21
May
Daga IBRAHIM HAMISU Kano Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da shugabancin jam’iyyar PDP, ƙarƙashin jagorancin Shehu Wada Sagagi har sai ta gama sauraron ƙarar da aka shigar a gabanta. Ana zargin Sagagi da biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.Wani Bello Bichi ne dai ya shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a A. M. Bichi, inda ya yi ƙarar jami’yyar PDP da hukumar INEC da kuma sauran mutane 40. Kotun ta ce ta bada umarnin ne domin guje wa wani yanayi da za a zama babu…
