Editor

9513 Posts
Waye Ibrahim Taiwo?

Waye Ibrahim Taiwo?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haifi Ibrahim Taiwo a shekarar 1940, a ƙaramar hukumar Wushishi ta Jihar Neja da ke tarayyar Nijeriya. (Bincikenmu bai samo rana wata da kuma kwanan watan da aka haife shi ba). Ya taso a garin Kagara, har ma a lokacin da ya ke makaranta a kan kirashi da suna Ibrahim Kagara. Ya yi Firamare ɗinsa a Senior Primary School Minna, sai kuma Bida Middle School. Ya halarci Provincial Secondary School da ke Okene na ɗan wani taƙaitaccen lokaci, inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare. Aikin Soja: Ya fara shiga aikin damara ne a shekarar…
Read More
Ɗaukar nauyin iyali: Taimakon da ya wajaba a kan mace

Ɗaukar nauyin iyali: Taimakon da ya wajaba a kan mace

Daga AMINA YUSUF ALI Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata, mun tattauna a kan haƙƙoƙin iyali da kuma wasu dalilai da suke hana maza kasa sauke wannan nauyi da Allah ya raba ya ɗora musu. Su ma mata Allah ya ɗora musu nasu haƙƙoƙin. Sai dai abin lura kusan dukkan ko ma dukka haƙƙoƙin da suka shafi ɗaukar nauyi ta fuskar kuɗi maza Allah ya ɗora wa. Sai dai wani lokacin maza kan bar wa mata wannan ragamar ba tare da tunani ko yardar ta ba. Wata kuma ba yardar tata amma ta karɓa don…
Read More
HOTUNA: Yadda mawaƙi Rara ya shirya addu’ar zaman lafiya ga Nijeriya

HOTUNA: Yadda mawaƙi Rara ya shirya addu’ar zaman lafiya ga Nijeriya

A ƙarshen makon da ya gaba Shugaban tafiyar 13x13, mawaƙi Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, ya shirya addu’a ta musamman a kan rashin tsaro da ke addabar Arewaci da ma wasu sassan Nijeriya. Yayin taron, an gabatar da karatun Alƙur'ani da sauransu. Taron addu'ar ya samu halartar n'manya da tsofaffin masu shirya finafinan Hausa na faɗin ƙasar nan, mata da maza. Hoto: Sani Maikatanga Photography Taron addu'ar da mawaƙi Rara ya shirya
Read More
Ta zuwa wa mijinta ruwan batir har lahira kan ƙarin aure

Ta zuwa wa mijinta ruwan batir har lahira kan ƙarin aure

Wata matar aure ta halaka mijinta ta hanyar zuba mishi gubar asid saboda zai yi mata kishiya. Matar ta yi wa mijin nata wanda suka shekara 12 tare wannan ɗanyen aiki ne ranar Lahadi a unguwar Apo da ke Masaƙa a Jihar Nasarawa. Majiyarmu a yankin ta ce, a baya-bayan nan mamacin mai shekara 42, na yawan samun saɓani da matar tasa kan shirinsa na ƙara aure. Majiyar ta ce, a baya matar ta taɓa kwashe kayanta daga gidan mijin na tsawon shekara biyar, daga baya shi kuma ya auri wata mata. Wani qanin marigayin ya ce, “ɗan uwana na…
Read More
Matashi ya yi wa ƙanwarsa fyaɗe a Gombe

Matashi ya yi wa ƙanwarsa fyaɗe a Gombe

’Yan sanda a Jihar Gombe sun kama wani matashi mai suna Abubakar Hamidu, ɗan shekaru 35 da ke zaune a Unguwar Jauro Abare, da zargin yi wa ƙanwarsa fyaɗe har sau biyu a lokuta daban-daban. Rahotanni sun rawaito cewa, da ya ke gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Baba’ita, ya ce, wani mai suna Muhammad Hamza ne ya shigar da ƙarar matashin a ranar 19 ga watan Yulin da mu ke ciki. Baba’ita ya ce, mai shigar da ƙarar wanda ke zaune a Unguwar Kasuwar Mata, ya kai wa ’yan sanda…
Read More
Ya aika budurwarsa lahira kan ragargaza masa wayar iPhone

Ya aika budurwarsa lahira kan ragargaza masa wayar iPhone

Saurayin mai suna Godspower Adigheti ɗan shekara 23 ya kashe budurwarsa mai suna Gift Ojoku, inda ya aikata hakan saboda tsananin fusata da kuma kishi. Rahotanni sun rawaito cewa, fusataccen saurayin ya halaka masoyiyar tasa, wadda ta kasance ɗaliba a makarantar koyon Fasaha da ke jihar Delta. Kuma ta tarwatsa wayar tasa ne mai ƙirar iPhone 13 pro max. Wannan tashin-tashina ta faru ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata. Wata majiya ta shaida mana cewa, soyayya ta yi nisa tsakanin waɗannan masoya guda 2, domin kuwa akwai ƙaruwar ’ya a tsakaninsu. An dai ce rigimar ta fara ne…
Read More
Cikin watanni uku an haifi yara sama da 27,000 a Kano

Cikin watanni uku an haifi yara sama da 27,000 a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa cikin watanni uku an haifi jarirai 27,490 a faɗin jihar. Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, babban daraktan hukumar da ke kula da asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Nasiru Alhasan Kabo, ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke ƙaddamar da shirin rarraba kayan kula da lafiya ga asibitocin kula da lafiya na matakin farko da na biyu da kuma na uku. Dakta Nasiru ya ce, kayan da aka raba da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 15 na haihuwa ne da kayan bayar da na sashen kula da bayar da agajin gaggawa da na…
Read More
Shugaban Zambia ya ziyarci rumfar Sin a taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na ƙasarsa karo na 94

Shugaban Zambia ya ziyarci rumfar Sin a taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na ƙasarsa karo na 94

Daga CMG HAUSA A jiya Lahadi ne shugaban ƙasar Zambia Hakainde Hichilema, ya halarci taron baje kolin harkokin noma da kasuwanci na ƙasar sa karo na 94, inda ya ziyarci rumfar ƙasar Sin, irinta ta farko da Sin ɗin ta kafa a baje kolin. Taken baje kolin na bana shi ne "Fasaha ke ingiza ƙirƙire ƙirƙire-Fasaha ke sauya kasuwanci". A bana baje kolin na Zambia, ya samu tarin kamfanonin Sin mahalarta, cikin kamfanoni kusan 110, waɗanda suka shafi sassa daban daban, kamar fannin shuka tsirrai, da sarrafa na’urorin aikin gona, da na sarrafa albarkatun noma. Mai fassarawa: Saminu Alhassan
Read More
Ruwan tumfafiya: Tattaki a yanar gizo, leƙe cikin zaurukan ‘Yahoo Groups’

Ruwan tumfafiya: Tattaki a yanar gizo, leƙe cikin zaurukan ‘Yahoo Groups’

Tattarowa: Khalid Musa Hausawa su ka ce kishi kumallon mata. Duk da cewa ba mata ne kawai su ka kaɗaita da halittar kishi ba, mazaje ma a nan ba su tsira ba amma ya fi shahara ga mata domin karancin juriyarsu gare shi. Wannan muhawara ta Ruwan Tumfafiya an yi ta ne a kan Kishi ko Kishiya. Wata Marubuciya Salamatu Adamu ita ce ta haifar da wannan muhimmiyar Muhawar a dandalin Marubuta na Yahoo wacce ta samu gudunmawar wasu hazikan Marubuta da su ka ja zaren muhawar abinda ya kara ma ta armashi. Wadannan Marubuta sune: Habibiy, Muhammad Fatuhu Mustapha…
Read More