Editor

9513 Posts
Muna da katin zaɓe 389,000 da ba a karɓa ba a jihar Kano — INEC

Muna da katin zaɓe 389,000 da ba a karɓa ba a jihar Kano — INEC

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Hukumar Zaɓe Mai zaman kanta ta Ƙasa, INEC ta ce akwai sama da katikan zaɓe dubu ɗari uku da tamanin da tara da masu su ba su je sun karɓa ba a jihar Kano. Kwamishinan zaɓe na jihar, Riskuwa Shehu ne ya bayyana haka lokacin da Kwamishinan Tarayya na Hukumar Ƙorafe-ƙorafe, Ahmad Daɗinkowa ya kai masa ziyara a jiya Alhamis. Riskuwa, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gudanarwa, Garba Lawan ya ce katikan da ba a karɓa ɗin be tun na shekarun 2011 zuwa 2018 ne. Ya ce mutane ba sa son zuwa su karɓi katin zaɓen…
Read More
Hukumar Kiwon Lafiya ta Bauchi ta tabbatar da ɓullar cutar Ƙyandar Biri

Hukumar Kiwon Lafiya ta Bauchi ta tabbatar da ɓullar cutar Ƙyandar Biri

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Shugaban hukumar kiwon lafiya a Matakin Farko ta jihar Bauchi, Dokta Rilwanu Mohammed ya tabbatar da ɓullar cutar Ƙyandar Biri, wato Monkey Pox a cikin jihar. Dokta Rilwanu Mohammed ya shaida wa manema labarai a kwanakin baya cewar, bayan tabbatar da cutar ga wani mutum, ana kuma gwajin wasu mutane biyu da ake ganin sun kamu da ita wannan cuta. “Harbabbe daga cutar ya fito daga Jihar Adamawa ne, kuma a halin yanzu ana yi masa tattalin kiwon lafiya daga wannan cuta a wata keɓaɓɓiyar cibiyar kiwon lafiya dake cikin jihar ta Bauchi. Ba za…
Read More
An kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a kai hari gidan yarin Kuje

An kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a kai hari gidan yarin Kuje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami'an tsaron Nijeriya sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga 'yan bindiga a babban birnin ƙasar, Abuja. Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai ƙarfi ta hukumar leƙen asiri ta ƙasa da ke tabbatar da kamen. Jaridar ta ce an cafke mutanen tare da wasu na'urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu da basa amfani da intanet. Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu ɗaukar nauyinsu. Waɗannan mahara ake kuma zargi…
Read More
‘Yan fashin daji na ta kwararowa jiha ta, Gwamnan Nasarawa ya koka

‘Yan fashin daji na ta kwararowa jiha ta, Gwamnan Nasarawa ya koka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana damuwa game da yadda gungun 'yan fashin daji ke tururuwa zuwa jiharsa bayan koro su daga maƙwabtan jihohi. BBC ta rawaito cewa, Gwamna ya ce jami'an tsaro sun lura da ƙaruwar 'yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Karu, wadda ke da nisan ƙasa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin ƙasar. "Mun lura da tarin 'yan fashin nan da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan Juli da Rugan Madaki da ke Ƙaramar Hukumar Karu," a cewar gwamnan yayin taron…
Read More
NDLEA ta rufe gidan abinci bisa zargin sayar da kayan maye a Kano

NDLEA ta rufe gidan abinci bisa zargin sayar da kayan maye a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya ta NDLEA ta rufe wani gidan abinci da take zargin ana sayar da kayan maye tare da kama kusan mutum 51 a Kano. BBC Hausa ta rawaito cewa hukumar ta NDLEA ta ce ta kama mutanen ne bayan samun ƙorafi daga mazauna unguwar da gidan abincin yake a titin Lamido Crescent da ke cikin birnin na Kano, saboda yadda matsalar ke neman gurɓata tarbiyyar 'ya'yansu. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta aike da wani mai…
Read More
Malaman Jami’ar Kaduna sun janye yajin aiki bayan barazanar korarsu da El-Rufa’i ya yi

Malaman Jami’ar Kaduna sun janye yajin aiki bayan barazanar korarsu da El-Rufa’i ya yi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bayan rantsuwa da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi cewa sai ya fatattaki duk wani malamin Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, da ya cigaba da yajin aiki, Malamai sun dawo aiki gadan-gadan a ranar Litinin. Rahotanni da suka iske Manhaja sun nuna yadda ɗalibai suka yi tururuwa zuwa jami’ar domin ci gaba da karatu. Sai dai kuma ba karatu aka yi ba a wannan rana, inda ɗaliban sun ci gaba da jarabawa ce wacce suna tsaka da zana wa aka tafi yajin aikin. Ɗalibai sun garzaya ɗakunan karatu duk sun zauna domin fara rubuta jarabawa.…
Read More
ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako huɗu

ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami'o'i a Nijeriya ta ASUU ta bayyana matakin tsawaita yajin aikin da take yi da mako huɗu. Dama ASUU ta shafe sama da watanni biyar tana yajin aikin bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin Nijeriya, yanzu kuma ga shi ta ƙara wata ɗaya. Idan har aka shafe wasu makonni huɗu ba a sasanta tsakanin gwamnati da ASUU ba, hakan na nufin ɗaliban jami'o'in sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida. Sanarwar da ASUU ta fitar na ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke, an kuma fitar da ita…
Read More
Tsohon Sufeto-Janar, Tafa Balogun ya kwanta dama

Tsohon Sufeto-Janar, Tafa Balogun ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa tsohon Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Mustapha Balogun, rasuwa. Majiya daga ahalin marigayin ta tabbatar wa Daily Trust rasuwar, sai dai babu wani ƙarin bayani a kan haka. Marigayin wanda ya zama Sufeto-Janar na 'Yan Sanda a watan Maris, 2002, ya rasu ne kwanaki huɗu kafin cikarsa shekara 75 da haihuwa. An haifi Bologun ne a ranar 8 ga Agustan 1947 a Ila-Orangun da ke Jihar Osun. A halin rayuwarsa, marigayin ya shahara ne a 2005 bayan da aka gurfanar da shi a kotu bisa zargin tafka mundanar sama da Dala miliyan $100…
Read More
Ana zargin ‘yan bijilante da kashe malamin makarantar allo a Kano

Ana zargin ‘yan bijilante da kashe malamin makarantar allo a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana zargin 'yan ƙungiyar sintiri (vigilante) da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Davai, da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano. Shi dai Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Ƙur’ani ne a unguwar, inda yake da ɗaruruwan almajirai. Ana zargin 'yan ƙungiyar sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunƙurin satar yaro. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ɗan malamin, Ibrahim ya shaida mata cewa, ”mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa…
Read More
Ma’aikatar tsaron Sin ta yi bayani game da matakan soji da Ƙasar ta ɗauka

Ma’aikatar tsaron Sin ta yi bayani game da matakan soji da Ƙasar ta ɗauka

Daga CMG HAUSA Kakakin ma’aikatar tsaron ƙasar Sin Tan Kefei, ya ce ƙasar Sin ta ɗauki matakan soji domin tsaron kai, bisa la’akari da yadda kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan, a ranar 2 ga wata. A cewarsa, wannan yunƙuri ne da ya saba da alƙawarin Amurka na kin goyon bayan ‘yancin Taiwan, kuma taƙala ce ta siyasa mai tsanani ga ƙasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin na adawa da kin lamuntar hakan. Rundunar yankin gabashi ta runduanr ‘yantar da al’ummar ƙasar Sin PLA, ta shirya kai farmaki na hadin gwiwar sojoji, ta ruwa da…
Read More