuma sabuwar hanyar mota da ta kewaye gabashin Nairobi da aka kammala ginawa a ranar…
Read More
Hollywood ta yi rashin babban jarumi, Paul Sorvino

Hollywood ta yi rashin babban jarumi, Paul Sorvino

Daga AISHA ASAS Sharararren jarumi a masana'antar finafinai ta Hollywood ya cimma wa'adinsa, inda ya mutu yana da shekaru 83. Jarumin ya mutu ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata, a asibitin Mayo Clinic. Labarin wanda ya fito daga 'yar jarumin, Mira Sorvino ta bayyana mutuwar mahaifin nata a shafinta na tweeter, inda ta ke cewa, "mahaifina mai girma Paul Sorvino ya mutu. Zuciyata ta girgiza da rashin masoyin rayuwata. Kuma na tabbatar ƙarshen jin daɗi da soyayyarsa gareni ta zo ƙarshe. Uba ne nagari, Ina sonshi sosai. Zan yi ma ka aike da ɗaya daga cikin taurari a…
Read More
Hotunan tsiraici da Ranveer Singh ya yi sun bar baya da ƙura

Hotunan tsiraici da Ranveer Singh ya yi sun bar baya da ƙura

Daga AISHA ASAS Biyo bayan hotunan tsiraici da shahararren jarumin masana'antar Indiya, Ranveer Singh, ya fitar, mutane da yawa daga ɓangarori da dama sun tofa albarkacin bakinsu, yayin da hakan ya janyo cece-kuce a ciki da wajen masana'antar, wasu na ganin rashin dacewar wannan tsiraici, yayin da wasu ke ganin hakan bai zama illa ba. Kasancewar hotunan na mujalla ne, hakan ya sa wasu ke ganin babu tsiraici a cikin abin da ya yi. Wannan lamari dai ya sanya rabuwar kai a tsakanin jaruman masana'antar, inda wasu ke mayar da martani ga masu zagin abin da ya yi. Makusantan jarumin…
Read More
MOPPAN ba ƙungiyar siyasa ba ce, masu amfani da ita a siyasa su daina – Al-Amin Ciroma

MOPPAN ba ƙungiyar siyasa ba ce, masu amfani da ita a siyasa su daina – Al-Amin Ciroma

Daga AISHA ASAS Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya wato, MOPPAN ta gargaɗi masu amfani da ita wurin neman biyan buƙatunsu na siyasa, ta ja kunnen su da su daina amfani da sunanta yayin harkokinsu na siyasa. Gargaɗin ya zo ne a wata takarda ga manema labarai da Kakakin Al-Amin Ciroma, MOPPAN na ƙasa, ya rattaba wa hannu. Al'Amin ya ce, "Ana jawo hankalin dukkanin masu ruwa da tsaki gami da shugabanni a matakin jiha da na ƙasa cewa, ƙungiyar MOPPAN ba ƙungiya ce ta siyasa ba, kuma ba ta da alaƙa da wata jam'iyya." Wannan tunatarwar tana zuwa…
Read More