21
May
Daga WAKILINMU Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da ita a kan hanyarta ta zuwa Yola daga Kaduna don halartar Musabaƙar RABIDA. Kafin rasuwarta, marigayiyar ita ce Amirar Gidauniyar Nana Asma'u ta Ƙasa kuma shugabar Ƙungiyar IMWON. A halin rayuwarta, Hajiya Rabi'atu ta ba da gudunmawa matuƙa a harkokin da'awa da ayyukan Hajji a matakin jiha da ƙasa. 'Yan uwa, dangi, maƙwabta da abokan arziki na kusa da nesa na ci gaba da yi wa marigayiyar addu'ar dacewa da Jannatul Firdausi.
