Editor

9513 Posts
Babu ranar janyewa daga yajin aiki, cewar ASUU

Babu ranar janyewa daga yajin aiki, cewar ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rahotanni sun ce an kasa cimma matsaya tsakanin ƙungiyar Malaman Jami’oi ASUU da Gwamnatin Tarayya, kan yajin aikin da ƙungiyar ta shafe matanni tana yi. Tun watan Fabrairun 2022 ASUU ta shiga yajin aiki, haka ma ƙungiyar ma’aikatan jami’a sun shiga nasu yajin aikin daga baya kan wasu buƙatu da ƙungiyoyin suke son gwamnati ta cika masu. Rahotanni sun ce ɓangarorin sun tattauna a ƙarshen mako, amma babu wata matsaya da aka cimma tsakanin shugabannin ƙungiyar malaman ASUU da ƙungiyar SSANU da NASU da kuma ɓangaren gwamnati, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Shugabannin…
Read More
Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga taron ministocin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS

Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga taron ministocin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS

Daga CMG HAUSA A yau Alhamis ne shugaban ƙasar Sin Xi jinping, ya gabatar da jawabi a yayin buɗe taron ministocin wajen ƙasashe mambobin ƙungiyar BRICS ta kafar bidiyo. Cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya ce a halin yanzu, dalilan dake haifar da rashin kwanciyar hankali, da rashin tabbas, da rashin tsaro a harkokin ƙasa da ƙasa na ƙara bayyana. Amma duk da haka, jigon wannan zamanin da muke ciki na zaman lafiya, da neman ci gaba bai canza ba, kaza lika burin al’ummun duniya na samun kyakkyawar rayuwa bai sauya ba, haka kuma, fatan sassan ƙasa da ƙasa…
Read More
Baki biyu bai dace da matsayin Amurka ba

Baki biyu bai dace da matsayin Amurka ba

Daga CMG HAUSA Yayin da gwamnatocin ƙasashen Sin da Amurka ke ƙara azamar daidaita tsakani, da shawo kan sabani, da kaucewa mummunar takara, masharhanta na ganin mafi yawan matsalolin da ƙasashen 2 ke fuskanta na da nasaba ne da yadda Amurka ke karya ƙa’idoji, ko ra’ayoyin da sassan biyu suka amincewa. Daya daga muhimman batutuwa dake ci gaba da janyo hankalin duniya, don gane da takun sakar dake wakana tsakanin Sin da Amurka shi ne batun yankin Taiwan na ƙasar Sin, inda a wasu lokuta Amurka ta sha bayyana goyon bayan ta ga kasancewar yankin Taiwan ɓangare na ƙasar Sin…
Read More
Jakadan Sin ya yi kira a bada fifiko wajen bunƙasa cigaban yankin Sahel

Jakadan Sin ya yi kira a bada fifiko wajen bunƙasa cigaban yankin Sahel

Daga CMG HAUSA Wakilin ƙasar Sin ya buƙaci a bada fifiko wajen bunƙasa cigaban yankin Sahel. Zhang Jun, zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD, ya ce Afrika tana fuskantar wahalhalu wajen cimma nasarar samun cigaba. Matsalolin ƙarancin abinci da duniya ke fuskanta a halin yanzu, da matsalar makamashi, da ta kuɗaɗe, sun kara tsananta halin da ake ciki a Afrika, sannan matsalar ta fi kamari a yankin Sahel. Zhang Jun, ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin sulhun MƊD game da shirin G5 Sahel, wato wani shiri ne na hadin gwiwa don tsara manufofin bunƙasa cigaba da tabbatar da…
Read More
Yadda aka gudanar da bikin Ƙaramar Sallah a fadar Tsibirin Gobir

Yadda aka gudanar da bikin Ƙaramar Sallah a fadar Tsibirin Gobir

Daga MUKHTAR YAKUBU Bukukawan sallah wani abu ne da yake da muhimmanci a fadar sarautar Hausa wanda aka shafe tsawon shekaru ana yi domin raya al'adun Hausawa da muka gada iyaye da kakanni. Dukkan masarautun da suke ƙasar Hausa da ma wadanda suke kewaye da su suna gudanar da irin nasu bikin, sai dai na wata masarautar ya sha bambam da yadda wata take gudanar da nata bikin. Wannan ya sa manyan mutane da masu yawon buɗe idanu daga ƙasashen duniya suke halartar bukukawan sallah a ƙasar Hausa.  Masarautar Gobir dake Tsibirin Gobir a Jihar Maraɗi dake Jamhuriyar Nijar tana…
Read More
Kaso 30 na marubuta kawai ke buga littafi – Umar Muhammad

Kaso 30 na marubuta kawai ke buga littafi – Umar Muhammad

"Zuwan wayoyin zamani ne ya girgiza kasuwar littafai" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Satar fasaha na daga cikin manyan matsalolin da marubuta a ko'ina a duniya ke fama da su, idan ana batun ƙirƙira, rubutu, da adabi. Marubutan adabi ma suna fama da nasu irin ƙalubalen da ke dakushe cigaban harkar rubutun adabi. Fitowar sabuwar manhajar zamani ta ArewaBooks ta zo a lokacin da ake buƙata, sakamakon yadda take ƙoƙarin killace rubuce rubucen littattafan Hausa, musamman na yanar gizo, don masu karatu da kasuwancin littattafai cikin tsari da kiyaye haƙƙin mallakar marubuci. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu ya zanta da…
Read More
Fa’idar Habbatus Sauda

Fa’idar Habbatus Sauda

Daga BILKISU YUSUF ALI Tambaya:Anti Bilkisu, mu na son mu san fa’idar Habbatus-Sauda. Amsa:Habbatus Sauda wata ƙwayar itaciya ce mai albarka, wacce ta ke tattare da fa’idoji kala-kala a jikin ɗan’adam wanda ya kamata dukkan iyali ya kyautu a ce suna ajiye ta a cikin gida domin magani da kariya ga iyali da kiwon lafiya. Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye daban-daban saboda muhimmancinta da shahararta. Bayan sunanta Habbatus Sauda ana kiran ta Habbatul Baraka. Da Turanci kuma ana kiran ta da ‘Blessed Seed, Black Cumin, Nigella Aativa, Black Caraway’ da sauransu. Daga cikin fa’idojin Habbatus Sauda akwai:Magance larurar rashin ruwan…
Read More
Na fuskanci ƙalubale a neman ilimin boko – Hon. Hafsat Abdullahi

Na fuskanci ƙalubale a neman ilimin boko – Hon. Hafsat Abdullahi

"Da kaina na yi fafutukar samun ilimin boko" Daga JOHN D. WADA a Lafiya Honorabul Hafsat Abdullahi cikakkiyar ‘yar siyasa ce da ta riqe muƙaman siyasa daban daban a Jihar Nasarawa. A yanzu ita ce mataimakiyar shugaban Ƙaramar Hukumar Lafiya kuma hedikwatar gwamnatin jihar. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana tarihin rayuwarta da ƙalubale da ta fuskanta a rayuwa da sauransu, inda ta kuma shawarci ‘yan uwanta mata su yi dukka mai yuwa wajen neman ilimin zamani da na addini da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.HONORABUL HAFSAT: Sunana Honorabul Hafsat Abdullahi. An…
Read More
‘Yan ta’adda sun sace jami’in kula da harkokin ɗaliban AGP

‘Yan ta’adda sun sace jami’in kula da harkokin ɗaliban AGP

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau. Hukumomin Abdu Gusau Polytechnic Talata Mafara a jihar Zamfara sun tabbatar da sace jami’in kula da harkokin ɗaliban Polytechnic Mal. Sanusi Halilu ta ƙungiyar 'yan ta'adda. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin hulɗa da jama’a na kwalejin kimiyya da fasaha ta HOD mass Communication, Mal. Aliyu Damri (ANIPR), and made available to Blueprint in Gusau Laraba. Sanarwar ta nuna cewa, Mal. An yi garkuwa da Sanusi Halilu a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Talata. “Jami’in kula da ɗaliban mu Mal Sanusi Halilu tare da sauran…
Read More
Shugaba Xi ya jaddada aniyar ƙasarsa ta buɗe ƙofa mai nagarta

Shugaba Xi ya jaddada aniyar ƙasarsa ta buɗe ƙofa mai nagarta

Daga CMG HAUSA A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar ƙasar sa ta buɗe kofa mai nagarta, yana mai cewa Sin za ta ci gaba da bude kofa ga duniya baki ɗaya, ba tare da sauya matsaya ba. Xi ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake jawabi ga taron cika shekaru 70, da kafuwar hukumar yayata hada-hadar cinikayyar ƙasa da ƙasa, da taron kolin ƙasa da ƙasa na ingiza harkokin cinikayya da zuba jari, da ya gudana ta kafar bidiyo. Fassarwa: Saminu
Read More